Skip to content
Part 6 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Halima na gindin injin makarde tana markaden waken Awara, Mubarak da Zaidu suka fito cikin kayan makaranta suka fice amma bata ga keyar Mai Kano ba. Don haka cikin sauri ta karshe makarden ta kashe injin din ta nufi daki.

Yaron dan kimanin shekaru sha biyu yana ta dininiya don dai kar yaje makaranta ya jawo wannan ya saki ya kamo wannan ya saki.

Ta daga labulen tana kallon shi. “Sannu uban shiririta kowa ya tafi sai kai kadai me kuma kake jira?

Ya jawo jakar makaranta yana fitowa har ya kusa ficewa sai kuma ya dawo.

“Yauwa Mama dama ina so na tambaye ki wai malamin mu na makarantar islamiya yace duk abinda yaro ya zamo daga uwar sa ne wai haka ne? Ta zuba mishi ido kafin ta amsa mishi.

“Haka ne mana kana kokonto ne akan abinda malamin naku ya fada?”

“A’a Mama to in haka ne ni dai don Allah ki yi min ADDU’A in zama Maikudi. Wallahi na gaji da zuwa makarantar nan . Ya fada da tabbaci.

“Ni kuwa kaga nafi son ka da karatun nan tunda shine gatanku. Amma kudi sau tari suna zama kalubale.

“To ai Mama in na samu kudin komai ma sai nayi…

“To Allah Ubangiji Ya baka kudi na halal Kuma masu Albarka Amma fa kasani karatu ya zame maka jazaman don Haka wuce ka tafi ADDU’A ka roka na kuma yi maka to ina fatan Allah Ya amsa.

Ya wuce ya tafi ba don yaso ba sai dai ya na fatan Ubangiji ya amsa ADDU AR mahaifiyar tashi shi kam aduniya yana da kulafucin son kudi.

“Allah Ya shirye ka Mai Kano ya shiryi dabi’ar ka.

Ta soma shara kenan ta jiyo kugin mota a waje amma ba ta yi zaton nan gidan aka zo ba. kamshin turaren shi ya fara yiwa hancin ta sallama kafin ya karaso da sallama idon shi ya sauka akan Halima.

“A’a kai wata sabon gani Alhaji Aminu sannu da uzwa. Ta aje tsintsiyar ta na dauko mishi tabarma ta shinfida tana bude fridge ta dauko mishi lemun zobo da ruwan leda.

Bayan sun gaisa tana tambayar Hajiya Wasila da Muhsin da Amal. Ya amsa da kowa lafiya ya kuma dora da tambayar me gidan wato Mu’azu.

“Ai kuwa yana shago amma bari na kirashi ta waya…

A’a bari na kirashi har yanzu yana nan yana dinki n? Ya tambaye ta.

“Yana Nan kuwa Yanayi.

Ya kira wayar Mu’azu ya sanar dashi gashi yazo gidan idan babu damuwa yazo su gana. Da yake kusa ne da gida shagon yake sai gashi ko minti goma ba ayi ba ya karaso…

“Amma dai mutumina batan hanya kayi ko?

“Eh sai kuma aka yi sa’a na fado gidan abokina. Suka yi musabaha suna tambayar iyali da bayan rabuwa.

“To dama dai nine me sadar da zumuntar nan indon ta kai ai da ba ayi ba Aminu…

“Kaima din da kake yi ai ka yanke…

“Ba yankewa nayi ba sabgogin ne dai da suka yi yawa. Suka bude fejin fira ta yaushe gamo har misalin Sha biyu na rana inda Alhaji Aminu ya kawo musu abinda ya kawo suka yi murna da godiya ya kuma kawo kudi har dubu dari Biyu ya bawa Mu’azu ya bawa Halima dubu hamsin yayi musu sallama ya wuce.

Allah sarki rashin sani anzo har gida an siyi ruhin sa ba tare da ya sani ba kaico da tarayya irin ta cuta.

Rayuwar ta samu sauyi saboda wannan tallafin da ake ganin ya samu ashe kuka ne zai biyo baya.

Anyi wa yara dinkuna da takalma da sauya musu kayan makaranta da littatafai. Kuma miyar gidan ma ta sauya kullum za aci me dadi a kuma sha da dadi ana ta godewa Ubangiji. Sai dai me?

Sati guda daya tak da ziyarar ta Alhaji Aminu Mu’azu ya fita wurin da yake dinki ko awa daya ba ayi da fitar tashi ba sai gashi ya dawo afujajan kai na ciwo, wanda yake jin tamkar kan zai tarwatse. Kan kace kwabo zazzabi me zafi ya rufe shi. Halima da kanta ta fita ta siyo mishi magani Amma tamkar ta karawa ciwon azama. A wannan rana Mu’azu ya kwana cikin wahala washegari dole aka dangano da asibiti aka shiga neman lafiya magani da ban ciwo da ban.

Tsawon sati Mu’azu na kwance gadon Asibiti Amma babu sauki sai wurin Ubangiji. Yayin da aka shiga kashe kudi Amma dai abanza. Har ta Kai Dan sauran tallafin da aka samu duk sun shige a jinya, Kuma saukin Bai samu ba. Halima hankalin ta yayi masifar tashi har tana kokarin saka injin dinta da fridge kasuwa ta siyar a nemawa Mu’azu lafiya inda hajiyar ta ta hana akan wai yaushe zata siyar da kayanta su shige a cikin ciwon Miji? Bata manta ba dama hajiyar ba wai yin Mu’azu take ba don dai Allah ya kaddara shine mijinta . Ita hajiya so tayi tayi auren kudi shiyasa bata faye bawa Mu’azu muhimmanci ba.

Halima ta ciwo bashi da nufin zata siyar da kayan sana ar tata ta nemawa mijinta lafiya

Kullum cikin kashe kudi ake amma lafiya tayi wuya. Mu’azu da ke cikin halin ciwo shi ya nemi sallama wai su koma gida. Dole aka sallamesu suka taho Halima na tsegumin yaushe zasu dawo gida alhalin yana fama da ciwo?

Ranar da suka dawo gidan a ranar ne kuma bakon lamarin ya soma inda jini ya soma fita ta kofofin hancin shi tamkar hab’o. Abinda ya Ruda Halima kenan.

Duk wata hikima da dabara da tasan ana yiwa me hab’o ta jaraba amma babu sa a. Haka Mu’azu ya kwana cikin jini face face kafin gari ya waye ya bata riga uku .

Halima kuka yaran nata kuka inda suke tausayawa Mu’azu. Bayan ta turasu makaranta ne ta Kuma Nemo Rancen kudi don maida mu azu Asibiti. Amma Sai me? Yace ta hakura da zuwa Asibiti don lokaci kawai Yake jira.

Duk yadda taso ta lallabeshi Amma ya kafe dole ta hakura tana kuka tana shafa mishi kankara akan hancin shi. Har tayi nasarar jinin ya tsaya. Sauki Kuma ya samu Amma fa ya dashe yayi wani irin haske fayau.

Wannan iyalai sunyi murna da samuwar jigon nasu suna kewaye dashi har dare suka ci abinci tare uban na sakawa kowane su Albarka Akan rayuwar sa da burin sa. Mai Kano ya kamo hannun shi.

“Abba don Allah kayi min ADDU A na samu kudi nidai wallahi Ina son kudi.

Mu azu yayi murmushi. “To Allah ya baka masu Albarka ya Kuma azurtaku da halal.

“Ameen Abba Allah ya baka lafiya.

Haka suka gama firar kowa ya kwanta sun dade da Halima itama Yana zubo Mata ADDU OIN kafin suka kwanta.

Can tsakiyar Dare ta farka taganshi zaune jini na tsiyaya ta hancin shi ga jijiyoyin kansa sun fito Rada Rada.

“Ya subhanallah Mu’azu jikin dai? Ta fada tana bude fridge ta dauko kankara tana goga mishi .
Ashe wasa farin girki.

Kan kace me kamannin Mu’azu sun jirkice jini kuwa har ta cikin kofofin kunnuwan shi da idanun shi zuba yake abinda ya firgitata.

Ta koma tasbihi da neman daukin Ubangiji. Ta rungume Mu’azu tana tofeshi da ADDU OI yayin da jikinta yajike da jinin da ke zuba.

Tana ji yana ambaton kalmar Shahada cikin Aminci Mu’azu yace ga garinku nan.

Ubangiji ka Azurta mu da kyakkyawan karshe in Ajalin mu ya gabato ka bamu Mai sauki mu Isa muna masu Imani

Wanda suka je Kuma Ubangiji kayi Rahama a garesu kayafe laifukan su ka sanya su a kyakkyawan matsayi.

<< Hawaye 5Hawaye 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.