Skip to content
Part 31 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

 “Salma? Makauniyar ta kwada kiran sunan yarinyar da iyakacin karfin ta Kuma a zafafe yadda zai nuna maka makauniyar ba karamar masifaffiya bace.

“Wannan tsinanniyar yarinya gidan uban wa Kuma ta shige don Uwar ta? Ta fito daga dakin tana laluben bango cikin Rashin sa a kuwa tayi tuntube da mutum har taci da kasa cikin fushin zuciya ta Soma jibgar wadda tayi karon da ita a zaton ta Salmar ce.

Da sauri Auta da kunnenta ke toshe da bututun zuko sauti ta cire tana fadin “Ke Adama me nayi Miki Haka ko kina hauka ne?

“Yi hakuri Auta kece a Nan? Ina wannan bankadaddiyar yarinyar take?

“Kamar makaranta fa Naga ta tafi. “Ban Hana ta zuwa makarantar Nan ba?

“Adama ki fa shafawa yarinyar Nan lafiya Wallahi Ina tsoron Dan iskan yayan ta ya kula da abin da kike Mata komai zai iya faruwa.

“Yo aka fada Miki ina tsoron shi ne? Uwar shi ma da ta goga kishi Dani Bata wanye lafiya tuni ta tunkuyi bangon kashewa bare su Kayan banzan da ta Haifa bayan ta saci kwanana.

Yarinyar ta shigo da kayan makaranta ajikin ta shekarun ta ba zasu wuce Sha biyar zuwa Sha shida ba inda take gaishe da Adams da Auta.

“Yauwa Yar iska ku dai Kam uwar ku ta cuce ku ta haife ku duk Yan iska ke bin malaman makaranta Dan uwan ki Kuma sace sace uwa beran tanka.

“Ban hanaki zuwa makarantar Nan ba? Da Yake kin Raina Ni shine Kika saci jiki Kika tafi wurin malaman dake matse ki a cikin aji ko? Ko da Yake ai barewa batayi gudu Dan ta yayi Rarrafe ba uwar ki ma Haka wadan da suka santa suka fada bin maza ne Aikin ta kamar karya har dai ciki an zubar Mata to gashi Nan kema kin dauko hanya.

“Uhm uhm Adama cin mutunci bashi da Dadi uwar yarinyar nan itace kishiyar ki ba ita ki Daina fada Mata irin wannan maganar gaskiya yarinya tana Miki biyayya kina wulakanta ta?

“Maza ki wuce ki Yar iska wadda ta gado bakin hali ki dauko ga hatsi can ki surfa min yau hatsi da wake Zaki dafa salon kiyi min muguntar da Kika Saba ta cika min gishiri inci uwar ki la ada waje

Salma ta dauko geron ta nufi turmi da nufin surfe Auta ta zuge jakar ta ta zaro Naira hamsin ta Mika Mata tace ta Kai injin a surfo… Auta diyar Adama ce itace Auta shiyasa take ce Mata Auta duk da babu sauran diyan wasuma tun kafin a haife su suke barewa Amma Adama tace Assibi ce wato uwar su zarto da Salma Wai ita ke kashe Mata Yara daga karshe ma sai haihuwar ta daka ta inda Kuma Assibi tayi ta haihuwa Kuma duk maza take Haifa inda Adama tace sai ta Rama ai kuwa ta shiga yiwa yaran Assibi sanadin mutuwa. Tayi sanadin jefa wani Rijiya wani Kuma ta bashi gawa dubu yaci wani Kuma tun daga haihuwar shi ta sharbeshi da Reza da sunan yankan cibi.

Sai fa masu Rabon numfashi irin su zarto Wanda sunan shi Hamza da Kuma kanwar shi Salma bayan Adama ta samu Auta Amma duk da Haka sai da Adama tayiwa Assibi sanadin ciwo Wanda yayi Ajalin ta Kuma Kai tsaye take Fadin a itace tayi Mata don ita ba a Auren mijinta a zauna lafiya duk ma wadda tsautsayi yakai Auren mijinta to zatayi Ajalin ta inda Kuma mijin da takeyiwa ya Rigamu gidan gaskiya Amma Bata kyale yaran Nan sun huta ba duk da mugun Riko ya maida Hamza Dan iska me biye da dabar Yan iska. Ita kuwa Salma Allah ne ya shiryi abinshi duk da ikirarin Adama na sai ta watsa Rayuwar salmar Amma Allah ya dubi maraicin ta ya Bata nutsuwa da hankali duk ukubar Adama tana shanye ta inda Kuma fatan da takewa salmar ya fada Kan Yar ta Auta don Yar barkice ta sosai in ma ta bar gida sai ta yi tafiyar ta Legos sai Kuma an ganta Amma hakan Bai damu Adama ba sai cewa da take Wai farin jini gareta.

Auta tana son Salma a cewar ta Yar Uwar tace tunda uban su guda ne shima Zarton nata ne.

Shiyasa Salma ke Dan samun sauki wurin Auta ba kamar yadda Adama ke so ba don har wankin Auta da na Adamar ita keyi sai da Auta tace ta Bari ita a shago ake Mata wanki

Salma ta dawo surfen tuni Kuma ta SHIGA hidimar hada girkin hatsin.

Tuni Kuma ta kammala ta Kuma zubewa Adama sai abinda ta Bata inda Kuma kullum sai tayi Mata Gori Wai ita din ce dai gatan ta

Auta tace ita Kam ba zata ci hatsi ba sai dai ta tafi hotel ta siyo abincin ta

Zarto ya shigo daidai da dawowar Auta daga City Restaurant suka shigo a tare suna kallon kallo shi da Auta don yadda ya tsani Adama Haka ya tsani Yar ta itama da Yake ba shirgin shi take SHIGA ba sanin bashi da mutunci Akasin Salma dake girmama ta ko don Hana Adama da take ta takura Mata

Ya zube gaban Adama Yana gaishe ta inda Auta ke mamaki don Bata taba ganin yayi hakan ba.

Adama ta ce “Kai ku Kam Uwar ku ta cuce ku Bata bar muku gadon komai ba sai iskanci Kai shaye shaye da dauke dauke kanwar ka Kuma malamai na matse ta a aji.

“To Inna ba sai kiyi Mana ADDU A ba?

“Allah ya kwabe tsautsayi da Asara Ni nayi muku ADDU A? Sai dai nayi tsine muku kufi Haka lalacewa

Allah ka ya Kara tsine muku tsinannu Diyan satar kwana.

“Ya sinna Mata kunshin Naman Yana fadin ayi hakuri inna.

Ta karbe kunshin Naman tana fadin.

“Nemi uwar ka can a Bayan gari k’ashin ta ma ai yayi fari

Ya Mike Yana zuwa dakin Salma inda Adama ta warware Naman ta na aikawa ciki Auta tace.

“Ya Kuma Baki nama kin karba kina tsinewa uwar shi Anya kuwa ba wata tsiyar ya kullo Miki ba?

“Kai haba da banci kaza kazan shi ba ? Tayi ta tausa Naman Bakin ta har ta cinye zata Kora da Ruwan tulu Mai sanyi Amma zarto yace ta Bari ya kawo Mata lemun kwalba.

“Shege halan wani ka yashe? Ai Ni na San kudin wani ka sato Allah ya tona ma Asiri.

Bai tsaya sauraren ta ba ya kawo Mata lemun ta kuwa karba ta shanye inda ya barta Yana Mata Dariyar mugunta don duk tarkon da ya Dana Mata ya kamata .

Ta ci Naman da ya bade da magani ta Kuma Sha lemun da ya Kuma zubawa maganin da zai saka ta baccin Dole don Haka sai ya fice

Auta ma ta sheko wanka tazo ta fice don tana da alkawari inda ta wuce zarto a kofar gidan zaune Akan dakalin kofar gidan zuciyar ta ta Raya Mata lallai ba lafiya ta zaunar dashi ba

Fitar Auta ya bawa Adama hangame Baki tana Jan hamma tamki bakin ta zai dare .

“Kai Wai wannan hamma Haka ta lafiya ce? Karfa maganar Auta ta tabbata. Kan kace me? Bacci yayi gaba da Adama tana ta Jan nasari

Zarto ya shigo Kai tsaye ya tunkari dakin Adama ya jiyo ta sai Jan Raguna take ya kuwa sungumo ta yayo waje da ita tana ta shakar bacci dama Ashe yayo hayar Dan sahu ya kuwa shige da Adama rungume tamkar wata Yar baby suka shara aguje inda Kuma hankalin Auta ya kasa kwanciya da ganin ladabin magen da zarto yayiwa Adama duk Ashar din da take ta durawa mahaifiyar shi Amma ya share ta har da kawo Mata nama da lemu ko shakka Bata yi akwai nufakar da yake kullawa don Haka tacewa Mai napep din da ya dauko ta ya jiyo da ita gida

Suka kuwa jiyo dai dai da taga zarto ya sugumo Adama ya SHIGA napep ai kuwa tacewa me napep din ya bi Mata bayan su zarto.

Da sauri ya juya kwana ya bi Bayan su zarto.

<< Hawaye 30Hawaye 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×