"Ban Gane abinda kake nufi ba? Ya Miko Mata hannu. "Bani key din Nan kafin nayi Miki yadda Zaki Gane. Ta Miko mishi tana binshi da kallo ya karba yana kwalawa Husna Kira
Suka fito ita da Amal inda Amal din ke cewa Daddy gaskiya motar Mami ta burgeni Allah yasa Nima zaka sauya min motar ko da ba irin ta Mami bace...
"Zan sauya Miki mana Amma ba yanzu ba. Ya fada idon shi Akan husna dake kallon Amal.
"Karbi Nan Husna makullin motar ki ne wannan ai Ina Jin yanzu hannun naki ya fada da iya tukin ko. . .