Haka aka dauko Safina cike da cin alwashi Akan Hajiya Wasila don haka Uwar ta ta Dora ta.
Washegari ma da aka yi walima babu Ango Kuma ba a sanar da haj wasila komai ba itama Bata taka taje gidan muhsin din ba duk da dangin su da suka halarta. Haka kuma maimuna ta Hana duk wasu Kaya da Al ada takeyi Wanda ya shafi Uwar Ango da Ahalin ta . Amma Kuma tayiwa Uban Ango bajinta ta kin karawa duk da dai tayi hakan ne don ta jirga haj wasila sai dai abinda Bata sani ba shine Uban Ango fa hankalin shi ba kwance Yake ba saboda Rashin ganin nashi farin cikin shiyasa Bai bi ta Kan kayan ba Bai ma San an bada ba .
Inda Kuma haj wasila ta Soma kyautar da kayan tun Akan idon Yan Aiken maimuna da suka kawo kayan. Wasu daga cikin su sun samu wasu kayan inda Kuma saura ta mikawa Mai gadin gidan nasu Kuma duk Akan idon Yan Aiken maimuna . Suka kuma da murna da Kuma tsegumi suka juyewa maimuna yadda akayi har ma da kyautar da haj wasila tayi musu cikin kayan Uban Ango Wanda saura kuwa aka baiwa Mai gadi.
Ta Mike tana Sababi “Me yasa kuka karbo abinda ta baku? Ko Baku fada Mata na uban miji bane ? Ita din ai Bata a lissafi na bare ko tayi zaton nata ne.
“Wallahi mun fada Mata sai dai ko in ji ne batayi ba.
“Ku tashi muje in ma tayi zaton nata ne to ba natan bane don ko Zan tafi kudi na zuba bayana bana Jin Zan iya baiwa wasila kayana tunda akayi walkiya ta hasko min ita Kuma kowa ya tsaya matsayin shi. Taki Allah yaso sai Kuma yanzu ta dawo tace ita din Yar Uwa tace? Na cireta a layin Yan uwana Wallahi.
Haka suka taho tana ta zuba masifa tamkar wasilar na gabanta.
Amma Kuma suna shigowa tayi shiru da masifar da takeyi sai gatsina fuska take inda haj wasila ta gansu tare da su turai dauke da kayan da ta Basu.
“Ya aka yi kuka dawo turai? Maimuna ta karbe a maimakon turan da aka tambaya.
“Sunce ne kin Basu wadan Nan kayan har kina bawa Mai gadi saura shine nazo na fada Miki ba naki bane bare kiyi wannan bugun gaban ai na San dake ana me na Baki kayan Uwar miji?
Fada min Dame Dame kikayi a cikin sabgar Nan da har Zaki ci wannan kayan?
To na me Gidan ne don shi Kam ya fiye min Wanda zaice shi Dan uwa nane ban ga Kuma dalilin da Zaki kasafce mishi Kaya ba.
Hajiya wasila ta daga Mata hannu
“Ke dakata haka maimuna ya isheki.
“Nayi Miki Kama da me jiran wani Abu daga gareki? Shi Wanda kike tunanin ya fiye Miki Dan uwan ne aka nuna Miki dashi da abin shi duk iko ake dasu shiyasa na Rabar da kayan don ki San ba a bukatar su. Ta dubi su turai tana fadin
“Kuje da kayan ku turai Allah ne ya Baku kafin Nan da wata biyu ko uku ku sake cin wasu kayan inda yarta zata Kuma yin wani Auren don Ina me tabbatar muku an Dade anan gidan wata biyu ko uku yarta zata dawo gabanta in har nice uwar muhsin Babu shi Babu Safina sai fa in Uban muhsin zata jonawa wannan Kam tana da daki in yaso sai mu goga Ni da ita kafin Uwar ta tazo taja kayanta in har tana da bukata.
“Uhum to bari mugani ai ba girin girin ba dai tayi Mai Safina ba zata auri Uban muhsin ba shi din dai zata aura Kuma sai ya bauta Mata ko duk mutan garin Nan zasu Kare ki Rubuta ki aje ki Kuma Soma lissafi ba cewa nayi sai ya Aure ta ba Kuma gashi ya Aure ta ba?
“Nima Kuma nace Miki Babu shi Babu ita ba? To kiyi ta duban dawowr Safina a Koda yaushe tunda burinki na Auren ya cika saura nawa na fiddo ta.
“Mu zuba shege ya fasa. Maimuna ta fada tana ficewa.
Su turai dai hakuri kawai suke ta bayarwa suka taho dauke da Kayan su suna son ganin kwam Akan wannan Aure na ya da kanwa Wanda kowa ke Shan alwashi.
Duk wasu kayan shiri da maimuna ta hado Safina dasu tun a Daren da akayi walima Safina tayi komai kamar yadda aka fada Mata Amma har karfe Sha biyu na Dare Babu Ango babu labarin shi inda Kuma magungunan da tayi amfani dasu suka Soma tambayar ta inda barci ya gagareta tayi ta juyi Amma shiru Wai me kalangu ya fada Rijiya.
Husna da ta fice daga gida Bata zame ko ina ba sai kurfi wurin dangin mahaifin ta gidan Anty bashariyya ta sauke zango tana gursheken kuka Wanda Anty bashariyya tayi ta Rarrashin ta kafin tayi shiru tana sanar da Antyn Dalili.
Ta yi shiru tana Nazarin maganar kafin ta tanka.
“Amma bakiyi dabara ba husna ai shi yanzu kin barshi a cikin duhu da ace ya San kina Nan da hankalin shi zai kwanta Amma yanzu ke dashi duk kin saka ku a garari.
“To Ni ta Yaya Zan tsaya ganin ya Auri wata ba Ni ba? Kadan ya Rage Anty bashariyya ta fashe da Dariya Amma sai ta share ta tambaye ta.
“To shi ya fada Miki Yana son wadda aka bashi ne?”
“Bai ce ba Amma irin kallon da Naga tana yi mishi ai wata Rana zaice Yana son ta ko? Anan Kam sai da tayi Dariya inda Kuma Husna ta karawa kukan ta sauti Jin Antyn na Dariya.
“Kinga yanzu Ni da zakiji shawara ta sai nace ki koma Kinga yanzu duk ki saka mutane da yawa a shakku da firgici kuma shi Wanda kike wa ai bakiyi mishi adalci ba indai kikaci gaba da boyewa kamar yanzu ke Baki huta ba shi Bai huta ba to meye amfanin badi ba Rai Wai ba a shekara lafiya ba?
“Ni Wallahi ba Zan koma ba Anty.
“To dama karya kikeyi ba son shi kike ba.
“Wallahi ba karya nake ba kawai dai tunda ya Aure ta shikenan.
Duk yadda Anty bashariyya taso ta koma ko ta Kira Yaya muhsin Amma Taki Dole ta kyale ta Amma Kuma tafi kowa ji ajikinta.
Shi kuwa muhsin tunda ya bar gida sai ya koma gidan wani abokin Aikin shi hamis shima bashi da Aure inda Bai boyewa hamis komai ba tsakanin Auren shi da Safina da kuma soyayyar Husna inda hamis din ke fadin ya karbi Safina a matsayin matar zabin iyayen daga baya Kuma sai ya Auro Husna zabin zuciya Amma baya Jin zai karbi Safina Koda husna ta samu.
Haka yayi zaman sa a gidan hamis Amma kullum Yana binciken inda zai samo labarin Husna.
Bai fashin zuwa aiki sai dai da ya dawo baya komai sai buge bugen waya gidajen Yan uwa ko zai samo labarin Husna.
A yau ne Hamis yayi mishi wata tambaya akan ko su Husna suna da dangi a wani garin?
Ya Mike a firgice Yana fadin.
Kwarai kuwa suna da dangin baban su a kurfi.
“To bana ko shakka Husna tana can in Kuma Bata can to ba zasu Rasa labarin ta ba.
“Yanzu kuwa Zan nufi garin kurfi duk da ban taba zuwan shi ba to yau zanje.
Ya Suri key din mota yayi waje da sauri inda Hamis ya biyo bayan shi Yana fadin.
“Bari nazo muje tare Koko ba a gayyata ta?
“Ai in nace kazo muje kana iya kawo min kauli Amma idan zaka Rakani ai Zan so.
Haka suka bugi hanya Hamis na nuna mishi hanyar har suka iso garin kurfi da tambaya suka gano gidan kakanin su Husna inda Kuma aka sanar dashi tabbas Husna tazo Amma tana gidan bashariyya tuni ya Roki da ahada shi da yaron da zai sada shi da Anty bashariyya Ashe ta kofar gidan ma suka wuce.
Ya tura Kiran ta inda tacewa yaron yazo yace ba zata fito ba don yadda takeji Babu wani namiji da zata kula ta ma gama soyayyar tunda daci gareta ba Zaki ba kamar yadda ake fada.
Anty bashariyya ce ta matsa da lallai sai ta fita kamar yadda me Aiken ya matsa da son ganin ta.
Ta fito a fusace da son tayi kashedi Akan me son ganin ta inda kuma idon su ya hadu da bakon nata Wanda ganin shi ma ya tado Mata wani Miki sai kawai ta fashe da kuka ta koma cikin gida aguje tana kuka inda Anty bashariyya ta bita da kallo.