Skip to content
Part 2 of 25 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

Bayan ta idar da sallah ta gama addu’a, muryar Innar su taji tana cewa “Hassu zo ki ɗauki abincin Baabaa ki kai mata in kin dawo ki ci naki”.

Girgiza kai Hassu tayi wato dai ita Inna ko a jikinta wai an yakushi kakkausa, rashin lafiyan Adda Innai bai dameta ba.

Ta so wa tayi tayo waje ta ɗauka kwanon abincin Baabaa Mero ta wuce dan kai mata.

Da sallama ta shiga gidan, amsa mata Baabaa Mero tayi, har ɗakin ta isa ta ajiye kwanon abincin.

Baabaa Mero ta kalleta tace “wannan fa” sai Hassu tace “abincinki ne wai inji Innanmu”

Ki ce mun inji tambaɗaɗɗiyar uwarku ai dai Allah wadaran naka ya lalace ni Indo na ban mamaki wato ma ki kawo mun abinci na ita takwarata kuma dama ta cike mata fili a gidan mijinta tunda na taho da ita ta huta shikkenan zata koma gidan ubanta bari ta warke ai gidan bana uban wani bane” bala’i take tayi tace “ki ɗauki abincin kikai mata kice ba zanci ba nima ta haɗa ta cinye wataqila tayi jiki kamar shashashar nan Lami”

“Ki yi haquri Baabaa” cewar Hassu.

Mai neman kuka an jefe shi da kashin Akuya, tsohuwa kam kaman jira take sharr sai ga hawaye a idonta tana cewa “yanzu dai duk da ke yarinya ce Hansai amma dole nayi maganar nan dake ko zanji sanyi a zuciyata, ki duba fa kiga abunda Innar ku keyi wannan Adda taki in kinsan irin wahalan da uwarku tasha da cikinta mu mun ɗauka ma ba zata yi rai ba amma sai Allah cikin ikon sa ya yaye maka ya baka lafiya ka haihu lafiya, yarinya mai hankali da tarbiya da tausayi irin takwarata sai kuma dan gaka kaika kawo kunyan ɗan fari duniya kana gani ɗan ka na neman mutuwa amma ko ah jikinka, nima fa nan bafulatana ce usul ma amma baruwana da wannan al’adah ta shashanci, nasan anayi ana kunyan ɗan fari amma ba irin na Innar ku ba, dan ita nata yabar al’ada ya koma rashin sanin ciwon kai, baiwar Allahn nan Indo tana fa gidan nan har na shiga har na fito ko leqowa bata yi ba gwanda wannan tambaɗaɗɗiyar munafukar ma ta leqo wai itama da bata taɓa haihuwa ba a ɗauki kyautan yaro a baka ka wulaqanta, ina na taɓa jin wannan tambaɗewan ni meramu daso amma dai malam bai yi sa’an mata ba wallahi”

Hassun ta kara cewa “kiyi haquri baabaa Allah bawa Adda Innai haquri nima abun ba yamun daɗi amma zai wuce”

Tashi kije to ba don halinta ba zamu ci abincin kuma Allah zai saka wa takwara, ke kuma Allah miki albarka Allah qara tausayi da qauna tsakaninki da ƴar uwan ki” Da “Ameen” ta amsa ta tashi ta fice a gidan.

Baba mero sai fama take da jikar tata akan cin abinci tace “ke kuma ja’ira tunda kin samu kin farka sai ki tashi kisha wannan furar ko ƴan hanjin ki zasu yi kwari kisamu kisha magani”

Hawaye take tana yarfe hannu tana cewa “ni kam Baabaa na koshi Allah”

Baabaa ta ce “Kin koshi dan ubanki Isa nace kin koshi uwar ki Indo kika ci? Ba ki da lafiya amma sai shegen taɓara to in baki rufemun baki kin tashi kin karɓa kinsha ba zan hau ruwan cikin ki na zauna tunda kinsan yacce kike kamar taliyar murji yanzu sai na kara sa ki kowa ma ya huta”. Yarfe hannu take tana hawaye taki amsan furar balle magani.

Baabaa Mero ta ɗaura hannu aka tace “ooh ni Mero ƴar Amadu yanzu takwara da ace Indo ta jaki jiki kam bansan ya zaki zama ba mutum kaman narkakken tuwon da bai nuna ba gaskiya duk wanda ya aure ki ya kwasawa kansa jaraba da taɓara yarinya kin kai zaman ɗakin miji amma tsabar fitinan ki, kanwarki har ta fiki auki da kazar-kazar na masu lafiya kullum ke kamar wacce masu tanɗe lashe suke kame da kurwar ta, Allah na tuba maka ni jikar mai allo”

Ganin dai ba karɓan zata yi ba sai ta koma rarrashi dan tasan abarta “haba takwarata shalelen Babanta Meramu uwar Isa Maryam farar zinariya mai alkairi kinfi karfin uban mutum balle ɗan mutum, Maman Babanta ƴar gaban goshin baabaar ta”

Turo baki tayi dan bata son yacce take ce mata Meramu suna ba ko daɗin ji.

Da lallaɓa da lallami dai a haka har ta samu tasha furan ta kuma shan maganin amma hawaye kam in zaka kawo drum to zaka cika da hawaye, tana gamawa ta koma ta kwanta bacci yayi awun gaba da ita”

Kama haɓa baabaa Mero tayi tasa jikar tata a gaba da kallo tace “ooh ni Allah na nagode maka Allah ka rayamun wannan zuria’a nawa Allah ka shiryamun su, yarinya jiki a sake kaman sakakken roba abu kaɗan sai kwanciya kaman kiste, duk mutum ba auki kaman ruwan aski to Allah dai ya baki lafiya Meramu”

Itama baabaa kishingiɗewa tayi a kan nata gadon.

Can dare bayan sallahn magrib wani dattijo ya shigo gidan bakinsa ɗauke da sallama.

Inna A’i da Mama Lami suka yi da suke zaune suke cin tuwo suka amsa masa suna masa sannu.

Hassu ta tashi ta amsa ledan da ya shigo dashi tana faɗin “sannu da shigowa Baffai” Amsa mata dattijon yana shafa kanta yace “sannun yar Baffai”.

Bayan Hassu ta kai masa ledan ɗakin Innar ta kasancewan ita ce da girki sai ta wuce ɗakin su, ganin ba ƴar uwan ta a ɗakin sai taji ya mata girma.

Inna ta tashi ta bisa takai masa ruwa tana sannu da dawowa malam.

Baffa ya ce “yauwa matar aljanna sannun ku da gida kuma ya aiki?

“Alhamdulillahi” ta faɗa tana murmushi sannan ta ce “malam a kawo maka abincin nan ɗakine ko-ko zaka ci a waje nasan kayi sallah kam”

Ya ce “a kaimun waje wannan zafin ɗakin sai a hankali”

Taso wa tayi ta ɗauki taburma tayi waje.

Shumfiɗa masa taburman tayi ta ɗauko tiren kwanun abincin da ruwa duka ta kawo kan taburman.

Komawa ɗakin tayi tace “malam an kai komai”

“To Allah Ya miki albarka matar aljanna ina futowa” ya faɗa yana miqewa.

Komawa tayi wajan Mama Lami suka ci-gaba da cin tuwon nasu suna hira sama-sama.

Bayan ya gama abunda zai yi ne ya fito da bismillahirrahmanirrahim ya zauna, Tashuwa Inna tayi tazo ta sa masa ruwa ya wanke hannu ta buɗe masa kwanon tuwon, Bismillah yayi ya fara cin abincin.

Mama Lami dai taɓe baki tayi ganin abinda Inna ke yi.

Bayan yaci abincin ɗan dai-dai ya wanke hannu yayi hamdala yana sanya musu albarka sai ga sallaman Magaji yana shigowa.

Ganin dattijon sai ya nufo wajansa yana faɗin “Baffai ka dawo ne sannu da dawo wa”

“Eh baban Baffai na dawo, yauwa dai nikam ina uwata ce tun dawowa na banji mostinta ba lafiya kam?”

Inna dai bata ce komi ba kaman ma bata wajan aka yi tambayan, dama kowa dake wajan ya tsammani haka dan sanin halin nata.

Lami ba kiji bane? baffai ya qara maimaitawa.

Ehm ɗan kame-kame ta fara “malam dama bamu son ɗaga maka hankali ne tunda jikin ba har can ba dan bata ɗan ji daɗin jikinta ba, to ɗazu dai tace zata gidan baabaa tana can bata dawo ba”

Magaji ya buɗe baki ganin ikon Allah shararo qarya ba ko tsoro kaman boka, duk da dama yasan matma Lami da iya lauye magana za tayi fin haka ma.

Sai kawai yace “eh Baffai bata da lafiya tana gidan baabaa Mero”

Baffai yace “to Allah ya sauwaqa ya bata lafiya, sai kaci tuwo muje muyi sallahn isha’i mu biya naga yaya jikin nata”

“To Baffai” ya faɗa a taqaice ya tashi ya shige ɗakin da yake mallakin sa.

Ɗaki 1 na Magaji.

Ɗaki 1 nasu Hassu.

Ɗaki 1 na Inna A’i.

Ɗaki 1 na Mama Lami.

Shigewa yayi yana qara ganin koqari irin na mama lami wajan iya zagewa ta laftowa Baffai qarya duk da bai san mene asalin abunda ya faru ba amma dai yasan shigowan sa bata tsakar gidan ma kuma ba ita takai Innai gidan baba mero ba sannan ba ita taje da kanta ba tunda dai shine ya kaita, Inna dake nuna halin ko inkula akan ƴar tata tana basa mamaki ba ɗan kaɗan ba, Shima dai gashinan shine ɗan fari agidansu amma ba ruwan gwoggonsu da wannan abun al’ada-al’adan.

Zaunawa yayi yaci tuwonsa bayan yag ama ya fito da kwanukan.

Alwala yayi yace “Baffai mu tafi masallacin ko”

Fita suka yi a gidan suka wuce masallaci suka yi sallah sannan suka wuce gidan baabaa. Da sallama suka shiga gidan, samunta suka yi itama ta idar da sallahn kenan tana jan carbi.

Innai ce ta fito a ɗaki tana cewa “sannu da zuwa Baffai na” ta shumfiɗa masu tabarma.

“Sannu maman baffanta ya jikin? A takaice tace “da sauqi baffai” .

 

Suna zaune sai suka ji sallaman Baba. Duk suka amsa masa ya shigo ya samu waje ya zauna.

Magaji ne ya gaishe sa ya amsa sai Baffai da yace masa “sannu da shigowa yaya” suka gaisa.

“Baba sannu da zuwa” cewar Innai da kanta ke qasa.

“yauwa maman Baba da Baffai sannunki ko, yau kuma a gidan takwara ake hirane” faɗin Baba cikin kulawa.

Langwaɓar da kai tayi tace “a’a fa Baba banda lafiya ne shiyasa”

Ashshaa! sannu maman Baba Allah baki lafiya ko

“Ameen” cewar baabaa Mero da ta shafa addu’a.

Kallon su tayi duka, gaisheta Baba yayi ta amsa Magaji ma ya gaidata ta amsa sannan Baffai ya gaidata amma tayi kaman bata kallesa ba ma.

Kansa a kasa ya ce “Baabaata me na yi a yi min afuwa”

Cikin karaji tace “Au tambaya kake me kayi bayan ka tara marassa tausayi da imani a gidanka wai matanka”

“Ayi haƙuri Baabaa Inshà Allahu ba zasu qara ba” cewar baba cikin sigar rarrashi.

“Ba wani ba zasu ƙara ba, Musa ka ƙyaleni da me sunan mallam na zaure, wato shi dai ba zai wa Indo nasiha da faɗa ta gyara halinta ba, ace mata suna gani suna ji yarinya ta kusa mutuwa amma ba mai temaka mata dan tsabar jaraban mugunta ai ba amfanin zaman su a gidan, Ita kuma wannan gulmammiyar Lami sanda ta ganni wai ta fito duba yarinyan wai duk wannan lokutan da yarinya ta kwasa a zube a qasa wanwar a sume duka walha take yi dan ta maida waye sha-sha-sha, Walha a gidan wa inba ganin arahan gabas da kuma renamun hankali da tayi ba yaushe ta tsaida sallah biyar 5 a rana ma bare ta qara da nafila, ni dai waɗannan marassa imani da ka tara a gida basu da amfani a wajena” baabaa ke maganan kaman zata rufe Baffai da duka.

Haƙuri suke ta bata dukan su, ita dai Innai ba tace komai ba saima tashuwan da tayi ta wuce ɗakin tsohuwar.

Da ƙyar suka lallaɓa tsohuwar tasu sannan tabar faɗan da take yin, Baba ya ce “In sha Allah za a gyara Baabaa, sannan kai kuma Baffan Magaji ka musu faɗa sosai dan nima abun nan da Innar su ke yi baya mun daɗi”

Baabaa ta ce “Ka ƙyaleshi dai tunda shi sha-sha-sha ne sha-giri girbau sun maida shi mijin ta ce, yana zaune zasu kashe masa ɗiyarsa da Allah Ya bashi, tom ni dai ba zan bari haka ta faru ba, daga shi ɗin har su zan yi daidai dasu”

Haƙuri Baffai ya bada akan za’a gyara zai musu faɗa.

Magaji yana zaune gefe be ce komi ba a zanceb iyayen nasa.

Baabaa Kallon magajin tayi tace “to kaima zan dawo kanka, wai kana boko kana nan ka gama girme mana a gida sai ka rasa wacce zata auri tsoho irinka ai”

Haɗe fuska yayi yasan dama tijaran stohuwar nan da yawa bata qyale kowa.

“Yauwa baabaarmu a faɗa masa ya nemo mata” cewar Baba.

Baffai yace “a dena takura wa yarona bai gama girma ba tukun”

taɓe baki baabaa Mero tayi tace “wannan zindiqin baligun yaron ne bai girma ba? Shikkenan zan kuwa bada shi sadaka wa wata baiwar Allah ba da jimawa ba”

Qwalawa Innai qira baabaa Mero tayi “takwara, takwaraa, takwaraaa zo nan”

Zuwa tayi ta zauna gefen baabaa Meron.

Baabaa tace “niifa banson zaman ɗakin nan kaman munafuka”

Baba ya kallesu yayi murmushi, cewa yayi “baabaarmu kar dae mu jiki da takwararki”

Baabaa tace “Allah sauwaqa a jimu”

Baba ya maida kallonsa kan Innai yace “mamar baba meke damunki?

take idonta ya kawo ruwa, cikin shagwaɓa tace “Kai na ke ciwo sai ciki na”

Salati baabaa Mero tayi tace “kunga ja’irar ƴarku ko tun da rana nake binta ta faɗa mun amma taqi faɗin meke damunta sai yanzu dan taga iyayenta shikkenan zaki tashi ki bisu dama ba za’a bar Hassu ita kaɗai ba tun da dai ke ma munafurcin kike son koya yarinya kaman narkakken tuwo, nan yanzu ma daga tambaya sai kuka, ooh ni Mero Allah nagode maka shikkenan ai kema ɗin tattara ki zamu yi mu aurarki”.

Suka ci-gaba da hiransu da baabaar tasu cikin raha, ita kuma Innai ta kwantar da kanta a qafan baabaa mero.

Magaji ya tashi ya fice yace da iyayen nasa in sun gama yana waje.

Baabaa Mero ta bisa da harara tana cewa “mutun sai jarababben baqin hali ai zaka ji dashi dan ni dai ba kayo halin miji na ba”.

Can su Baffai suka wa baabaar tasu sai da safe suka fice a gidan.

Magaji bayan ya fito wucewa yayi dandalin dake qauyen direct abunsa, Baffai da suka fito basu gansa ba sunsan za’ayi haka daman dan haka tafiyansu suka yi suna hira na yan uwa.

Baba ya qara jan kunnen Baffai akan abinda matansa keyi, lallai ya musu faɗa su gyara hakan bai kamata ba inba dai basu son zaman lafiya da baabaa Mero ba.

Bayan ya gama jaddada wa ganin nasa sai suka yi sallama Baffai ya shige gidansa kasancewan basu da nisa da baabaa Mero, Baba ma ya wuce nasa gidan dake gaba da na Baffai ba sosai ba.

Ya shigo gidan ya samu duk basu tsakar gidan, ɗakin Innar su Hassu ya wuce da sallama ya shiga, samun ta yayi ita da Hassu suna taɗi tana haska mata tana homework nata( kasancewansu fulani kuma waɗanda ke qauye bai hanasu karatun boko ba tunda yanzu duniya a waye take).

Ganin Baffai ya shigo ta tashi ta tattara littatafan nata dan dama da gama ta masu seda safe, albarka Baffai ya sanya mata. Ɗakin mama Lami ta wuce dan ba zata iya kwana a ɗakinsu ita ɗaya ba tsoro take ji in ƴar uwanta batanan.

Da sallama ta shiga, amsa mata mama Lami tayi.

Ba ta dai ce mata komi ba ta haura gado ƙarami dake ɗakin bayan ta kakkaɓe ta kwanta ta lulluɓu abunta, mama lami ba tace mata qala ba kawai ita ma lulluɓuwan ta tayi sai bacci kuma.

Baabaa Mero ta lallaɓa Innai taci tuwo ta qara shan magani, suna hiransu baabaa mero na mata ta-tsuniya, har suka kwanta zuciyan ta cike da tunanin ƴar uwanta zata kwana ita ɗaya a ɗakin nasu gaba-ɗaya sai taji ba daɗi, a haka suma har baccin ya ɗauke su.

Baffai tunda ya zauna nasiha yake mata akan inba zata daina wannan halin ba to ta rage don kuwa bai kamata ba, Allah zai mata hisabi tsakaninta da ƴar da ya bata.

“Aishatu su yara da kike gani da Allah ya bamu amana ne ya bamu ba wayonmu ko dabarar mu ba, amana kuwa kinsan ko ɗan adam ne ya baka to dubi abunda sakaci da amanansa keja maka balle wanda ya haliccemu da kansa ya bamu amana muyi sakaci dashi me kike tunani a kai? Tabbas wannan ba al’ada bane A’ishatu dan naki ya wuce a qira sa da hakan, dan girman Allah ki aje wannan abu a gefe ki rungumi abunda Allah ya azurtaki dashi, dan su ‘ya’ya arziqi ne babba ma kuwa, ko kina ga a wannan duniya tamu in uwa ba taja ɗan ta a jiki ta soshi ba wani zai so mata shi ne? Ko ɗaya dan wannan alhaqi ne dake kan uwa kuma duk abinda wani zai nuna wa ɗan ki na soyayya ko tsangwama(hantara/qiyayya) to kece sila dan kece malamar da kika nuna hakan a koyarwanki. Dan girmam Allah ki gyara A’ishatu kamun lokacin hakan ya qure miki”.

Inna kanta a qasa bata ce komi ba illa iyaka “ayi haquri malam”

Taso wa tayi ta haye gado ta kwanta

Shima baffan hawa yayi dan ya lallashi matar aljannan sa, tunda yaga abun sai a juya ɗayan sigan dagann sai…

*****

RUGAN HAMMAN

Shine sunan rugar tasu, ruga ce da take nan kaman gari ba ruga ba sakamakon cikan da tayi da kuma cigaba da ake samu a rugar ta hanyan asibiti da makarantu etc…

Fulani ne mafiya yawa a rugan sai ɗaɗɗaya-ɗaɗɗaya daga wasu yaruka kaman Bolawa, Terawa, Wajawa har da Hausawa.

Rugan ya zama kaman gari ne sakamakon fulanin rugan mazaunane ba matafiya ba, suna gudanar da rayuwansu cikin nasarorin ci gaba Alhamdulillahi.

Suna karatun muhammadiya sosai da boko duk da ba su da na gaba da primary, rugan nasu na qarqashin qaramar hukumar 𝘼𝙨𝙝𝙖𝙠𝙖 dake garin Gombe State.

In mutum ya gama yaƙi da jahilci da primary a rugan su kan fito cikin ƙaramar hukumar Ashaka dan ci-gaba da secondary…

 

<< Jahilci Ko Al’ada 1Jahilci Ko Al’ada 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×