Skip to content
Part 32 of 48 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Kai tsaye napep ya shige har cikin gidan Alh Aminu da mutum mutumin Adama dake sharara bacci

Fitowar napep din yayi dai dai da karasowar su Auta inda Kuma me gadin ya maidi kyauren gate din ya Rufe

Zarto ya shimfide Adama da har yanzu take ta shakar bacci Alh Aminu ya Miko mishi Rafar dubu hamsin ya cabe yans murmushi…

“Godiya nake Mai gida. Ya fada Yana shirin ficewa inda Alh Aminu ya tsaida shi…

“Daka ta Ina zaka bar min wannan makauniyar nayi Yaya da ita? “Kar ka damu Mai gida zata maida kanta gida

Auta ta Soma dukan kyauren gate din inda goloko ya bude Yana tambayar ta wurin Wanda tazo Kai tsaye ta bashi amsa tana shigowa Kai tsaye ta tunkari falon saukar Baki da fatan ta wuce tsakar gidan don taga inda akayi da Uwar ta don Haka NE ma suka samu sabani da zarto Wanda ya fice abinshi

Zaman da tayi yasa ta Gane ba Zama ne ya kamace ta ba don Haka ta Soma laluben inda zata gano Kan gidan

Inda Kuma Alh Aminu ya fice don turo Wanda zai fice mishi da Adama tunda an biya Zubaina bukatar ta

Adama da ta farka tajita a wani yanayi ta Soma lalube inda Auta ta hangota tayi saurin karasawa ta kamota.

“Me sukayi Miki Adama? Auta ta tambaye ta.

“Nima ban San abinda ya faru Dani ba Auta inajin dai juwa na neman kayar Dani Rike Ni Kar na Fadi.

Suka taho Adama na fadin Wai me ya kawo Ni Nan ne?

“Shegen zarton banzar can ne na dawo na iske ya dauko ki ya kawo ki Nan shine na biyo ki Allah ya sa ba wani mugun abun sukayi Miki ba.

Adama ta fashe da kuka tana fadin Wallahi an yi min fyade bana iya tafiya.

Dole Auta ta kinkime ta suka fice me napep ya taho dasu Adama sai kuka take tana tsinewa zarto har da Uwar shi dake kwance kushewa.

“Ni dama Raina Bai bani ba Adama nasan Zarto wata tsiyar Yake kulla Miki Amma Kika hadidiyi Naman shi Kika Kora da lemun shi ke da kanki bakiji son tuhumar shi ba tunda Bai taba kwata Haka ba?

“Muje gida kiyi min Ruwan zafi ai Allah ya kawo shegen lafiya na Rantse Miki sai naci kutumar Uwar shi.

Ai Wallahi ko Ni sai na Rama wannan wulakancin da yayi Miki sai ya Gane Nima na SHIGA duniya na kuma iya iskanci.

Da Haka suka iso gida inda Kuma Adama ta Kara matsa lambar ta ga Salma tamkar itace Zarto Amma yarinyar tana hakuri da kawar da Kai inda a kullum sai Adama ta la anci zarto.

Tun daga wannan Rana Kuma shahara ta zamowa Alh Aminu sabuwa komai ya taba sai ya hauhawa tamkar yadda iska ke cika tif din Taya

Tuni duk Asarar da yayi ya linka sau ba adadi yayin da Kuma agefe guda ya jingine duk sallolin da Zubaina ta umurce shi

Sai yanzu ne hankalin shi ya kwanta idan Yana da matsala to Bata wuce cikin Halima ba da Kuma danta Wanda ake ikirarin yafi shi fada da naci jinin shi ma me karfi ne wato Mai Kano

Ya na zaune afalon Yana faman amsa Kiran wayoyin mutane Kan masu kawo karuwa Kan masu neman Alfarma inda Husna da Amal suka shigo ya Kuma bisu da kallo har suka zube gaban shi da son ya Basu kudi zasuje shopping ya Kuma kawo kudin ya Basu Yana Mai mamakin girman Husna Haka

Har suka fice Yana bin bayan husna da kallo.

Duk yadda yake ganin Halima da tsari da matanci husna ta CE ba ta iya komai ba na matanci

Ya Dade cikin hada lissafi kafin ya sauke ajiyar zuciya inda Kuma sai a yau ne ya lura da muhsin Yana fita aiki a maimakon dawowa kamfanin shi.

Yana zaune muhsin din ya shigo da kayan aikin shi inda sukayi ido Hudu Yana mishi barka da gida.

Wato bakaji maganar da na Gaya maka ba ko? To Ina me tabbatar maka da indai aikin ka ka zaba Zan tsame hannu na daga Rayuwar ka kaje kaji da Aikin ka.

“Kayi hakuri Daddy tunda na Fara aikin Ranar da bani da office Zan Rika ziyartar kamfanin.

“In ka Kuma min maganar Aikin ka Zan sharara maka Mari Wallahi

Yayi ta bashi hakuri Amma yace duk abinda ya tashi yayi kanshi tsaye ba sai an sanar dashi ba.

Da Haka ya sallame shi ya fice Ranshi babu Dadi.

Har ga Allah ba don kudi Yake son aikin shi ba sai don yadda Nigeriar mu ta zamo Kiri Kiri ake tauyewa marar gata hakki a kotuna Amma saboda Basu da madafun iko suke hakura shi Kuma ya tashi da wannan akidar ta kwatowa Mai hakki hakkin shi mussamman malam talaka da ake cuta saboda kawai bashi da kudi Amma baccin Haka da zai hakura da Ra ayin shi ya bi na mahaifin shi

Su Husna suka dawo inda Alh Aminu ya hango su ta cikin gilas din tagar shi.

Bai San yadda akayi ba ya samu kanshi da dage labulen Yana karewa Husna kallo ba har suka shige suna ta fama kyalkyala da Dariya ita da Amal.

Tun daga wannan Rana Husna ta tsayewa Alh Aminu a Rai kulawa wadda da can Bai Mata itaba komai zai siyo to zaice na Husna ne ba kamar yadda yake hadesu da Amal ba . A da komai zaiyi musu tare Yake hadewa inda har haj wasila ta saka ido Akan hakan.

Kamar dai yau da aka wayi gari an kawo wata hamshakiyar mota fitowar sabuwar shekara inda haj wasila take faman hura hancin Tata ce tunda ta fada mishi tana son ya sauya Mata mota Tata tana Bata matsala don Haka da taga zuwan motar sai ta dauka ita ya kawowa don Haka ana kawo key din ta karba cikin farin ciki ta Kuma Zo tana dubawa tana yaba yadda motar ta burgeta.

Su Husna suka shigo ita da Amal suna Fadin. “Kai Mami motar waye Haka?

“Tawace Mana duk gidan Nan ba motata bace me matsala? To itace aka kawo min yanzu kun ganta Nan fitar 2020 ce

Suka SHIGA Koda kyan motar har Husna na cewa. “Mami a bamu mu Dano.

Ta kuwa Mika Mata key din ta SHIGA tayi ribas don tuni Yaya muhsin ya koya Mata ya Kuma yi mata alkawarin kyautar a matsayin gift din Auren su.

Sai da Husna ta dawo kafin Amal ma ta karba ta dano ta dawo

Hatta muhsin da ya dawo ya iske motar ya yaba don duk inda aka SHIGA da motar Dole ne ido ya biyo ta. Sai dai me?

Mai gidan ya dawo matar gidan ta Soma da “Naga mota ta iso Kuma ta burgeni Allah ya Kara Arziki..

“Wa ya fada Miki Taki ce? Tayi saurin duban shi da mamaki.

“To ta wacece?

“Duk gidan Nan ai husna ce kawai Bata da mota kums ke waccan motar ai tayi Miki yarinta saboda ta Yara CE don Haka Mika Mata makullin motar Tata ce.

<< Hawaye 31Hawaye 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×