Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Hukuncin Allah by Umar bin Ally

A wani lokaci da ya gabata an yi wani matashi maisuna salim salim ya kasance yanada wata mummunar akida wanda shi yake ganin duk abinda yasamu mutum tofa kawai sakacinsa ne yajawo masa koda rashin lafiya mutum yayi saikaji yace aida aceyi yayi abu kaza da baiyi ba anyi anyi dashi akan yagane cewa idan Allah ya nufi abu yafaru tofa ba makawa sai ya faru amma sam yaki ya yarda mahaifiyarsa tarasu a hatsarin mota suna tafiya da ita da yayansa mota ta bugeta tamutu wanda tundaga nan ya daina kula yayan nasa acewarsa rashin kulawarsa ne yajowo mutuwar mahaifiyarsu har yana ikirarin cewa da yana gurin nayanzu mahaifiyarsu tana raye suna zaune da mahifinsu Allah ya jarabceshi da iftilai na gobara ashago kayan ciki suka kone da duk dukiyarsa dan ya kasance yana ajiyar kudadensa ne acikin shagon wannan dalilin yasa salim anan ma ya kullaci mahaifinsa yake cewa da ace agida yake ajiye kudi aida yanzu kudin basu kone ba

Cikin ikon Allah watarana salim ya kwanta bacci kawai yana tashi ya gan shi aranar da mahaifiyarsu zata rasu komai abinda ya faru a wancan ranar shine yake faruwa awannan ranar banbancin kawai da aka samu shine alokacinda tazo fita maimakon su fita da yayansa sai yaga shi takira tace yazo sutafi tare sunfita suna tafiya har sukazo gurinda mota ta bugeta sai yace da ita mukoma ta wancan bangaren tanuna A,a amma ya nace saida suka koma aikuwa suna komawa ta daya bangaren saiga wannan mota da ta bugeta tataho ta bangaren da suka baro da alama ta kwace ne a hannun matukin motar ta tafi da gudu akan titi tayi kan wata motar zasuyi karo sai wancan matukin ya kauce masa aikuwa yana kauce masa sai shima tashi motar ta kwace yakasa riketa basu ankaraba saiji sukayi matar nan tazo tabi takansu shidai salim kawai farkawa yayi yaganshi a asibiti ya tambaya ina mahaifiyarsa akace motarnan ta takeya akai Allah yayi mata rasuwa cikin razana yayi yunkurin tashi bisa da mamaki saiyaji yakasa yaji kamar ba jikinsa ba yana yaye mayafinda aka rifeshi dashi sai yaga kafafuwansa ayanke akace masa sanadiyar hadarinnan anyi nasarar ceto rayuwarka amma kuma motar tabi takan kafafuwanka dole aka yanke su nantake hankalinsa ya tashi ya fara wani irin matsanancin kuka sai ji yayi kawai ya yanke jiki ya suma .

Yana farkawa kuwa sai ganinsa yayi andawo dashi ranarda shagon mahaifinsu yake konewa tunda safe yatashi yadauki makullan shagon yaje yabude ya kwaso duk kudaden da suke ciki yazo gida ya ajiye yadebo kayayyaki masu muhimmanci duk yakawosu gida yana jira mahaifinsa yana masa magana shikuwa cewa yake kabari tukunnan baba zaka godemin nan da kankanin lokaci ashe abinda baisaniba shine dakinda yake ajiye kayan an ajiye turaren wuta akunne shikuma saboda tsabar sauri ko dubawa baiyiba haka yaringa jibga kaya akai aikuwa bayan wani dan lokaci wutar nan takama kayan basu ankara ba gidan gabadaya yakama da wuta kafin akawo musu dauki tuni gidan yakone daduk abinda ke cikinsa sai farkawa yayi yaganshi a asibiti gaba daya jikinsa akone mahaifinsa da dan uwansa duk sun kone sun mutu sani irin kuka yakamayi mai ban tausayi sai ji yayi kamar an dakeshi akai ya suma

Said bani yayi yasake farkawa a ranarda mahaifiyarsu ta rasu aranar gaba daya tashi yayi jikinsa ba karfi yaga duk abinda yafaru aranar yanata faruwa da mutum zai fadi wani abu kafin yafada sai shi yarigashi fada sukaita mamakin ya akai yasan abinda zasu fada aranar yayi iya bakin kokarinsa ya hana mahaifiyarsu fita suka zauna agida aikuwa bisa mamaki dai dai lokacin da ta rasu yana zuwa sai sukajiyo hayaniya daga waje ashe wani me babbar mota ne motar ta kwace baizame ko ina ba saida yazo katangar gaban gidansu adaidai lokacin aukuma sunfito atare shi da mahaifiyar tasu da dan uwansa suna fitowa motor tana dukan gidan nan take yahada dasu da ginin yabi takansu babu wanda ya shura suka fadi matattu.

Ya farka adimauce abisa mamaki sai yasake ganinsa aranar da shagon mahaifinsu yake konewa yana ganin haka ya fadi kasa yana tuba ga Allah yana cewa Allah duk hukuncinda ka yanke shine mafi daidai bawanda yafika sani babu kuma wani mai dabara babu masanin daidai sai kai Allah natuba Allah kadawo min da rayuwar da katsaramin itamce mafi dacewa dani Allah natuba Allah natuba

Sai ji yayi ana kiran sunansa ana jijjigashi yafarka a dimauce sai yaga yayansa yana cemasa lafiya kuwa kana bacci kana kuka nan take yakwashe labarin abinda yafaru ya fada masa yakuma nemi gafarar sa abisa zarginsa da sakaci wajen rasuwar mahaifiyarsu sannan yaje ya nemi gafarar mahaifinsa yakuma ajiye mummunar akidar nan tasa ya fauwala lamarinsa ga Allah.

Karshe

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

2 thoughts on “Hukuncin Allah”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.