Skip to content
Part 46 of 48 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Safina Bata San lokacin da su Amal da Husna suka shigo ba har zuwan haj wasila da ficewar su dashi zuwa Asibiti duk bata sani ba saboda tsabar haushi da takaici na Rushewar burin ta dole ta kwana juyi da tsinewa ciwon da ya kawo mata tazgaro akan muhsin.

Washegari ta sheko wanka na neman fitina inda take godewa Anty maimuna da ta samo Mata turaren Nan tunda dai tayi me wahalar wato samo zuciyar muhsin ai ta gama Babban aikin ciwo kuma yayi ya gama.

Ta fito inda ta taka Aman da muhsin yayi a Daren jiya sai kawai ta lailayo Asher.

Dole tayi Aikin kwashewa tunda ba Yar Aiki gareta ba Amma tunda ta samo muhsin Yar Aikin ma zai kawo ta.

Ta gama Aikin ta Kuma kunna CD Wanda ya cika gidan da hayaniya har bataji shigowar haj wasila ba saboda merming din wakar da takeyi da bakinta.

Batayi aune ba taji saukar Mari Akan fuskar ta inda ta firgita don batayi zato ko tsammani ba.

Ta juyo idon ta ya fada Akan haj wasila dake Huci wadda ta fincike wayar CD tayi shiru kafin ta Dora

“Uwar ki ma Bata Isa ba Wallahi bare ke kayan banzan da Basu Kai na wofi ba Yan iskan karshen zamani.

“Kar ki Kuma zagin Uwa ta don wallahi Zakiyi nadama me nayi Miki Kika mareni? “Uban ku ma zanci ke da Uwar Taki. Fada min abinda kuka yiwa muhsin wanda ya kaishi gadon Asibiti?

“Me mukayi mishi fa ciwon so ne ya kamashi Kuma Wallahi sai kun gane kuren ku ke dashi don sai na mantar dashi ke sai fa idan ya ganki ya tuna dake Amma yadda Kika wulakanta mu Ni da Uwa ta kema kinyi bankwana dashi har abada shege ya fasa tsakanin Ni da ke.

“To Bari na Fara dake kafin na koma Kan Uwar ki inda za a gano shegen da zai fasa.

Sai kuwa ta Rufe Safina da duka tamkar ba zata barta ba inda itama Safinar tace itama fa ta iya suka Soma dambe Amma duk da Haka haj wasila tafi karfin ta.

Duka na Sosai tayi Mata irin na Shan gishiri kafin ta jawo ta da nufin zuwa ta kaiwa maimuna ita.

Sai sukayi kicibus cikin wani Arashi Domin ko Anty maimuna ta Garzayo Domin taji inda aka kwana tsakanin muhsin da Safina don da nufin karbar kudin da tasa safina tazo sai Kuma ta iske wani Alamari Safina fuska na yoyon HAWAYE da majina.

“Yauwa Dama gida zanje na mayar Miki da yarki ai idan Baki manta ba na fada Miki Zan dawo Miki da yarki gabanki? To gata nan kije da ita ki Kuma saurari karasowar takardar sakin ta daga muhsin yau din Nan zai Aiko muku da ita.

Sai nace ku sake sabon malami wannan fahamin dai na karya shi da ana bada sakin Nan ma da nice Zan saki Auren Safina Amma kuje Zan nuna Isa ta a inda na isa.

“Ai in Kinga safina ta bar gidan Nan wasila to gawar muhsin aka dire a gidan Nan wannan ne fa zata fita don zaman shi take ba naki ba. Kuma albishirin ki kice Dani farin goro malamin da Kika karya fahamin shi shine me sakewa Safina sabon lale ki Kuma Rubuta ki aje ai tunda Safina tayi nasarar shigowa gidan muhsin to ya Zama Dole ya karbeta don Haka Babu inda zataje wallahi.

“Kice kuwa jikin ku zaiyi tsami don yadda na tsaneku komai zai iya faruwa Kuma Bari ki gani
Ai kuwa ta Soma jibgar su duk da kokarin da Anty maimuna ta so kwatawa Amma ta kasa dama dai ita Safina jiki yayi tsami Dole suka fice a guje.

Kwanan muhsin Biyu a Asibiti aka sallamesu ya dawo gida inda Kuma haj wasila ta Miko mishi biro da takarda tace ya karba ya Rattabo wa Safina saki uku kwarara.

Ya karba hankalin shi kwance don shi da kanshi ya yanke wannan shawarar sai gashi Mami ma ta Raya hakan a ranta.

Ya kafa biron zai fara rubutu yaji muryar Alh Aminu na fadin.

“Idan har ka saki Auren Safina kamar yadda uwar ka ta bukata Ni kuma Zan tsine maka Albarka adadin yawan sakin da kayiwa Safina…..

Da sauri ya saki biron jikin shi na Rawa. Haj wasila ta dube shi fuska murtuk tana fadin,

“Meye Haka Kuma? Baka da labarin ko Ubangiji sai da ya ambaci uwa har sau uku ba kafin ya ambaci uba ba? Zaka bar abinda na saka ka saboda maganar shi? Muhsin ya dubeta idon shi ya kada jajir.

“Mami bakiji abinda yace ba? Ta daga mishi hannu Alamar dakatarwa.

“Ya isheka Kai kaji ko? Zakayi abinda na saka ka ko kuwa? “Mami wa zanyiwa biyayya a cikin ku?

“Idan Baki saki Auren Safina ba Nima Zan tsine maka Albarka adadin yawan maganar da kasani. Kanshi ya Kuma juyaw ya dafe kirji ya Mike Yana layi kafin ya tafi Rica, Ya zube akasa ya suma.

Da sauri Alh Aminu ya juya ya bar haj wasila da sallalami tana sheka mishi Ruwa har ya kawo nunmfashi ta shiga jera mishi sannu yana Hawaye.

Dole ta saurara da maganar sakin Safina amma fa da alwashin hakan Aran ta. Sai dai me? Dawowar da Alh Aminu yayi sai gashi tare da Safina har da Anty maimuna Wai ya dawo wa da muhsin da matar shi

Anty maimuna tana yamutsa fuska take fadawa Alh Aminu cewa.

“To Alh Aminu kasan dai girman ka ne kawai yasa na yarda Safina ta dawo ka fadawa matar ka ta cire idon ta Akan Safina da mijinta don ba zaiyuwu ba kici zamanin ki kici na wata don dai tana takamar Dan ta aka Aura. Idan kuwa tace ba Haka ba Zan bawa Safina damar yagata idan tace zata shiga hurumin ta don tun tafiya batayi nisa ba naji Auren Nan ya fita a Raina saboda mugun halin surukata.

“Idan ma har wasila tayi kokarin raba auren nan to ki tabbatar itama nata Auren ba zai tsira ba Wallahi.

“To Haka dai yafi Wallahi.

Cewar Anty maimuna dake kyalkyala Dariya ta kuma karbi makullin sashen Safina suka fice ita da Safina ta bisu da kallo kafin tayi murmushin mugunta.

“Indai nice uwar muhsin Babu Ranar da zaiyi zaman Aure da Safina indai nayi nasarar Raba su to Aure na ma don ya tsinke huta Roro waken gizo yaki Ya’ya ai na Kai minzalin da zanyi zaman Yaya ka sake Ni Mana ka gani idan Zan matsa Nan da can?

“Kin dai ji abinda na fada ko? To don Allah kiyi sanadin da Kika Raba Auren ki gani sunan ku zai zamo daya wato jawarori. Da Haka ya fice ya barta da yi mishi Rakiya da idanu.

Saura sati guda daurin Auren shi da Husna inda yazo wurin hajiya bayan sun gama tsare tsaren su hajiya ke tambayar shi matar shi dai ta San halin da ake ciki kuwa? Ya fada Mata Bata sani ba saboda in ta sani ba zata barshi Zama lafiya ba shiyasa ya barta har sai an Kai Husnar tunda kowa wurin shi daban Hajiya Bata hango wata matsala ba sai ma cewa da tayi.

“Kayi dabara da kayi hakan don Haka idan ka koma gida sai ka turo min Husnar Nan don ta Soma shirye shiryen ta tunda yau saura kwana bakwai da Haka ya karaso gida ya samu Amal da Husna har ma da Yaya muhsin zaune suna fira abinda ya kashe shi da haushi har ya hau masifa da kumfar Baki tamkar zai Rufe muhsin da duka. To maji ma gani Wai an binne tsohuwa da Ranta

<< Hawaye 46Hawaye 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×