Skip to content
Part 69 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Alhaji Bello ya dubi muhsin dake fitowa a mota ya karasa suka gaisa Yana tambayar shi don Allah ko shine barrister muhsin Aminu?
Muhsin ya amsa da yes shine.

“Dama wani taimako ne nake so kayi min saboda Kai din aka bani tabbacin zaka iya taimaka min. “Ok to Ina jinka…

Bello ya kwashe komai ya sanar da muhsin na son ya tsaya mishi Akan jinin yarshi Safiyya da wani Azzalumi mutum yayiwa fyade ya Kuma Kai karar shi Amma ya nuna mishi karfin kudi har aka Kori Shari ar shi Kuma yanzu Allah ya Rufa mishi Asiri Yana da kudin daukar lauya don ganin an kwato mishi yancin yarshi.

Muhsin ya dubeshi Yana fadin ya bashi kwana biyu zasuyi magana inda sukayi musayar lambar waya. Da haka Alh Bello ya wuce.


Washe gari kuwa muhsin na wurin aiki Amma hankalin shi baya tare dashi saboda tunanin Husna da Daddy yayi mishi tsaye a Rai. Ya Rasa a wane mizani zai aje wannan Abu da ya kasa yarda Husna ce da Rungumar Daddyn shi Kuma Yana Bata hot kiss Yana tsoron wani Abu fa. Ganin in ya tsaya wannan banzan tunanin zai wahalar da kanshi abinda kawai yafi ya Isa Abuja ya samu Husna yaji ta bakinta . Ya Mike Yana neman takardar da ya Rubuta lambar Mai kano wadda ya amso wurin Salma Amma takardar tayi batan dabo ya Soma bincike har a drowar Adana record na kotun inda ya Soma bude file file Yana duba tarin Shari un da aka gabatar har zuwa Kan wani tsohon file Wanda ya hango sunan Daddyn shi Radau ya jinjina sunan don Yana ganin ko akasi aka samu Amma dai ya Gane shi din dai ne don Haka ya jawo file din Yana Kara check din shi inda Kuma ya ga sunan wani Bello. Sai Kuma kwakwalwar shi ta tsaya cak Yana son hada uku da biyar su bashi takwas. Wace harkalla ce ta kawo Daddyn kotu? Wane Bellon ne Kuma? Wancan Bellon da Yake ikirarin wani yaci zarafin Yar shi ta hanyar fyade?

Ya aje file din Yana Jin yadda gaban shi ke sarawa wannan shine gaba kura baya siyaki ana Dara Kuma ga Dare yayi.

Ga dai tafiya gobe Agaban shi zuwa Legos don sanin halin da Husna take ciki ga kuma wani sabon lamarin ya tunkaro shi. Amma Kuma lamarin Husna gareshi babba ne Dole sai ya je ya San abinyi kafin ya dawo kan Alh Bello.

Agefen Husna kuwa abin ba a magana domin kuwa haukacewa ce batayi ba Akan yadda take Jin Alh Aminu a Ranta gashi haj Laila ta saka ido kwarai Akan ta bare fitar ta inda kuma takan karbi wayar zulaihat ta Kira Alh Aminu Amma kwana biyu Bata samun shi . Dole take hakuri Amma yadda takeji duk lokacin da ta samu fita Wallahi sai ta bar garin Legos ta iso katsina wurin Ruhin ta Daddyn ta
A kullum Mai Kano Yana gaban Halima inda aka ware musu bos kwata inda kuma Husna ke kula da ita amma fa Ranta na can wurin Daddyn.

Jikin Halima kuwa sai sauki take samu tana Shan Rubutun da ake RubuceMata Alkur ani Kuma ana sauke wa kafin ta gama ayi Mata Rukiyya

Ranar wata Asabar Mai Kano ya bugo hanya ya shigo garin katsina ya kuwa zarce gidan Alh Aminu tun a kofar gidan me gadin gidan ya tabbatar mishi baya Nan don Haka sai kawai ya zarce sardauna Estate wancan gidan nashi ya Kuma nasarar samun shi acan inda ya tambaye Mai gadin Wanda ya bashi damar shigowa Kai tsaye

Kamar daga sama Alh Aminu yaga shigowar Mai kano cikin dogon wandon jeans Wanda aka yayyanke gwiwar da gefen aljifan sai Rigar LV wadda ta matse jikin shi sai kuma hular face cap

A Rude Alh Aminu Yake kallon shi har ya zaune Yana fuskantar shi.

“Me ya kawoka gidana Mai Kano? Sai Kuma ya gaggabe da Dariya Yana Fadin “Kai yaro ne Zan Kuma nuna maka kuruciyar ka a fili kayi wauta da har ka tako zuwa gidan Nan Mai kano Kaine matsala ta a yanzu da Rayuwa ta don Haka a yau zaka Gane kana SHIGA hurumin da ba naka ba.

“A a Baba Aminu Kai ka ce Ina shiga hurumin ka Ni Kuma nace me saboda Allah? Rayuwar da kake kokarin yi cikin Ahalina koma nace kakeyi in ba cikin dabbobi ba a Ina akeyin ta? Uwa fa har da Diya kake son ka Aura? Kuma Ina me tabbatar maka Wallahi Kaine zaka Gane SHIGA hurumin da ba naka kake ba . Yanzu ma abinda ya kawo Ni tambayar ka kurum nazo yi don ka tabbatar min da shin duk Duniya Babu Mata ne sai Uwa ta da kanwa ta? Idan ma wahayi akayi maka dasu to ka koma kace a sake maka lakani Uwata Kuma Zan so daga yau muce kurun kus Kan Dan bera Akan ta shima Ina son sanin wace alakace da har ka saka aka sato maka ita ka kawota gidan ka ? Ko kasan anan gidan ka na samu mahaifiyata? Ko kasan anan gidan naka ta hadu da Bakin cikin da har mu ba zamu taba mantawa ba? Sila kawai nazo ka fada min in kuwa kace kana Nan a Jan wuyan ka to Zan nuna maka Jan wuyan katsina da na Legos akwai banbanci na San komai Akan ka da mahaifiya ta sai kuma Akan Husna da ban fidda tsammanin akwai wani Abu a boye ba.

Bai aune ba yaji saukar Mari a fuskar shi Alh Aminun ya wanke shi da Mari.

“Sharri zakaja min don ubanka? To Zan sa adaure minkai Akan wannan maganar Kuma Ina me tabbatar maka a wannan karon ba zaka tsallake ba in ma ka fita a gidan Nan kenan.

Ya fada Yana fizgo wayar shi da nufin Kiran su tsini in da mai Kano ke dafe da inda ya Sha Mari sai Kuma ya sauke hannun shi Yana zura shi cikin aljihu ya fito da wata zabira siririya ya bude ta ya nufi Alh Aminu dake kokarin Nemo lambar tsini ya nuna mishi askar Yana fadin.

“Ai ba zai yuwu ba nazo na barka babu tabon da zaka Rika kallo kana tuna Ni tunda har Al aurarka ta iya nufar mahaifiyata to ina me tabbatar Mata da taga nufar wasu Matan Wallahi don Zan canja Mata sabon yankan da Kai da wata mace sai dai ido.

Alh Aminu ya zaro ido kafin ya San abinyi Mai Kano ya kafa mishi sai kuwa ga jini Yana diga a a wandon Alh Aminu.

Mai kano ya yi murmushi Yana fadin
“Wannan shine Dan mabudin bude kofar fansar da Zan dauka Akan ka Zan tafi sai Kuma na dawo dama ai na Fadi nine ajalin ka Kuma sai nayi hakan ko da Zan Rasa tawa Rayuwar.

<< Hawaye 67Hawaye 71 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.