Skip to content
Part 43 of 54 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

}

 

 

 

Bai sauke hannun shi daga Marin Safina ba yaji saukar Mari a tashi fuskar Alh Aminu ya Mai da mishi nashi Marin cikin masifa da kumfar Baki.

“Wane irin yaro ne Kai? Matar Auren ka kake wulakantawa ? To daga yau na haramta maka Zama anan bare Kuma fira da Husna tunda matar ka Bata so. Idan Kuma ka Kara Kai hannu ajikin matar ka da sunan duka zaka Sha mamaki tashi ka fice min anan Kar na Kuma ganin kafar ka anan na sallame ka kaje can sashenka in ma gaisuwa ce ke kawo ka Nan to na sahale maka gaisuwar. Uwar ka Kuma ka Kira wayar ta in bukatar hakan ta taso in Kuma Amal kake son gani ka Kira ta zata Zo Amma Nan sashen bana bukatar ganin ka.

Safina dake kuka ta nufi sashen su tana sharar HAWAYE inda Dole ya bi bayan ta Yana Jin ko kusa ba zai taba yin abinda ake son yayi ba don babu karsashin hakan a Ranshi.

Tuni Kuma Husna ta SHIGA taitayin ta don ta kula da gaske ake son Raba su inda ta tashi ta nufi daki ta iske Amal kwance tana karatun wani littafi YARDA DA KADDARA ta dago da salon zolaya tana fadin.

“Kai Husna Ina ma zaki karanta littafin Nan Wallahi soyayyar ciki ya Asmau da Abba lawal tayi min Kama da taku da Yaya muhsin Kai wannan littafin yayi min Dadi wallahi Ina ma Zan samu so da kulawa irin wadda ma.u ta samu ga Abba lawal wurin Gayen da yayi min tsaye a Rai na kasa manta shi? Sai ta Soma fitar da HAWAYE sai Kuma tausayin ta ya Kama Husna don ita Bata Kama masoyin ba ma bare taga takun nasu me yuwa ma yace ba kalar ta Yake muradi ba Akasin ita da ta samu take Kuma ganin tana neman Rasawa

Ta dafa kafadar Amal tana Bata Baki “Ki yi hakuri Anty Amal komai da Kika gani Allah ne ke yin shi inaji ajikina Gayen can zai dawo wata Rana Allah yayi Mana jagora Nima yanzu kinji abinda daddy ya fadawa Yaya muhsin? Wai Kar ya Kuma shigowa Nan sashen ya tsaya can shi da matar shi Kuma daga Safina tazo ta ganmu zaune shine ta mareni Amma Daddy ya Mari Yaya muhsin don kawai ya Rama min.

“Husna da Akwai abinda Daddy Yake nufi ko yake son yace ke dai kiyi taka tsantsan.

“Koma me Daddy zaice bana Jin zaiyi nasarar Raba zukatan mu da Yaya muhsin Kuma Nasha alwashin ko da za ayi me wallahi ba Zan taba barin Yaya muhsin ba ko da Safinar ne na yarda ya hada mu Zan iya da ita ai ba karfi bane kishi miji ya yarda da Kai shine ya Kuma soka ya kula da Al amarin ka shine kishi.

Wayar ta tayi Kara ta jawo ta inda taga sunan Mai Kano ta daga da sauri tana gaishe shi inda Yake fada Mata gashi yazo a garin katsina ta fito su gaisa.

Da sauri ta Mike tana fadawa Amal tazo ga yayan ta Mai Kano yazo su gaisa Suka taho da Amal inda suka hango shi shi da Yaya muhsin a zaune Akan kujera har muhsin din ya kawo mishi lemu.

Tun daga nesa idon Amal ya hango Mata Mai Kano Wanda taga ya Kara haiba da kwarjini take zuciyar ta ta dauki Rawa.

Sai dai fuskar Mai Kano a daure babu sassauci don neman Alh Aminu yazo muhsin yake fada mishi yanzu ya fita kuwa don Haka ko Ruwan da muhsin ya bashi Bai Sha ba.

Amal ta kafe shi da ido tana kallo shi kuwa kallo Daya yayi Mata ya maida hankali ga Husna wadda yaga girman ta tamkar ba ita ba

Suka gaishe shi inda Husna ke tambayar har yanzu Babu labarin mamar su?

“Za a ganta Husna Ina sulaiman? Ya tambaye ta inda muhsin ke fada mishi Yana Isa kaita dake Dutsin ma can Yake bording school.
Ya Mike Yana bawa muhsin hannu Alamar zai tafi ya Ciro kudi ya mikawa Husna yace su Raba ita da Amal ya Kuma fita muhsin na biye dashi don yayi mishi Rakiya.

“Wai abokina lafiyar ka kuwa Naga fa baka da walwala. Cewar muhsin da yaga Mai Kano ya fiye cin magani don da can abokai ne na Sosai.

“Ba komai muhsin Raina ne baya yi min Dadi Ina da damuwa ne.

“To Allah yayi maka magani mutumina sai yaushe kenan? Zamuyi magana da Haka ya tsaida acaba ya wuce ya bar muhsin.

“Husna wannan shine Yaya Mai kanon da na sani Wai? Shine mana ya sauya Miki?

“Uhum Husna ko kinsan shine mutumin da nake fada Miki Ina so? Shine mutumin da nake kwana da tashi dashi a Rayuwa ta? Don Allah ki taimake Ni Husna Wallahi Zan iya Rasa hankali na Akan shi me Zakiyi akai?
“Kar ki damu indai Yaya mai Kano ne ki kaddara kin sameshi kin gama ai ban sani ba da Bai bar gidan Nan ba sai da guzurin kaunar ki.

“Yanzu dai bani lambar shi sai na Kira shi kawai. Husna ta karanto Mata lambar ta shigar a wayar ta kafin ta Danna mishi Kira ya kuwa dauka inda ta lankwashe murya tana fadin ta bugo don tayi mishi godiyar kudin da ya Basu.

“Ok kawai ya fada ya kashe wayar shi

Safina ta rangada girki Wanda yaji makaman Aiki don samo zuciyar muhsin Amma sai jiyowa tayi Yana fadawa Husna irin girkin da Yake so tayi mishi . Mintina kadan ma ya fice ya barta da nata girkin. Bata tsinke ba sai da Dare yayi Tayo shirin zuwan turaka ta iske ya datse Dakin shi Kuma tanajin takaicin bugawa Dole ta juyo na ta murkususu saboda maganin da kwankwada ya isheta ya Dame ta Amma da kyar ta Kai safe inda ta SHIGA Dakin muhsin da son lallai sai ta cika buri amma yayi Mata Jan ido kafin ya fada Mata ya taba ce Mata Yana son ta? To ta fita idon shi ya Rufe Kuma zaman da takeyi zaman Daddy take ba zaman shi ba kuma zaman lokaci take Husna kawai Yake so Kuma da ya Aure ta zai sallame ta.

Ai kuwa Safina ta nufi sashen haj wasila wurin Daddy tana kuka Wai muhsin yaki sauke hakkin ta ko kunya Babu ya kuwa isko muhsin Yana zazzaga masifa Amma ko ajikin shi ba Kuma zaiyi hakan ba.

Duk yadda yake son ya likawa muhsin Safina da son lallai sai ya Raba su day Husna Amma ya kasa Raba su don Haka yaga hukuncin karshe da ya kamata ya yanke shine kawai ya Kai maganar ga hajiya ta son Auren Husna in ba hakan yayi ba muhsin ba zai taba Barin shi Zama lafiya ba don Haka ya nufi masanawa gidan haj kulu.

<< Hawaye 42Hawaye 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×