Skip to content
Part 29 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Mai Kano ya fito daga motar Yana huci inda har motar ta kusa cika cika Amma ya fito a fusace inda Dan Kamashon Yana cewa yayi hakuri yanzu motar zata tashi Amma Bai kula shi ba ya wuce ya barshi ya fito Bakin titi Yana tare Mai napep ya SHIGA Yana fada mishi ya kaishi sardauna Estate. Ya SHIGA me napep din ya burka suka Miki titi. Suns tafe Mai Kano na Huci tamkar wata mesa inda kuma zuciyar shi ke fada mishi kayi wauta Mai Kano da ka sanar da mutumin can zuwan ka . Ai irin su Alh Aminu marasa mutunci da Rashin tsoron Allah ba a fada musu za a Zo sai dai ayi musu tashi na Kama ka. Don yadda ya keta haddin mahaifiyar ka Kai ma Bai zamo abin mamaki ba ya sheke ka tunda har ya San cewa Kai din ka San komai. Don haka Kar ka yarda ka tafka kuskure Daya Mai ban haushi.
“Juya ka maida Ni Tasha malam na fasa ! Ya fada Yana tsaida Mai napep din. Ai kuwa sai ya juyo suka nufi tashar.

Cikin sa a Kuma motar da ya Bari Bata tashi ba ya kuwa shige ba da jimawa ba motar ta daga suka bar garin katsina zuwa Legos Yana Jin ba zai iya tunkarar Alh Aminu a wannan lokacin da ya San zasu gana ba sai dai kawai yayi mishi dirar mikiya

Su zarto suka yi ta zaman karawa sama hazo suna jiran zuwan bakon da aka Basu umarnin da yazo suyi ta dukan shi har sai sunga ya Daina motsi Amma har magaruba babu shi babu labarinsa.

Dole suka tafi saboda shi ma Alh Aminun Bai tsaya ba ya dai Basu kamannin Mai kanon yace su tabbatar sunyi mishi bugun da ba zai tashi ba Amma kafin su fara dukan nashi su tambaye shi inda Uwar shi take idan ya fada din ma kar su barshi in ko Bai fada ba suyi ta dukan shi har Sai ya fada Amma sai shiru ta Basu labari.

Alh Aminu ya Kira Zarto misalin karfe Tara na dare Yana tambayar shi.

“Ya ya aka Kare ne Zarto?

“Ai Mai gida Babu Wanda yazo har takwas ta buga shiyasa ma muka taho Amma nacewa goloko idan yazo ya bude mishi gida ya SHIGA Ni Kuma ya kirani yanzu na Kira golokon yace min Bai Zo ba.

“To Bari na kirashi na CE mishi Ina jiran shi…

Ya Kira wayar Mai Kano ya zaro ta Yana dubawa inda yayi arba da lambar Alh Aminu
Wata zuciyar tace ya dauka wata Kuma tace ya Rabu da shi don Haka sai yaji yafi aminta da ya barshi kada ya dauka don Haka yayi ta faman Kiran shi Amma yaki dauka har suka SHIGA garin Legos Bai Daina Kiran shi ba Amma yaki dauka.

Ya sanar da Halima cewa kowa Yana lafiya hajiya da Husna da sulaiman.

“Naji Ina kewar su Mai Kano kamar na koma garesu.

“Ba yanzu ba Mama don in Kika koma yanzu Akwai damuwa don na Rantse Miki da Allah sai Alh Aminu ya Gane fadan da ya jawo yafi karfin shi ko Zan kyale komai ba Zan kyale wannan ba Kar ma kice min in Bari.

“Mai Kano mutumin da baya tsoron Allah komai zai iya aikatawa.

“Ni Kuma mama Allah na sako shiyasa zanyi nasara Akan shi Allah ya Baki lafiya ki Rabu da wannan cikin Zan koma gida in fada mishi kina hannu na Kuma Ina son inji Dalilin shi da ya Rasa duk Matan Duniya ya Rasa wadda zai cuta sai uwata.

“Kayi hakuri ka barshi Mai Kano sharrin shi zai koma mishi.

Ya Mike ya SHIGA dakin shi ta San ba zai kyale ba sai kawai tayi mishi fatan Ubangiji ya tsare shi dukkan sharrin Alh Aminu.

Amal ta zabga ta gumi Husna ta taho da sauri tana nuna Mata zoben da Yaya muhsin ya Bata me hoton zuciya sai dai duk karadin da take Amal din Bata San tanayi ba sai da ta dafa kafadar ta.

“Anty lafiya kike kuwa? Amal ta sauke ajiyar zuciya tana duban Husna. “Wallahi banji shigowar ki ba Husna. “Anya kuwa Anty lafiyar ki kuwa irin wannan tunani Haka?

“Uhum Husna Babu lafiya yasin.

Me ya faru? Ko Baki da lafiya ne?

“Ba gara ciwo da irin wannan yanayin ba? Kai Ashe hadarin da ya dake ka shi yayi Ruwa Husna…

“Don Allah fada min abinda ke faruwa wallahi Ni duk hankalina ya tashi…

“Kwanaki wani Gaye ne yazo gidan Nan neman Daddy Wallahi tun a kallon farko da nayi mishi naji zuciya ta ta buga tun daga Ranar ban Kuma samun sukuni ba komai nakeyi shi nake gani Husna ko bacci na kwanta mafarkin sa nake tun ina karyata zuciya ta Husna har na yardar wa kaina son shi nake Kuma gashi ban san inda Zan Kuma ganin shi ba har Daddy na tambaya ina fasalto mishi suffar shi Amma yace min Bai Gane shi ba. Sai yanzu nakejin haushin kaina da ban yi hikimar tambayar sunan shi ba da lambar wayar shi.

Kamar Dariya ta kufcewa Husna Amma ganin halin da take ciki yasa ta gimtse kayan ta ta Soma da Bata shawara…

“Ayya Anty Amal na tausaya Miki wallahi so baya misaltuwa ga Wanda Bai fada komar shi ba. Marubuta ma a yanzu sun kasa fasalto shi asalin yadda yake sai dai su bada misalin abinda kawai ya sawaka abakin su da alkalamin su. Abinda ya kamata kiyi shine kiyi ta kaiwa Ubangiji kukan ki ki Kuma Roke shi inda ALHERI ya kawo sanadin haduwar ku Idan Kuma babu ki Roke shi sauki Akan yadda kikeji a kirjin ki don son da ba a San kanayi ba yafi komai ciwo tamkar son maso wani koshin wahala Allah ya Baki abinda kike so in har ALHERI ne.

Amal ta amsa d Ameen…

Anty maimuna ta Zo wurin Yar Uwar ta haj wasila Akan maganar Safina da muhsin sukayi magana Akan tunda ya Fara aiki me ake jira? Suka gama maganar su maimuna ta tafi Akan sai Alh Aminu ya dawo an sanar dashi.
Da Kuma ya dawo ta fada mishi maganar ya dubeta

“Wai ba yaron Nan yace Miki baya son Safinar Nan ba? Koko Dole ne sai kun hada su?

“Karyar banza ce idan ma ya ce baya sonta don Bai ganta a dakin shi bane. Da an daura zaka Gane karyar so yake yi.

“To ki sameshi kuyi maganar ku Ni duk yadda kukayi na Amince…
Suna cikin maganar muhsin din da ake magana Akan shi ya shigo…

“Yauwa Kai Zo. Cewar Alh Aminu. Ya karaso Yana Rusunawa.

“Maganar kuce da Safina ta taso. Har Uwar ka maimuna tazo Akan batun sun kuma daidai ta shine nace sunji ta bakin ka? Don ai kamar ce min kayi baka son Safinar ko?

Ya gyada kanshi Alamar Eh Haka ne…
“To fada Mata da Bakin ka in Kuma ka Amince Ni iyakata ADDU A na Kuma bada abinda duk aka nema…

“Mami ayi hakuri don Allah abar maganar Safina Wallahi bana sonta Ina da wadda nake so…
“Fakat ! Cewar Alh Aminu.
Sai ki fadawa maimuna ayi hakuri tunda baya so abar maganar.

“Zaka Goya mishi baya ne ya batawa yarinya lokaci? Wallahi ba zai yuwu ba sai ya Auri Safina ko da kuwa zai Rika mutuwa ne Yana dawowa don na kula da take taken sa shi kanshi ai yasan ba Zan yarda da abinda Yake shirin tattago min ba . Don haka Auren safina ya Zama jazaman kaima da kake tunanin zance ka kawo wani Abu da shi da kake tunanin Zan nemi yardar shi duk kuje inuwa ku huta Ni Zan zube komai nawa har sai Naga Safina ta tako gidan Nan da sunan matar muhsin…

Karab sai a kunnen Husna wadda taji tamkar Aradu ce ta Rikito mata akwanyar kanta…

To. Bari mugani Safinar ce ko kuwa Husna?

<< Hawaye 28Hawaye 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×