Skip to content
Part 10 of 15 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

Washegari Innai ta tashi da mugun zazzaɓi ga ciwon ciki, hankalin Baabaa Mero in yayi dubu to ya tashi.

Hana ta zuwa makaranta tayi tunda bata da lafiya ta huta, amma Innai ta tirje sai taje dan suna da test.

Sai da Magaji yazo da kansa kaman zai mata duka tukunna ta haqura da maganan zuwa makarantan amma idanuwanta har da qwalla tana tunanin test na yau da zasu yi.

Baabaa ta kalleta tace “ja’irar yarinya shawaragiya wai ace baka da lafiya ka huta zuwa boko hakanan ka sanya mutane a gaba kana sheshsheqa da gulmammen kuka dan staɓar tijara, kai kace uwarku da ubanku ake raba muku a makarantar, Aradu takwara kika yi wasa daga yau kinbar zuwa makarantar sai na aurar dake in yaso kije can mijin yayi haquri ya raineki kiyi nunu a gidan sa” .

Tura baki Innai tayi tace “nikam tunda an hanani zuwa makarantar a bar damu na da magana”.

Buɗe baki baabaa tayi ta jero salati tace “eh tabbas ya tabbata bayan yaren ‘yan wuta har da halayyar ‘yan wuta ake koya muku yanzu wai du yaushe kika fara zuwa makarantar? Inaji baki cika wata biyu ba amma har kin koyo fistara yarinya shiru-shiru sanyi-sanyi ba ruwanki kaman kazar da aka sanya a ruwan sanyi amma yau ni kike cewa na dameki da magana to takwara kinyi da uwaki Indo, shashashar yarinya kawai ai inba tambaɗanci ba da rashin kunya baki gayamun magana, to Allah kawo ubanki daga yau an daina karatun da zuwa makarantar tunda rasar kunya ake koyowa a can”.

Innai fashewa tayi da kuka ta tashi tana riqe ciki ta shige cikin ɗakin Baabaa Mero, binta da harara tayi tace “ja’ira ‘yar kutun-kutun dubi yacce take tafiya kaman stohon da yasha sanda a baya amma wai ki dage zaki makaranta”.

Fitowa tayi a ɗakin tana share hawaye ko qala bata cewa Baabaa Mero ba ta fice a gidan, da kallo Baabaa ta bita ta tafa hannu tace “kai amma in akace yaro da kare basu da banbanci to haqqun anyi gaskiya, yanzu sabida Allah dan rashin sanin ciwon kai yarinya ta kwashi figaggun qafanta kaman wanda aka stoma kaza a ruwan sanyi tace zata je wancan gidan dan kawai anfaɗa mata gaskiya to Inshà Allahu ni Meramu ba ni binki kuma ba ni qara shiga tsabgarki da ta uwarki kayan kunyan ya ishe ni kuje ku fama in suka barki kika mutu su binneki ko gawan kar a gwada mun ‘yar ƙwal uba Allah baki lafiya, kuma makarantar ne nace ba zaki je ba babu zuwa sai Aure”.

Da sallama ta shiga gidan tana riqe da cikin ta, tafiya take tana layi kaman zata faɗi idonta na hawaye tayi hanyan ɗakin su, Inna na zaune qofan ɗakinta tana gyaran shinkafa tunda ta ɗaga kai sau ɗaya ta kalli Innai sai ta kau da kai ta cigaba da aikin ta, Innai na tafiya a duqe tayi tuntuɓe tana qoqarin faɗuwa Baffai da fitowansa bayi kenan da Mama Lami da itama fitowan ta ɗaki kenan kusan rige-rigen tare Innai suka yi lokaci guda Baffai na cewa “subhanallahi Uwata jikin ne har yanzu?” hutar da mama Lami Baffai yayi ya ɗaga Innai caɗak ya kaita ɗakin mama lami ya kwantar sannan ya fito, kallo ɗaya yawa Inna ganin ko mostawa ba tayi ba ya kau da kai ya juya yana ayyana irin hukuncin da zai ɗauka wannan karon, zai fita a gidan sai ga Magaji, ganin Baffai sai yace “Baffai za ka fita ne?.

Baffai yace “eh baban Baffai zan sayowa qanwarka magani ne zazzaɓi na damunta” kallon Baffai Magaji yayi yace “dama Hassu ba taje makaranta ba? Girgiza kai Baffai yayi yace “ba Hassu ba Innai ce”.

Da mamaki Magaji yace “Innai de da yanzu na barta gidan baabaa? “Eh ita dai yanzu shigowanta”.

Karɓan kuɗin maganin yayi ya juya sayo wa shi kuma Baffai ya koma cikin gidan.

Ɗakin mama Lami ya ɗage labule ya shige ya zauna gefen Innai yana jera mata sannu.

Magaji yaje ya sayo magani ya kawo Baffai yayi-yayi da ita tasha maganin amma sai taɓara take taqi amsa, da Magaji yasa baki sai ta fashe da kuka. ganin haka sai mama Lami ta bawa Baffai haquri akan ya bari sai anyi abincin rana taci sai ta sha, Baffai ba dan yaso ba ya qyale ta.

*****

Afrah tunda ta shigo makaranta take zuba ido ta inda zata ga ɓullowan habibtynta dukda dai sun rabu tana fushi da habibtyn nata amma ta mastu ta kalleta dan bata jin zata iya fushi da ita.

Wasa-wasa har aka yi assembly aka gama aka shiga class malam ba wasa ya shigo ya gama ya fita shima sai leqawa yake amma bai ga idon mutumiyar sa ba, Afrah tun tana ɗaukan abun wasa har taga da gaske ne dan gashi har an fita break an dawo an kuma fita sallahn azahar, nan dai duk gaba ɗaya yanayinta ya sauya sai take jin kaman ta dinga ihu rashin ganin Innai, Allah ya taimake ta ba’a musu test ɗin ba dan da kuwa bata san me zata rubuta ba balle ma tayi tunanin yiwa Innai.

Har aka tashe su aka zo ɗaukan ta amma ta roqi drivern ya jiraata, zaman dube-dube tayi sune basu baro makarantar ba sai da ɗaliban day gaba ɗaya suka waste na hostel ma suka shige hostel kamun tawa drivern magana su tafi idanuwanta cike da qwalla qiris take jira tayi kuka gashi gobe Saturday ba makaranta har sai Wednesday dan ranan Monday da Tuesday hutun Esther.

Driver na parking ta sauqa ko jakan makarantar bata ɗauka ba ta tura baki ta shige cikin gidan, hanyan ɗakinta tayi ko kallon palourn bata yi ba balle tasan ko akwai mutane ko babu.

Kaman daga sama ta jiyo muryan yayanta yana cewa “Afrah ba magana ne? Juyowa tayi sai kawai hawayen da take riqewa suka gangaro suna bin kuncinta ta wuce wajan yayan nata ta shige jikinsa.

Afreen ce ta taɓe baki tace “ke dai kinga ta kanki kuma in haka ake Auta to baki more ba duk anbi an sakalta ki kalli abinda kike yi fa kayan amai”.

Kamun Jay ya buɗe baki Hajja ta riga sa tace “ke maimuna banson rashin mutunci fa daga zuwa zaki addabi baiwar Allah, wai ubanwa yace kizo ne ma, kai kuma jabiru baka san hanya bane ka ɗauko wannan fitsaratun?

Jay bai kalli Hajja ba balle Afreen hankalinsa na kan damuwan da suke ciki yace “Auta me ya same ki? Cikin kuka tace masa “BB (big brother) ba Habibty na ce taqi zuwa makaranta yau ba” da mamaki yake kallon ta yace “wacce habibtyn? dan nasan mummy dai tana gida”.

Tura baki tayi tace “qawata ce mai sunan mummy shine nake ce mata haka, jiya da zamu rabu mun ɓata yau kuma ban ganta a makarantan ba kuma ina kewanta”.

Afreen cikin taqaici tace “amma Allah wadaran naka ya lalace aka bincika ma wata ‘yar talakawa ce har da zubar da hawayenki a kanta dan ganin arahan gabas karuwa da sallahn walha”.

Hajja ma guntun tsaki taja tace “fatu ke dai kin cika abin taqaici kaman mutum yayi kashi” Jay kuwa murmushi yayi cikin sigan rarrashi yace “to tashi kije ki shirya kici abinci na kaiki gidan su ki dubo ta ko”.

Tura baki Afrah tayi tace “nifa BB sunan ta kawai na sani bansan gidansu ba kuma kaman ba’a cikin Ashaka take ba amma dai ban sani ba, Allah BB sai ka ganta ga kyau ga hankali itama takawarar kakarta ce kaman ni kuma itama a gaban kakarta take zaune, BB Allah nikam ka aure ta ai sai ka ganta kaman ni take amma ta fini kyau dai sai bata da um’um” cikin jin kunyan abinda takeson cewa ɗin tace “kawo kunnenka na gaya maka” kunnensa ya kawo ta faɗa masa maganan tana miqewa tayi ɗakinta da gudu.

Murmushi Jay yayi yace “wannan yarinya kin girma soon kema zamu nemo miji mu aura miki”.

Hajja tace “fatu faɗi ba’a tambayeki ba, shikkenan har ta gama rigiman ta gudu saura kuma na anjuma in ta fito”.

Afreen ta jawo wayanta tana lastawa tace “anjuma kuma ke da ita dan mukam mun jima a Gombe”.

Jay kallonta yayi yana murmushin mugunta a ransa cewa yake “ina Gombe ba muna Gombe ba dan barinki anan zan yi”.

Nan Hajja ke tambayan sa batun mastalan da ake ciki.

Numfasawa yayi yace “Hajja har yanzu dai shiru ba wani labari cikiya ba irin wanda bamu bada ba har DMD ya bada kyauta akan wanda ya ganta amma shiru”.

Qwafa Hajja tayi tace “wancan fitinannen yaro da ya gagari kowa, ina ma yake da baku zo tare ba?

“Mun taho yana bacci Hajja”.

“Ya masa kyau ya fama da baqin halin sa, ita kuma uwar su Allah bayyana ta”

Da “Ameen Jay ya amsa”

Afreen ta tashi ta shige ciki tana “cewa bari na huta kamun lokacin komawa”.

Harara Hajja ta bita da shi tana cewa “sai inga gidan uban da zaki koma muna nan dake ja’ira”.

Jay yayi murmushi yace “Hajja ba na dawo zanje wajan wani freind na”.

“To a dawo lafiya ɗan albarka” faɗin Hajja tana murmushi

DMD Miqewa yayi yace “Whatttttt!?

“Eh uwarku bata iso ba kuma na qira layinta baya shiga maza-maza ka nemeta ka faɗa mata inma a ina ta staya ko me take yi ina buqatan ganinta a gida yanzun nan” kitt Abiy ya kashe qiran yana gama magana.

Layin Amminsa ya ke qira both na Nigeria da na Canada amma duka abu ɗaya ake faɗa masa “switch-off” huzar da iskan bakinsa yayi yana cewa “shittt! Na rasa me Ammi ke ɗaukowa a Nigerian nan har na tsani qasar kullum cikin matsaloli” zama yayi ya ɗau wayansa yayi dialing wani number ana ɗauka aka ce “hello Sir” cikin magansn sa mai kama da rigiman yace “Mark zan turo maka layuka yanzu ka bincika mun su” yana gama magana ya kashe qiran ya tura masa, can sai numbern ya qira sa ya ɗauka yace “Yes ina jinka”, “am sorry Sir amma a binciken mu layin na kashe kuma ba yanda za’a yi mu bincika sai dai a samu qwararru a Nigerian su bincika da kansu, sannan layin Canada kuma anjima da sauqe shi” mutumin da ya qira ya faɗa, ba tare da yayi magana ba ya kashe wayan qittt.

Main palourn ya sauqo ya tarar da sweedy na zaune riqe da waya a hannunta, kallonta yayi yace “ya aka yi” tashuwa tayi ta dawo gefensa ta zauna kaman za tayi kuka tace “Darling ina ta qiran layin Ammi baya shiga kuma fa tun da rana da muka yi waya bamu qara yi ba yanzu ga can sweetie sai kuka take wai za tayi waya da Ammi yanzu haka na barta da sweerie tana rarrashinta ne na fito na yi knocking qofanka baka ji ba” duk maganan da take cikin harshen turanci take yi sannan izuwa yanzu hawaye ya fara wanke fatan kumatun ta dake yalqi kaman na jarirai.

Ɓoye damuwan da yake ciki yayi ta hanyar cewa “karku damu Ammi na lafiya nafi tunanin wayanta ne ba chaji so ki turomun sweetie ke da sweerie kuma ku kula sosai sannan in Allah ya kaimu gobe zan tafi Nigeria karki faɗa musu ke dai ki kula da kanki da su sosai”.

Kallonsa tayi tana hawaye tace “Darling Nigeria dai? Kai da kace ba zaka qara komawa Nigeria ba sannan yanzu kace zaka je kuma kace mun lafiya, please inda wani abun ka faɗamun zanfi samun nistuwa dan na qira Abiy yaqi ɗauka” murmushi yayi ya shafa kanta yana share mata hawayen yace “da akwai wani abu zan faɗa miki ki yarda da yayanki ko, ki kula da kanki da qannenki kaman yanda nace in naje kuma zan haɗaku da Ammi yanzu je ki rarrashi sweetie in na dawo zanzo na ɗauke ta”.

Ba dan taso ba ta haura sama sashin su taje ta samu sweetie tayi bacci idanuwanta duk bushashshen hawaye, sweerie kuma tana zaune gefenta tayi tagumi, kallon su da tayi ya sanya jikinta ya qara mutuwa nan dai ta daure tayi yanda yayansu yace mata ta nunawa sweerie komai lafiya wayan Ammi ba chaji ne kawai sannan itama ta zauna gefen su dan yau basa jin kowa zai iya kwana shi ɗaya a ɗakin sa.

Ɓangaren DMD yana ganin haurawan qanwan sa sama ya sauqe ajiyan zuciya yana fita driver yazo da mota ya buɗe masa ya shiga yaja motan suka fice a gidan, a taqaice kawai yace ma drivern “airport”.

Suna zuwa airport suka samu ba jirgi mai tafiya Nigerian sai gobe, yaso biyan kuɗin jirgin gaba ɗaya a tafi da shi yau amma sai ya fasa tuna sweetie dan in ba shi ya rarrasheta ba baza taji rarràshin sweedy ko sweerie ba. Juyawa suka yi suka koma gida lokacin ma dare yayi amma abinka da qasar turawa kuma babban qasa ko ina kaman rana ga jama’a ga haske.

Sama ya haura ya shiga ɓangaren su, ɗakin sweetie ya nufa dan yasan ba zasu wuce can ba, yana murɗa handle ɗin sweedy ta zuba mishi ido, sweetie tayi bacci kanta na cinyan sweerie ita kuma sweerie kanta na kan cinyan sweedy, duk sai yaji sun basa tausayi rana guda kawai na rashin jin Ammi har sun rame.

Qarasa shigowa yayi ya qara kwantar wa da qanwar tasa hankali, sannan ya ɗauki sweerie ya kaita ɗakin sweedy yace suje su kwana a can shi kuma ya ɗauki sweetie ya fito ya nufi ɓangaren sa da ita.

Har bedroom ya kaita ya kwantar da ita akan faffaɗan gadon sa, shi kuma yaje ya ɗauro alwala yayi sallahn isha’i da bai samu yayi ba ya kuma yi shafa’i da wutiri sannan yayi addu’oen sa ya kwanta gefen qanwar tasa yayi addu’a ya shafa mata shima ya shafa.

Sama-sama yake ji ana bubbuga shi ana sheshsheqan kuka, idanuwansa ya buɗe ya kalli sweetie na tukuikuya shi, tashuwa yayi ya zauna ya riqo ta yana tambayan ta menene? Cikin sheshsheqan kuka tace “Darling Ammi na nayi mafarkin bata da lafiya kuma banji muryanta ba tun jiya ka qiramun ita” shafa kanta yayi alaman rarràshi ya miqa hannunsa ya ɗauko wayan sa ganin har 3 na dare yayi sai yace “sweetie ki bari sai gobe da safe kinga yanzu dare yayi kuma kinsan wannan lokaci Ammi na bacci kar mu tashe ta” da qyar ya samu ta haqura har bacci ya ɗauke ta, tashuwa yayi ya ɗauro alwala yayi nafilfilu da addu’oe sannan ya sha dai-dai ana qiran sallan asuba, jan carbi ya dinga yi har aka shiga ya tashi yabi masallaci.

Yana idar da komai a gaggauce ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin qananun kayan da suka karɓe sa sosai, ganin sweetie bata farka ba sai ya barta a ɗakin ya fice yaja mata qofa.

Yana shiga mota driver yaja sai international airport Canada.

Suna isa komai ready, driver ya ajiye sa ya juya shi kuma cikin mintuna biyar jirgin su ya tashi sai Nigerian.

Jirginsu na sauqa ya qira jay “Hello jay ina airport ka turo mun mota” qitt ya kashe wayan.

Bai kai minti talatin ba sai Jay da kansa yazo ya ɗauke sa, da mamaki ya kalle sa yace “jiya kawai muka yi waya ba zaka zo ba yau kuma sai gaka akwai wani abun da ya faru ne?

Lumshe ido yayi dan yama rasa ta yaya zai fara sai kawai yace “Jay bansan me ke faruwa ba amma dai Ammi tun jiya bata je gida ba” da mamaki Jay ya kallesa yace “shine har ka shigo Nigeria akan hakan me yasa ba zaka qira layinta ba ko ka qirani naje na ɗauko ta?

Cike da gundura da magana dan kansa har ya fara ciwo yace “Jay ka fahimta mana an qira layinta both baya shiga kuma nasa ayi tracking tun acan amma ba wani labari ga su sweedy duk sun ɗaga hankali qarshe ma jiya sweetie a ɗaki na ta kwana dan rigima wallahi har sun rame jiya kawai basu ji muryam Ammi ba”.

Jay kansa ya ɗaure ga tausayin su sweetie dan yasan irin sanya ta a jiki da Ammi tayi, cikin ɗaurewan kai yace “to yanzu ina muka nufa?

DMD yace “wai Jigawa fa jirginta ya sauqa tabi Companyna na can duba yanayin ayyukan sannan ta ɗau mota wai za tayi driving da kanta har Gombe nace mata a’a amma Ammi taqi ji”.

“Yanzu ita ɗaya ce ko tare da driver? Cewar Jay…

<< Jahilci Ko Al’ada 9Jahilci Ko Al’ada 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×