Skip to content
Part 42 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Kukan da shigo tana gurzawa ya bawa Anty bashariyya tsoro har bata biyo ta kanta ba ta zari mayafi ta fito waje don ganin abinda yasa ta kuka.

Muhsin da Hamis suka zube suna gaishe ta ta amsa a mutunce tana tambayar su daga inda suke.

Muhsin ne yayi Mata bayani inda ta Gane shine saurayin da Husna kewa kuka don Haka tace su shigo cikin gida.

Ta sauke su a falo ta kawo musu Ruwa inda suka nemi taimakon ta sada su da Husna.

Husna dake ta sharar kuka kamar wadda aka sanar mutuwar iyaye duka.

Anty bashariyya ta dubeta tana fadin
“Ke dai sakarai ce wallahi wannan ko Auren akayi indai da Safina zai hadaku to cikin Ruwan sanyi kishiya zata kwace miji a hannun ki. Baki da wayo fa Husna Sam.

“To ni ya zanyi Anty kike ce min zai hadani da Safina? Ai Auren ba Dole bane Wallahi Kuma tunda ya Aure ta Ni kice ya kyale ni.

Anty bashariyya tayi murmushi don ta Gane kishi ke wahalar ta don Haka sai ta nuna Mata abinda Bata fahimta ba.

“Kinga Ni yanzu share hawayen ki in fada Miki yadda Zakiyi muhsin ya dawo hannun ki Kuma ba zai taba son wata mace bayan ke ba.

Da sauri kuwa ta share hawayen tana duban Anty bashariyya.

“Yanzu da Kika baro shi muhsin din a waje me kike nufi? Kin barwa Safina kenan? To kuskuren farko kenan da Kika tafka kamata yayi kiji dalilin da ya kawo shi Kuma ai tunda ya biyo ki Nan karshen so kenan da baya son ki da zai biyoki ne? Ai da zai Rungumi Amaryar shi ne ya manta dake.

Da sauri ta Mike tana saka hijabin ta tana nufar kofar fita ba ta ko tsaya Jin karshen bayanin Anty bashariyya ba ta fice Antyn ta bita da kallo Baki sake kafin ta kyalkyale da Dariya.

Kai sabon SHIGA a soyayya dai akwai kayan haushi da takaici Wallahi. Maza marmari daga nesa Aure yakin Mata manya na tsoron ka Yara na Haye maka.

Husna da ta kinkimi Ruwa da lemu ta shigar wa Yaya muhsin dashi ba ta San Antyn ta Basu ba ta dire tana musu sannu da Zuwa. Hamis ne ya amsa Yana kare Mata kallo don taci a gigice kamar yadda abokin shi yayi
Shi kuwa muhsin ido ya zuba Mata kafin ya Riko hannun ta Yana kallon kwayar idon ta suka zubawa juna ido ita HAWAYE shi Kuma Jan ido saboda tashin hankali.

“Me nayi Miki kikayi min Haka darling? Anya kuwa na cancanci Haka wurin ki?

“Kar kaga laifina Yaya muhsin ban sani ba ko Anty Safina ta samu SHIGA a zuciyar ka shine kawai nake ganin babu Amfanin Zama na agidan ku tunda kayi Auren ka Nima sai na jira mijina anan.

“Kin dauki alhaki na Husna. Kin manta da maganar da na fada Miki? Kin manta da nace Miki ban taba son Safina ba a Rayuwa ta itace ke haukan ta? Ke kadai nake so idan Kuma kin barwa Safina to Zan hakura naje na karbi Safina zabin iyayena tunda na Rasa ki nasan na Rasa farin cikin Rayuwa.

“Ba Zan taba barwa Safina Kai ba Yaya muhsin Kaine mahad’i na Rayuwa ta.

“Idan Haka ne sai ki tashi mu koma gida don Nima tunda Kika baro gidan har yau din Nan ban Kuma waiwayar gidan ba.

Da sauri kuwa ta tashi ta koma inda Anty bashariyya taga tajawo trolly tana Kara gyara zaman hijabin ta.

“Yo Ina zuwa Haka Kuma? Ta tambaye ta.

“Zan koma ne Anty bashariyya ya bani hakuri Kuma na hakura.

“Uhum to dama ai fadan masoya hutu Husna Allah ya kiyaye Amma Kuma da kin Bari zuwa gobe na sama Miki Yar tsaraba ko?

“A a Anty yau dai Zan koma ki bar kudin ki na gode sai munyi waya.

Ta fada tana ficewa daga gidan inda su muhsin suka shigo suna Mata sallama har suka Bata Yan kudi suna fadin zasu wuce ne tare . Anty bashariyya tayi musu godiya ta Rako su har mota inda Husna ke dago Mata hannu itama ta daga Mata suna murmushi har motar ta kule tana Dariyar Husna.

Shigowar su yayi daidai da fitowar Alh Aminu inda ya zubawa motar muhsin ido Yana tsaye Yana kallon motar yana tuna Rabon da yaga muhsin a gidan tun bacewar husna. Bai tsinke ba sai da yaga Husna ta fito daga motar inda yaji gabanshi ya Sara.

Suka zube gaban shi suna gaishe shi.

“Husna Ina Kika shige Kika tada hankalin mu Haka?

“Kurfi na samo ta Daddy.

“Wani Abu akayi Miki ne Haka da fusata ki har Kika bar gidan Nan Husna? Nifa a matsayin mu azu nake wurin ki Kuma Nan din gidan ku ne uhum?

Ta sunkuyar da kanta tana Jin nauyin fada mishi Auren Safina ne yasa ta barin gidan don haka sai kawai tace mishi ba komai.

Suna SHIGA falon Amal ta taho tana Rungume Husna tana tambayar ta inda taje.

Muhsin ma ya shigo Amal ta kwadawa haj wasila Kira tana fadin ga Yaya muhsin da Husna.

“Har ya gama yajin ne da wuri Haka? Cewar haj wasila dake fitowa daga dakin ta inda kuma tayi Arba da Husna abinda Kuma baiyi Mata Dadi ba don har ga Allah Bata maraba da Auren Husna ga muhsin. Suka zube Agaban ta suna gaishe ta inda take tambayar muhsin inda yaje Amma Bata tambayi Husna inda taje ba inda shi kuma ya Bata amsar da ta kusa kasheta don ya fada Mata neman Husna yaje nema Kuma ya samota.

Safina kuwa da ta kwashe sati uku cif a gidan ba tare da ta leko sashen haj wasila ba bare gaisuwa ta kawo ta ko kuma irin kyautar abincin Amarya ba ta taba kwata Haka ba amma yau da taji shelar dawowr muhsin din sai gata ta garzayo cikin Ado da kwalliya suna zaune shi da Husna suna zanta matsalar su sai ganin Safina sukayi tsaye akan su Kuma ba zato bare tsammani sai Jin saukar Mari Husna taji a fuskar ta tana zazzaga masifa.

“Ke karere kafi Dan gida fita daga idona in Kika Kuma Bari na Kama ki kina fira da mijina sai nayi Ajalin ki Wallahi don bana Jin Zan barki kiyi min.

Bata karasa ba taji Barin makauniyar da muhsin yayi Mata Yana Nuna ta da yatsa Yana Huci.

<< Hawaye 42Hawaye 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×