Skip to content
Part 8 of 32 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Wata uku cur! Da tafiyar Mai Kano har yanzu Bai juyo ba Amma tana kyautata mishi zato tare da yi mishi Adduar fatan Alheri.

Tana zubawa Husna da Sulaiman abinci a launch boxe ta jiyo kugin motar Alhaji Aminu inda Sulaiman ke fadin “Ga baba Aminu nan Mama….

Ai kuwa kafin Sulaiman din ya gama rufe baki sai gashi ya shigo. Husna da Sulaiman suka je da gudu suka rungume shi suna mishi oyoyo . Ya cabe su Yana dagawa sama har yana sumbutar su tare da shafa kawunan su

Halima ta kawo mishi kujera ya zauna suna gaisawa inda Husna da Sulaiman suka dauki abincin su suka yi nufin wucewa makaranta. Halima ta kawo naira hamsin hamsin ta Basu . Ya Mike Yana fadin

“Ba dai kasa suke zuwa makaranta ba? Ya fada Yana kallon Halima. “Kasa suke zuwa ai Babu nisa fa…”

“Bari na Mika su na dawo. Ya fita yana rike da hannun yaran. Ya bar Halima da jin wani abu marar dadi don ta hango wani abu a cikin kallon da yayi Mata a yau.

Bai Jima ba ya dawo yana tambayar halin da yaran ke ciki. Ta fada mishi duk suna lafiya sai dai bata sanar dashi Mai Kano ya tafi Legos ba. Da Haka ya kawo kudi masu dama ya bata kafin yayi Mata sallama ya wuce da wani bakon abu da babu shi a ranshi tun fil azal. Amma ganin da ya yiwa Halima a yau ya darsa mishi wani abu da bai shirya mishi ba tun farkon rayuwar shi. Wasila ita kadai ya shiryawa Aure ita da zama ita kadai amma a yau Halima ta bude zuciyar shi ta shiga ba tare da sallama ba . Kuma tayi nasarar budewa da rufewa. Sai dai wata zuciyar na tambayar anya ko abin nan me yuwa ne? Ya bawa zuciyar amsa tamkar yana ganinta

“Yo ni yanzu me ye abinda ma ba zai yuwu a gareni ba? Wanda bai yuwa ma sai na maida shi me yuwa.

Bai zaci abin na gaske bane sai da ya kwanta bacci mafarkan shi kaf sun kare ga Halimar har ya kare da kiraye kirayen sunanta akan kunnen Hajiya Wasila.

Ta farka saboda jin kiran Halima da yake. Ta zuba mishi ido cikin tafasar zuciya tamkar tayi ta gaura mishi mari baccin da ta kasa komawa har gari ya waye

Tsayin watanni uku Yana fama da Abu daya wato wahalar son Halima har yayi rama don da gaske yanzu ne yake yin so bai ma taba sanin so na da zafi ba sai akan Halima.

Yayin da ganinta ne kurum ke sanyaya zuciyar shi don haka sai ya lazimci ziyarar ta Kai da kai

Watan Azumi ya tsaya inda ya jibga siyayya tun daga kayan abinci ya kai mata da kuma amayar mata da abinda ke damuwar shi akan sonta

Ya Isa gidan bayan ya dire mata kayan tayi godiya ya kuma dora Mata kudi ko zata siyi saura kayan masurufin saboda tsayuwar watan Ramadan tayi godiya ya zuba mata ido har ta tsargu ta kuma yi fatan ya wuce ya barta da wannan nataccen kallon da Yake binta dashi Wanda Bata fatan ya furta komai bare yace wani Abu akanta don tuni ta gama gano inda ya Dosa. Kai maza ma sai abar su wurin su. Basu Faye duba abinda zaije ya dawo ba in dai ta raya musu musamman akan Sha’anin mace to yanzu ne zasu maida baki ya koma fari

Ba komai take tsoro ba face Amincin ta da haj wasila Wanda ko ita aka yiwa haka ba zata so ba bare Hajiya Wasila da ta gama sanin wacece ita a bangaren kishi.

Ya katse Mata zaren tunani ta hanyar kiran sunanta. Ta dago ba tare da ta amsa ba.

“Halima Ina so muyi magana Mai muhimmanci Ina fatan Zaki fahimce Ni? Ya fada ya na kafe ta da ido

Gabanta yayi masifar faduwa, “To Allah yasa dai lafiya?

“Lafiya lau sai ALHERI. Yayi Jim kafin ya ce, “Ba Zan boye Miki ba Halima Allah ya jarabeni da kaunar ki wadda har nakejin mamakina akan hakan, “Sai Kuma Naga idan har hakan ta tabbata ai kamar ma nine yafi kowa cancantar hakan ko don na kula da Ya’yan mu azu Amma Dole amincewar ki nake nema idan har hakan yayi Miki.

“Dama nasan hakan”. Ta fada aranta. Tayi shiru ta kasa tsinkawa har ya gaji da shirunta ya tanka

“Ba ki ce komai ba Halima. Ta sauke ajiyar zuciya

“To ka yafe Ni Alhaji Aminu, abinda kazo dashi gaskiya ba me yuwa bane don ba zan boye maka ba kafi kowa sanin Ni da wasila mun san sirrin juna kaga kuwa Auren ka zai zamo tamkar cin Amana gareni gareta Kuma. Don Allah mu bar maganar nan, kuma a tsakanin mu. Yayi murmushi Yana Kare Mata kallo

“Halima kenan ku dai mata in dai lamari ya hado Aure ne to yanzu ne zaku maida halal ta koma Haram. Ni Ina ganin Auren mijin kawa ai Kara dankon kawance ne idan da kunyi nisa kun kusanci juna ku kashe ku Rufe babu Mai ji. Kuma fa Ni ba wuri Daya nake kokarin hada ku ba kowace da mazaunin ta bare Kuma ace wani Abu. Kuma Ni nayi zaton irin facakar da Wasila ke yi acikin ku tana homa da barazana tana yakar ku tana burgeki shin ke Baki fatan kasancewa kamar ita?

Wannan maganar tayi masifar Kona Mata Rai. Yana zaton ita kyalkyali na rudar ta? Amma sai bata nuna mishi ba

“Wallahi baya rudani Aminu, a duk yadda na tsinci rayuwa zan karbeta a duk yadda aka miko min zan Mika hannu na karba na kuma gode don haka wallahi duk abinda Wasila keyi ban taba hango kaina ba a matsayin ta. Don Haka muyi hakan dai kawai don Allah mu bar maganar Nan anan mu rufeta anan ba zanso wani can yajita ba bare Hajiya Wasila.

Na kula dai Halima tsoron Wasila ne zai sa ki haramta min abinda Yake halal to nine nake Auren Wasila ba Wasila ce ke Aure na ba don haka indai Wasila ce matsalar to Wallahi Zan sauwake Mata Aure na idan ta fita ai babu wani shamaki ko? Ya Mike Yana Shirin ficewa.

“Zan baku lokaci ki yi shawara zan ga yadda kika dauki Amincin ku da Wasila, shin kin zaba mata zaman aure ko zawarci kika zaba mata? Tunda kunce ciwon ya mace na mace ne. Zan dawo inji shawarar da kika yanke.

<< Hawaye 7Hawaye 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×