Mai Kano yayi maza ya Rike hannun hajiya dake ta jibgar Husna tamkar wadda aka Aiko sai dura mata Ashar take Wai tayi butulci Akan tace Bata son Alh Aminu.
Hajiya Bata San da zuwan Mai Kano ba sai ganin shi tayi yana rike mata hannu.
Ta dubeshi tana mayar da numfashi sai kace wadda tayi gudun fanfalaki.
"Haba hajiya me tayi Miki haka da har kike Mata irin wannan dukan Kuma kina yi kina zaginta ? Ya fada Yana zuba Mata idon shi da ya gama cika tab da masifa.
Hajiya ta kwada mishi harara tana fadin. "To ko zaka. . .