Skip to content
Part 77 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Fitar haj wasila Babu jimawa muhsin ya shigo Wanda ya Soma jiyo sautin muryar mahaifin shi Yana kakari da kwarara ihu.

Da sauri ya haura sama inda Yake jiyo muryar Daddyn Kuma ga mamakin shi Bai ji motsin kowa ba a gidan babu Amal babu Mami.

Ya shiga dakin inda ya samu Alh Aminu cikin wata muguwar Kama don gaba Daya halittar jikin shi ta juye ta jirkice yayin da fuskar shi tayi Baki harshen shi ya zazzago idon shi Kuma Yana fitar da jini.

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un din da Yake fada Yana maimaitawa itace tasa dakin ya Kuma amsa Rigugi da wasu iface iface Mara’s dadin sauraro cikin wasu muryoyi masu Kama da kukan jaki.

“Ka fice daga Nan Kar ka Kuma Kiran wannan abun da ka fada !

Aka umurci Muhsin da wata katuwar murya Amma baiyi kamar zai fasa fada ba Kuma baya Jin zai iya Barin mahaifin shi a wannan halin sai ma kokarin Isa gareshi yake da son ya taimake shi Amma kuma sai yaga Daddyn Yana dago mishi hannu Akan ya fita Kar ayi mishi illah yaje don shi kanshi baya son abinda zai taba lafiyar su shi da Amal ko ba komai shi dai yasan tashi ta Kare to ya mutu Yana sa Ran da zasu tuna dashi wata Rana suyi mishi ADDU A duk da zai mutu ya bar musu abin kunya Wanda zasuji haushin shi kuma ko basuyi mishi ADDU A ba to baya son a taba lafiyar su tunda Basu cancanci hukunci Akan abinda ya shuka ba Amma Ina muhsin baiji zai iya Barin mahaifin shi a Haka ba ai koma meye baifi karfin Allah da ADDU A ba don Haka da wata dakakkiyar zuciya irin ta maza ya tunkari Daddyn shi inda aka sake dako mishi tsawar Amma baiyi ko dar ba ya Isa inda Alh Aminu Yake Wanda har bakin shi ya Soma zubar da jini ya tallabo shi Amma sai nuni yake mishi da yaje Kar acutar dashi ya barshi kawai Amma sai Muhsin ya duka zai sungumo shi ya dauko ai kuwa yaji wata Aradu ta tarwatse asama kafin Rufin dakin ya Soma jijjiga sai kawai ga wuta tana tartsatsi ta Kuma nufo su gadan gadan da sauri muhsin ya Fara ambaton sunan Ubangiji da A uzubi bi kalimatullahi tamat min sharri mah khalak. Allahumma inni Auzu bika Min kulli shaidanin Rajim.

Ga mamakin shi sai wutar kwana ta koma inda ta fito Tana sakin wani sauti tushh tushh.

Ya sungumo Alh Aminu Yana ta Jan ADDU OIN da suka Zo bakin shi har ya fice da Daddyn daga dakin ya fice dashi gidan ma gaba Daya don ya gano aikin na miyagun aljanu ne.

Hajiya Kulu ta tarbi Halima har tana zubar da HAWAYE ta Soma sauke Mata tarin tambayoyi Mai Kano kuwa in Banda harara Babu abinda Yake aikawa haj yayin da Husna ta matsu da son ganin Yaya muhsin don Haka ta fice gidan kawu Amadu ta Ari wayar matar shi hajara tana dokawa Yaya muhsin Kira Amma ko da ya dauka yaji muryar Husna ce sai yayi maza ya kashe tayi ta Kira Amma yaki dauka karshe sai ta tura mishi text messages Amma shiru babu reply sai taji jikinta yayi sanyi.

Halima ta sanar da haj komai Akan Alh Aminu tun daga sawa a dauketa da Abun da yayi Mata na lalata Mata Rayuwa har zuwa bullar cikin da ya kusa zuwa Duniya Kuma ya zube ko aka tsafe.

Haj ta Dora hannu aka tamkar me Shirin fasa ihu har Halima ta Kare bayanin ta da karshen abinda ta sani na juyewar kwakwalwar ta Amma abinda ya shafi Rayuwar da tayi cikin tabin hankali wannan Mai Kano ne kurum ya sani Amma yadda yake Jin haushin hajiyar ko kallon ta baiyi ba bare ya Kare Mata labarin

Ta dubeshi tana fadin, “Yanzu Mai Kano duk kasan wannan Amma ka barni Ina bawa mugun mutumin can Amana da mishi kallon waliyyin Allah?

Ya harari hajiyar Yana fadin, “Kina kulafucin abin hannun shi Yana Baki kina kauda kanki daga gaskiya Zan fada Miki ki yarda? Kuma ai in Baki manta ba na fada Miki nine ajalin shi to ki Rike a yau din Nan Zan karar da Jin shi da ganin shi Wallahi zai koma zaman shi bashi da amfani a Duniya har sai ya Roki na karasa kashe shi da Bakin shi zai Roki na kashe shi !

“Tashi maza wallahi don Ni da kaina na Kuma Arba da munafukar fuskar shi Babu abinda zai Hana na kashe shi cewar hajiya.

“Ai bake Kika sani ba can da nayi in kin matsu sai ki iske shi ai dama karshen munafuki yaji kunya. Ya fada a fusace inda Halima ta dube shi tana fadin. “Kar ka sake fadawa hajiya wannan maganar Mai Kano ko da Bata tsuguna ta haifeni ba tayi min Ruko irin na uwa a matsayin ta na matar mahaifina.

Wani kololon bakin ciki ya tsaya mishi a wuya da yasan hajiya ba itace uwar mahaifiyar shi ba Yasin da tuni ya Dade da firdeta don abinda tayi ba dai Uwa mahaifiya ba sai yaji ya Kara tsanar ta don Haka ya fice daga gidan zuwa gidan su Salma wadda Bata boye murnar ta ba da ganin shi tayi ta tambayar shi Halima ya fada Mata anganta har ta warke ai kuwa tace suje ta ganota yace ta sanar da Adama wadda ya SHIGA don ya gaishe ta ya iske sai kuka take ga Auta kwance Agaban ta ga Alama Kuma Bata da lafiya ya tambaye Adama abinda takewa kuka Anna sai Ashar ta antako mishi Amma Kuma da ya Miko Mata kudi ta amsa tana fadin bata gode ba.

Sai akan hanya ne Salma ke fada mishi Adama yarta ce aka kawo Mata Wai ta kamu da cuta me karya garkuwar jiki yau Bala in da Adama ke jawowa ya sauka Akan yarta yayi Mata ADDU AR Allah ya Bata lafiya da Haka suka Isa gidan hajiya Halima taga Salma sosai ta ganeta ta Rungume Salma tana murmushi Salma tayi Mata fatan alkhairi inda Halima take kallon Mai kano tana Raya wani Abu a Ranta Akan shi shi da Salma .

Wuni sur salma tayi kafin dare Mai Kano ya maida ta gida ya dawo yacewa Halima gidan su zasu koma tunda yasa an gyara shi hajiya ta dubeshi tana bashi hakuri Amma yace ba zasu kwana ba Dole kuwa suka wuce inda Halima Bata boye Sha awar Salma da son ya dauko ta ba shima ya ya fada Maya dama ita ya fidda ai kuwa tuni magana ta Mika manya suka SHIGA Mai Kano kuwa yace in sun shirya wata Daya ma Yake so Kuma baya bukatar su wahalar da kansu Salma kawai Yake so.

Haka kuwa akayi Aure ya kullu a tsakanin su Salma ta tare a gidan shi na can Legos yayin da Alh Dan iro ya sanar da Mai Kano cewa shifa idan Halima zata yarda to zata maye mishi gurbin haj naja inda Mai Kano yace ya Amince Amma itama aji ta bakinta ai.

Haka suka iso garin katsina Halima taji bayanin Alhaji Dan Iro don Haka sai tace sai abinda Mai Kano yace in ya yarda itama ta yarda don shine Mai bada Auren ta ai kuwa ya ce shi ya Amince ko don halaccin da yayi musu tuni kuwa Aure ya dauru tsakanin Halima da Alh Dan iro wata daula da Bata taba mafarkin SHIGA ba sai gata a garin Legos Aure Mai Daraja ya kawo ta inda Kuma Husna tace zata zauna a wurin haj ba Kuma saboda komai ba sai don muhsin Wanda zuciya ke wa kulafuci sai Kuma taji zuciyar ta na fada Mata muhsin fa jinin Alh Aminu ne Wanda ya jefa mahaifiyar ta da Dan uwanta a cikin gararin da bai so suka fita ba sai taji ai muhsin ko shine autan maza ta barshi Bari Kuma na har abada don Haka tayi shiri tacewa hajiya Legos zataje ba don taso ba ta barta inda hajiyar ke nadamar abinda tayi don tana ganin kamar Halima da Ya’yan ta zasu juya baya gareta mussamman yanzu da Duniyar ke damawa dasu sai ta Fara kuka tana da ta sani Wanda ake cewa keya ce.

Amal ta samu labarin halin da mahaifin ta ke ciki ta hannu Yaya muhsin Wanda Bai boye Mata komai ba itama ta sanar dashi ta bar gidane tana kaduna wurin kanen Alh Aminu wato Alh Mustafa amma zatazo katsina sai suje Legos wurin me maganin da yayiwa Halima magani don taga ikon Allah wurin shi da Haka suka aje magana.

Washegari kuwa Amal ta bugi hanya ta iso katsina ta samu mahaifin ta cikin wani mugun Hali wanda yasa ta zubar HAWAYE Kai mahaifi mahaifi ne ba Kuma a sauya su Sai dai a nema musu gafara yayin da haj wasila tace shi ya siya don Haka ita tsakanin su sai dai tayi musu ADDU’A.

Washegari Muhsin da Amal sukayiwa Legos tsinke inda akayi wata haduwa Muhsin da Husna Amal da Mai Kano Amma abin mamaki muhsin da Husna tamkar sunga wasu makiya Abokan gaba yayin da Muhsin ke kallon Husna taci Amanar shi tunda Daddyn shi ya sameta ya gama dashi ita Kuma tana kallon shi a wani gagarumin makiyin ta da ya fito daga tsatson wanda ya keta Alfarmar uwar ta sai suka daukewa juna Kai kowa Yana Jin wani daci da makaki a zuciya.

<< Hawaye 76Hawaye 78 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.