Masifar da Alhaji Aminu ke zubawa ta bawa su muhsin mamaki tamkar Wanda ya kamasu da kayan laifi. Sai da suka bashi hakuri kafin ya nufi saman benen shi Yana fadawa Husna ta sameshi a saman.
"Na Rasa abinda mukeyiwa Daddy Haka da zafi da Yake yawan fada musamman idan ya ganmu da Husna ban San Dalili ba.
Husna ta Mike zata bi bayan Alh Aminu dake Kiran ta Amma sai Amal ta Riko hannun ta ta dawo ta zauna
"Yaya muhsin ya kamata ka San abinda kakeyi na Rantse maka in ba sannu kayi ba to Daddy zaiyi maka. . .
Ma sha Allah