Skip to content
Part 11 of 15 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

DMD cikin yanayin damuwa yace “Jay yanzu dai bansani ba sai dai mu tambayi Managern Companyn”.

Laluɓo wayansa yayi ya fito da shi ganin wayan dake hannun sa sai ya lumshe ido, kaman zai yi kuka ya ce “shitttttttttt! Jay ba wayana mai layukan Nigeria na taho da shi ba”.

Kallonsa yayi yace “to ya za muyi? Dai-dai sun iso qofan gidan Abiy dake cikin GRA kusa da gidan governor.

Jay zai yi horn DMD ya dakatar da shi yace “ina zaka kai ni?

Kallon sa Jay yayi mai nuni da banson tambayan renin wayo sai yace masa “in kawo ka gidan ku kace ina zan kai ka kaga banson irin tambayan nan”.

Qaramin tsaki yaja yace “to daman wa ya gaya maka nazo gidan mu ne? Nazo neman Ammi na ne kawai kuma kasan bana shiga gidan nan in bata ciki so ko ka juya mu tafi ko kuma ka sauqa ka bani mota nayi gaban kaina”.

Dariya Jay yayi yace “in sauqa in baka mota ni kuma na ɓace kenan na koma gida? Hararansa DMD yayi yace “yauwa na tuna layin nasa na kan ɗayan Gmail account na bari nayi loggin.

Jay jan motan yayi suka tafi gidan su dake Tunfure, suna isa ya kammala komai ya qira Managern ya ɗauka suka yi magana.

Cikin palourn suka shiga tare da sallama a bakin su duka, Jay yayi sama ɗakin sa yace bari ya sauya kaya yazo su fita, shi kuma ya wuce ɗakin mummy.

Sallama yayi a qofan ɗakin, mummy ta amsa masa tace “shigo”. sai ya murɗa handle ɗin ya shiga.

Waro ido tayi cikin mamaki tace “yaron Ammi kai ne da sassafen nan? Iso ka zauna” zama yayi a bakin gadon mummy sannan ya gaisheta nan yake faɗa mata abinda ke faruwa cikin tashin hankali ta kalle sa tace “yanzu maimakon ku wuce jigawan ko wajan ‘yan sanda shine ka biyewa jabeer, ba’a tafiya da jallabiya ne? Ko kuwa a qafa zaku tafi ba mota ba? Qasa yayi da kansa dai-dai Jay ya shigo ɗakin da sallama.

Shima gaishe da mummy yayi ta amsa tana cewa “jabeer baka da hankali ashe? Sanja kayan me zaka yi zance za kaje ko neman uwarka? Shafa kai Jay yayi yace “afuwan habibty yanzu zamu tafi, tashi mu wuce DMD”.

Miqewa DMD yayi yace “habibty sai mun dawo” mummy tace “Allah bada sa’a ku dawo lafiya ubangiji Allah yasa lafiya ne ya riqe ta Allah sa komai yazo da sauqi kuyi sauri maza zan faɗawa Daddyn ku”.

Ficewa suka yi suka ɗau wani motan DMD yace shi zai yi driving jay in yana driving kaman mai storon hanya.

DMD ya ja su sauka ɗau hanyan barin Gombe, sun bar cikin Gombe sun isa Kwami local government har suka fita.

Sun fita a kwami ba jimawa Jay yace “dude tsaya na rage mara” ba tare da yace komai ba ya ci-gaba da driving.

Jay ganin zai jaza masa aiki sai ya danna birki, kaman za su gangara wani rami haka motan ya tsaya DMD yaja guntun tsaki yace “malam yi sauri bamu da enough time yau nake so mu dawo” Jay na sauqa ya gangara zai yi fistari sai yaga wani mota kaman wanda aka yi hastari kaman kuma ba hastari ba, fasa fistarin yayi ya qarisa wajan motan da mugun sauri ya dawo wajan motan su yace “dude zo kaga wata mota kamar ta Companyn ka”.

Ba shiri ya fito a motan suka gangara hanyan da Jay ya fito, tun daga nesa DMD ke mamaki wannan ai motar Companyn sa na Jigawa ne.

Jay fistarin sa yayi kamun ya dawo wajan DMD ya samu yana waya da Managern sa.

Yana kashe wayan ya dubi Jay muryan sa a raunane kaman zai yi kuka yace “Jay wannan ne motan da su Ammi suka taho da shi”. da qyar DMD ya buɗe qofan motan nan ya samu handbag na Ammi da wayoyinta da komai a ciki, yana buɗewa yaga tana cikin WhatsApp akan layin sa, dubawa yayi yaga ta fara typing amma bata qarisa ba.

Abinda ta rubuta ya maimaita cikin harshen Indianci ta rubuta “Darling ina fatan za kaga saqon nan muna hanyan shiga Gombe wasu suka tare mu za..” bata qarisa rubutun ba.

Wani gigitaccen qara ya saki da qarfi cikin harshen turanci yace “koo kai ne shugaban Aljanu you most pay for this sai ka biya taɓa mahaifiyata” Jay kallonsa yayi ya sa hannu ya amshi wayan amma sai ya samu da Indianci aka yi rubutun kuma bai iya ba, kallon sa yayi yace “me ke faruwa DMD?

Idanuwansa jajir ya faɗa masa abinda Ammi ta rubuta, ba tare da ɓata lokaci ba Jay ya fitar da waya dan qiran ACP(assistant commissioner of police) da yake abokin sa sai kuma qiran Daddy ya shigo, ɗagawa yayi suka gaisa yake tambayan su ya ake ciki? Nan Jay ya faɗawa Daddy komai sai Daddy yace ya bari zai qira commissioner of police da kansa yanzu ya lallaɓa ɗan uwansa su dawo gida.

Jay yayi yayi da DMD su tafi ga abinda Daddy yace amma sam yaqi, suna staye a wajan kusan fin awa sai ga jiniyan motan ‘yan sanda.

Da kyar DMD ya yarda ya shiga mota suka koma cikin Gombe, sanin halinsa da kuma yanayin da yake ciki sai bai kai sa gidan Abiy ba yayi gidan Daddy.

Gabaɗaya bincike ake ko ta ina neman Ammi da drivern ta, lamari dai har yakai gaban governor sakamakon aminin Abiy ne governorn Gomben, al’amari yayi stamari tun ana ganin kaman komai zai zo da sauqi amma ina ba su Ammi ba labarin su, sai da aka kwashe sati guda gaba ɗaya DMD ya fita hayyacin sa a ɓangaren su sweedy kuwa kullum cikin kuka take qira tana masa itakam Ammin ta, tun yana ɓoyewa Muhseena (sweedy) har ya faɗa mata abinda ake ciki amma tayi haquri ta ci-gaba da kula da qannen su.

“Duk wannan magana da kake bai taso ba fa Mustapha yanzu abun damuwan shine Maimuna Allah Ubangiji ya bayyana ta ba maganan surutu ko wani magana daban wa zai so haka kawai yabar iyalansa dan son ransa? Kasan babu wannan mutum ɗin sai dai in ta kama ba yanda aka iya Allah ne ya aiko da hakan” faɗin Daddy da fuskansa ke cike da damuwa.

“Hmmn! Yaya kenan duk da nasan ba mai son hakan amma in ba ganganci ba me na tsayuwa a jigawan da tayi, me zai hanata qarisowa gida inyaso daga baya ba sai taje jigawan ba, kuma mai ya hanata bin jirgi ta dawo Gomben, ita sai dai a mota gaskiya ɗaya ce yaya kuma ba’a sonta Wallahi Maimuna bata ji bata kiyayewa yanzu gashi duk tasa hankalin mutane ya tashi”.

DMD da ya cika yayi fam idanuwan sa suka kaɗa suka yi jajir har fiskan sa jaa yayi dan ɓacin rai dake ƙwarzaban sa ji yake kawai kaman ya tashi ya shaqe Abiy ya huta da irin maganan da yake faɗan nan, tashuwa yayi zai haura sama ɗakin Jay sai maganan da Abiy ke yi ya tsayar da shi “yaya ka gani ko yaron nan ba abinda yake damunsa sai reni, gani yake kanmu ɗaya yanzu ina magana ya tashi zai tafi ko qala bai ce ba wato ga mahaukaci na magana hmmn duk Maimuna tabi ta lalata tarbiyyan yara basa ganin girman kowa dama sai da aka hanani auren ta amma na dage, gashi nan abinda ake jiyemun”.

Juyowa DMD yayi a fusace ya dawo palourn gaban Abiy yaje ya tsaya yana huci kaman zai maqure sa, wani malalacin kallo yake wa Abiy, ya buɗe baki da niyan yin magana “….

“Kul son karka soma mahaifinka ne shi” cewar mummy da ke qarasowa palourn.

Abiy da kana ganin sa kasan ya girgiza dan kuwa ba wanda ya kaisa sanin halin ɗan nasa “a’a ki qyale sa yayi abinda zai yi ba gashi nan ba inba reni ba har zai tsayamun a kai yana huci kaman wani maciji, kasheni za kayi ko? To shaqeni ka kasheni dan ba zan taɓa kallon laifinku ba komai kuka yi ku yara ne nuna muku aka yi, Maimuna dai ta cuce ni bata gwada wa yarana rayuwan ‘ya’yan musulmai ba dan duk musulmi na qwarai yasan ba’a ja da iyaye” Abiy ya faɗa ransa a ɓace.

Daddy miqewa yayi ya dafa kafaɗan sa yace “son calm down ka nustu kaji kayi haquri” jan hanunsa yayi ya zaunar da shi kamun ya dubi Abiy yace “Mustapha magana ya qare ba wanda zai so a dinga zagin mahaifiyarsa ko da a bayan idon sa balle a gaban idonsa”.

Qwafa DMD yayi ya tashi ya fice a gidan gaba ɗaya.

Wasa-gaske sanda aka kwashe wata guda ba Ammi ba labarin ta, abun duniya duk ya taru yawa DMD yawa, bincike ba irin wanda ba’a yi cikin Nigeria har da kewayen Nigeria ba gidan TV da ba’a bada cikiya ba haka jarida duk wata kafar sada labari ba inda ba’a bayar ba kuma tare da garaɓasa duk wanda ya kawo ta ko ya ganta yana da kyautar gida da million biyar, amma duk da haka ba labarin Ammi.

Kan DMD ya qulle ga su sweedy sun dame shi zasu zo Nigeria shi kuma baya jin zai iya komawa Canada ba tare da Ammi ba kuma baya jin zai iya bari su Muhseena su shigo Nigeria dan a yanzu ji yake ya qara tsanar Nigeria dan da Ammi na Canada ba mai taɓa ta balle sace ta.

Jay kallonsa yayi yace “dude kayi haquri mana dan Allah dubi fa yacce ka koma har dishewa kayi, addu’a ya kamata mu dage da shi ba damuwa a rai ba”. Lumshe ido yayi cikin yanayin damuwa ya buɗe baki kaman mai ciwon baki yace “Jay ba yanda na iya abun yamun yawa, da rashin Ammi zan ji ko da maganganun Abiy dan bana ta Hajja ita matsalar stufa gare ta na sani sannan ga su sweetie sun dage zasu zo Nigeria in su ma suka shigo aka sace mun su ya zanyi ai sai dai a ganni bushe a tsaye dan sune rayuwata”.

“Kayi haquri da lamarin Abiy ka san ba laifin sa bane duk aikin Aunty Amarya ne da zugi amma Abiy na son Ammi duk sonta ke sanya shi wannan hargagin”.

“Hmmn! Jay kana son magana, Abiy a da ne yake son Ammi amma tun da ya auri wannan matar ya daina son Ammi tunda yana ganin ita ta haihu ta tsufa, ni babban damuwa na su sweetie”.

“To dude ka barsu suzo mana inyaso sai su zauna nan tare da Afreen ko ka kaisu Ashaka gidan Hajja tunda kasan tana son su sosai kuma suna shiri in sweetie ta ga Hajja nasan zata rage damuwanta” kallon Jay kawai yayi ya girgiza kai yace “Jay zuwansu ba zai yiwu ba bazan taɓa barin su suzo ba ko Abiy zai kashe ni ne duk da su yaransa ne”.

Abiy zaune a palourn sa yana waya wanda daga gani mai muhimmanci ne ganin yacce ya staya yana sauraro da kyau.

Aunty Amarya ce ta yi sallama ta shigo palourn cikin shiganta na alfarman jikinta sai tashin qamshi yake, gefen Abiy ta zauna ta kwantar da kanta a kafaɗan sa har ya gama wayan kamun ya dube ta yace “sweetheart irin wannan qamshi da kyau ɗin haka”.

Murmushi ta masa tace “baby duk wa kai dan nustuwarka da farinciki ka” ta faɗa tana masa fari da ido, Abiy susucewa yayi yana faɗi a ransa “gwanda da abun ya tsaya iya kan Maimuna kar ya taɓa mun Amarya tunda dai ta zaɓi yaranta a kaina farinciki na bai dame ta ba” yana murmushi ya kalli Aunty Amarya zai yi magana sai qira ya shigo wayan sa “baby ana qiranka ba na ɗauko ma” faɗin Aunty Amarya cikin kissa, Abiy riqeta yayi yana guntun tsaki yace “sweetheart qyale mai qiran kawai baqin ciki ake mun da son yanke mun jin daɗi”.

Murmushi tayi ta zille ta miqe ta ɗauko wayan tana cewa “lah-lah baby Hajja ke qiranka fa lallai ka faɗawa Hajja magana” ta faɗa tana rufe baki ta miqa masa wayan.

Amsan wayan yayi yana murmushi yace “ai na ɗauka ko maganan maimuna ne” fakan idonsa tayi bayan ya ɗau wayan tayi murmushi a ranta tace “ni bansan inda ta shige ba amma addu’a nake gaba-gaba harrr kar ta dawo ta barmun mijina” a fuska kuma ta ɗan ɓata fuska taqi komawa jikinsa.

“Assalamualaikum Hajja an tashi lafiya? Ya gidan ya Afrah?

“Duk muna lafiya Alhamdulillahi Mustapha, ya yayanka da yaranku ya labarin maimuna?

“Uhmñ Hajja har yanzu dai shiru ba labari sai kan bincike ake”.

“To Allah Ubangiji ya bayyana ta, yarannaka fa?

“Hajja suna can Canada shi kuma yayansu yana nan gidan yaya Nura suna tare da jabeer”.

“Ashe Mustapha baka da hankali? Dan lalacewa da rashin imani sai ka bar yaran mata har su uku gatsal-gatsal a qasar turawa su kaɗai to maza-maza kayi gaggawan ɗauko su ka kaiwa Rabi’atu su in kuma ba zata iya ba ka kawo mun su nan na riqe su kamun Allah ya bayyanar da uwar tasu”.

“Hajja ba naqi ɗauko su bane yaron nan ne ya dage ba zasu zo Nigeria ba”.

“Mustapha nace ubanka kai da yaron naka, jimun shashanci kana ubansa sai ya faɗa maka abinda za kayi, wai shi ya haifa maka su ko kai ka haifi kayanka? Duba banason rashin hankali ka wuce kaje da kanka ka ɗauko yaran nan in ba haka ba ni da kai ne tunda kai kana storon ɗan cikinka ni ba storon ka nake ba balle ɗan da ka haifa, banson rashin mutunci da rashin tausayi”.

“Kiyi haquri Hajja in Allah ya yarda a cikin satin nan zanje na ɗauko su”.

“Mustapha ince ka ɗauko yara da gaggawa sai kace mun cikin satin nan? To nabi satin da gudu in kayi wasa yanzun nan zaka tafi wallahi ai kaji na ranste ba?

“Eh kiyi haquri Hajja Insha Allahu zanje jibi dan gobe akwai wani abun da zamuje dubawa tare da governor game da mahaifiyar su”.

“Mustapha kaji na ranste ba to wallahi gobe-goben nan karka yarda mangariba yayi ba tare da yaran nan suna cikin Gombe a gidan ubansu ba sha-sha-sha kawai ba, ni zaka faɗawa wani gomna ba gomna ba ubansa shugaban qasa karka kuskura na jefo qafana a cikin Gombe dan haɗuwanmu ba zata maka daɗi ba, fatan kana ji na?

“Eh Hajja ina ji Allah huci zuciyanki in Allah ya yarda goben zan ɗauko su”

“To yafi kam Allah muku albarka duka ya bayyana uwar su, ina ita Rabi’atun?

“Gatanan Hajja ba na miqa mata wayan”.

Abiy ya miqawa aunty Amarya waya ta kara a kunne tana sallama.

“Assalamualaikum Hajja anwuni lafiya?

“Lafiya Alhmdlh ƴar nan fatan kuma kuna lafiya? Ya kuma fargaba ya haquri?

“Alhamdulillahi Hajja”.

“To Masha Allah, za’a kawo miki yaranku sai ayi ta haquri da yara ko kinsan yaro sai a hankali…. ata haquri kamun Allah ya bayyana uwar ta su”.

“Lah…. Ba komai Hajja ai shi ɗa na kowa ne fatanmu Allah ya bayyana ta lafiya”.

“Ameen… Ameen Rabi’atu Allah miki albarka ya qara miki haquri kema in da rabon to Allah baki yara masu albarka, kici gaba da zama zuciyanki fari karki damu ko kaɗan da kowa kinji?

“Insha Allah Hajja, Allah qara girma ya qara lafiya”.

“Ameen ƴar nan”.

Kashe wayan Hajja tayi daga ɓangaren ta sai Aunty Amarya ta ajiye wayan ta juyo tana fuskantar Abiy tace “baby kaje ka ɗauko su yanda Hajja ta buqata inson samu ne ma ka tafi yau in yaso zuwa gobe sai ku dawo da wuri”.

Kallon ta Abiy yayi yace “sweetheart to ko zaki raka ni? Kinsan ba zan jure kwana bakya tare da ni in ba kamawa yayi ba”.

Murmushi ta masa tace “wannan ma kamawa tayi baby, Allah kaika lafiya ya dawo da ku lafiya dama nayi missing na yara na kaga zan gansu kamun Amminsu ta dawo ta qwace abunta, Nima dai Allah ya bani” tayi maganan idonta cike da qwalla har da sheshsheqa na kissa.

Abiy rungumeta yayi yana rarrashinta da maganganu masu daɗi.

Aunty Amarya ta taya Abiy shiryawa har airport ta raka sa bayan jirginsu ya tashi driver ya juyo da ita gida, tana shiga tayi jefi da mayafinta kan kujera tana huci tace “wannan stohuwa da kini-bibin stiya take dan Allah in ba kini-bibi ba kana zaune lafiya da mijinka ace za’a ɗibo ƴaƴan kishiya a kawo maka in ba cin fiska da son takurawa ɗan Adam ba, amma ba komai su da kansu zasu nemi komawa inda suka fito ko kuma duk suji a jikinsu ƴan iskan yara masu kama da aljanu ai wallahi ba don yayansu ba sai na kashe su duk na huta miji ya mutu dukiya tawa na fancama iya son raina” qaramin tsaki taja bayan ta gama zancenta ita ɗaya sai ta tashi ta shige ɗakin ta…

<< Jahilci Ko Al’ada 10Jahilci Ko Al’ada 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×