Haka aka dauko Safina cike da cin alwashi Akan Hajiya Wasila don haka Uwar ta ta Dora ta.
Washegari ma da aka yi walima babu Ango Kuma ba a sanar da haj wasila komai ba itama Bata taka taje gidan muhsin din ba duk da dangin su da suka halarta. Haka kuma maimuna ta Hana duk wasu Kaya da Al ada takeyi Wanda ya shafi Uwar Ango da Ahalin ta . Amma Kuma tayiwa Uban Ango bajinta ta kin karawa duk da dai tayi hakan ne don ta jirga haj wasila sai dai abinda Bata sani ba shine Uban Ango fa. . .