Skip to content
Part 3 of 15 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

Tana taso wa da safe bayan sun yi sallah sun idar ta ɗau tsintsiya ta share ɗakin ta gyara musu sannan ta fito tana share tsakar gidan.

Baabaa Mero da fitowan ta kenan daga banɗaki ajiye butan hannunta ta yi tace “ke dai takwara Allah kawo miki sauƙi ko kaɗan ba kya gajiya da wahala shiyasa gaki nan ba auki kaman taliyar murji dan nemawa mutane wata jarabar ba ki da lafiya kin kama aiki, yarinya sai son manyan ce kaman wata Babbar mata”

Innai tana jin tsohuwar amma ko a jikinta sharan ta gama ta tattara kwanuka tace “Baabaata bari na kai kwanukan gida na dawo”

Baabaa Mero taɓe baki tayi ta karyi goronta sannan ta ce “in kinga dama karki dawo sai bayan shekara 100, wahalalliya kawai ai so kike kije ki aikatu da jikin da ba kiji sauƙi ba, yarinya sai shegen jarabar rashin ji, ni dai Allah ya gani ba haka halina yake ba wai ance mutum ya kan iyo halin takwaransa to aradu baki biyo halina ba dan ni nan bana barin ko ta kwana sannan bana ɗaga qafa ba ruwa na da jarabar haukan stiya amma ke a masu suna Maryam ɗin ma kamata yayi ace maki damo(sarkin haquri) yarinya zuciya kaman kare ya lashe, ni ɓacemun daga gani kamun na qarisa ki da kaina” ficewa Innai tayi tana murmushi bata tsaya sauraran baabaa Mero ba dan tasan duk da sonda take mata yanzu zata iya kwaɗa mata abu.

Baabaa Mero ta ci-gaba da mitan ta kaman zata daki babu sannan ta ɗauko kwanon madaran da ta ajiye dan ta bawa takwarar tata tasha da magani sai kuma ta bostare ta tafi gidan nasu da zata mutu bamai kallonta, zama tayi ta shanye abunta tass sannan tace “Allah ganar da ke mai qaunanki takwara”.

Fitowa tayi daga gidan baabaa Mero tana murmushi, tafiya take cikin nustuwa wanda wasu sukan ɗau tafiyan nata akan rigima ta keyi.

Yarinya ce yar kimanin shekara 14 da haihuwa amma in ka ganta sai kace takai 16 year’s, domin halittan da Allah ya mata. Fara ce sol kuma Siririya ce ba mai jiki ba(qiba) abunka da bafulatana, amma rashin jikinta da qarancin shekarunta bai hana halittar da Allah yayi mata bayyana ba dan tun bata gama girman ba maqerin budurci ya bayyana gare ta.

Tana da ƙugu(mazaunai), kuma duba da gashin dake kwance gaban goshinta da kuma sajen fuskanta hakan ya isar da cewan Allah ya mata baiwan gashi Masha Allah! Round face take dashi mai ɗauke da dara-daran idanunta (golden eyes) farare ne tass kaman madara kai kace idon jinjirine haka baqinma baqi wuluk, tana da yalwan cikan gashin gira wanda har ya haɗe hakan kuwa sai ya bada wani sirri a kyau nata, Tanada dogon hanci wanda shi da biro banbancinsu kawai rubutu ne, ɗan madedecin bakinta wanda inka gani za kayi mamakin anya tana ma cin abinci kuwa tsabar ƙanƙantarsa, tabarakhallah Masha Allah don kyakkyawa ce ta ajin ƙarshe wanda ƙarancin shekatunta ba su ɓoye ni’imomi da baiwan da Allah ya azurta ta dasu ba, duk da ba wai girman ya gama bayyana a gareta ba.

Innai kenan wacce asalin sunanta shine Maryam takwara ga mahaifiyar Baffanta wato Baabaa Mero.

 

A nutse ta yi sallama ta shiga gidan nasu ta kuma yi sa’a Baffanta na nan, ta samu Innar su na aikin ɗumame ƙanwarta Hassu kuma na shara.

Kallon Innar tasu sai jikinta yayi sanyi amma a haka ta qarisa wajanta, durqusawa tayi har ƙasa ta ce “jamɓanduna Inna”

Inna A’i kanta a gefe tana ayyukan ta ko juyowa ta kalli yarinyar nata ba tayi ba kawai ta girgiza kai alaman ta amsa gaisuwan.

Daman in da sabo ta saba da hakan tasan iya abunda Innan tasu za tayi kenan, kanta a qasa haryanzun jiki a sanyaye kaman kullum in hakan ya faru ta wuce ɗakin mama lami.

“Jam ɓanduna mama”

(Antashi lafiya mama)

“Jam innai noi ɓandu ma”

(Lafiya innai ya jikin ki)

“Ɓandu waɗu dama”

( jiki dasauqi)

“To Allah hokke en jam”

(Allah qara sauqi) Mama Lami ta faɗa tana jera kwanukan ta.

Da “Ameen” Innai ta amsa sannan ta miqe ta fito a ɗakin.

Hassu ta gaishe ta cikin fillanci tana tambayan ta jikin nata “Adda Innai noi ɓanduma?” “Ɓandu waɗu dama Hassu am”.

Mawanki ta wuce dan tayi wanke-wanken, Hassu tace “Adda zanyi wanke-wanken ki bari ki huta abunki kinga baki da lafiya”

Murmushi kawai tawa qanwar nata ba tace komai ba. Haɗa kwanukan wanke-wanken tayi da wanda ta shigo dasu daga gidan baabaa duk ta wanke su, bayan ta kammala ɗakinsu ta wuce ta gyara musu.

Tana kammala ayyukan ta Hassu ma ta gama sharan da take yi dai-dai Baffan su ya fito a ɗakin Innar su sai dukansu suka nufe sa, suna zuwa suka stugunna suka gaishe sa cikin fillanci.

Amsawa yayi yana sanya musu albarka sannan ya tambayi Innai jikinta, da sauqi ta amsa masa, duk gaisuwan da suke yi da fullanci suke magana.

Magaji ya fito a ɗakin sa shima ya tsugunna ya gaida Baffan nasu, Baffai ya amsa cikin fara’a. Gaishe da shi Innai da Hassu suka yi ya amsa masu sannan shima ya tambayi ya jikin Innai ɗin, da sauqi ta amsa masa.

Albarka baffa ya sanya musu duka yace kowa yaje ya karya.

Inna ke madafi tana raba musu abun karyawan, Innai zuwa tayi tace “Innan mu bari in qarisa miki”

Ba tare da Inna tace komai ba ta tashi ta fice a madafin.

Ƙarasa wa Innan ta aikin tayi ta raba komi har da madaran da Hamman su magaji ya kawo ta raba ta sawa kowa nasa, ta kaiwa Hamman su nasa har ɗakinsa sannan ta qira Hassu kuma takai na Baffai, ita kuma ta miqawa su Inna nasu, Hassu ta ɗauka musu nasu suka yi ɗakinsu da shi.

Ɗumamen tuwon surfaffen masara da aka wanke yayi haske sosai da miyar ɓaskoje bushashshe(bushashshen kuɓewa) da yaji nama da man shanu, sai naman zabbi da kuma madaransu mai ɗumi.

Karyawa suka yi sannan suka haɗa kwanukan Hassu ta wanke masu bayan ta dawo kai wa baabaa Mero nata.

Ɗakinsu suka shige ko waccen su ta kwanta dan hutawa amma kowa da abunda take tunawa a ranta.

Innai da ta faɗa duniyar tunani hawaye ne ya gangaro a idonta wanda ke nuni da damuwan da take ciki, sai tace “Duk da kasancewana yarinya amma abun na damuna anya Inna ce ta haifeni anya ba tsintata suka yi ba suke ɓoye mun” sai kawai ta fashe da kukan da bata san ma ya qwace mata ba.

Hassu ta tashi tana cewa “Adda Innai ɗume?”

Innai cikin hawaye tace “Hassu jam, wala ko ɗume”

Itama hawayen ta fara tana magana cikin harshen fillanci “Adda Innai ki faɗamun bana son ganinki cikin damuwa in baki faɗa wa ƴar uwanki abinda ke damunki ba wa zaki faɗa wa?”

Cikin Kukan ta ce “Hassu ba za ki fahimta ba ko na faɗa miki, Hassu ina jin kaman zan mutu bansan me nawa Inna ba bansan me yasa Inna bata qauna ta Inna bata sona kaman ba ita ta haifeni ba” ta faɗa tana hawaye

Haƙuri take ba ta itama tana kukan “Adda kiyi haƙuri Allah Inna na sonmu kin ji” cewar Hassu tana rungume ƴar uwanta.

Haka suka rungumi juna tana taya Addan nata kuka kai kace marayu ne ko kuwa mutuwa aka musu.

Baffai ne a ɗakin Inna bayan ya gama karyawa ya ce “tom A’ishatu yanzu ke me shawaranki akan makarantan Innai da nake son tayi gaba, dan gaskiya wannan al’ada ta aurar da yara da wuri ba ruwa na, ni ba wani al’adan da zan gwada wanda yake kaman jahilci ya sanya na cuci rayuwan yara na”

Shiru Inna ta yi ba ta ce komai ba, Baffai cikin hasala da ƙuresa da halin take yi ya ce “wai ke A’ishatu me yasa kika zaɓi haka ne? Ko kaɗan baki son gaskiya na jima da fahimtan ki, wannan ƴar taki ba ki tunanin da ƙanƙantan ta ciwon zuciya zai iya kashe miki ita، wannan kalan banzan al’adan naki zai sanya ki tafka babban asara tunda kina uwa amma zai sanya uwa ta gagara ceton rayuwar ɗiyarta sannan ta kasa mata abunda zai zama ci-gaba a gare ta har da ita uwar kanta tunda komi ɗa ya samu a rayuwa ba mai amfanuwa ko morar sa irin uwarsa barin ma dai ɗiya mace, A’ishatu yanzu ke baki tunanin Innai zata fara tunanin ba kece kika haifeta ba shiyasa kike mata haka? Yarinyar nan ki godewa Allah da yayo ta da haquri sannan ki kiyayi ranar qarewan haqurin ta ɗan aje-aje zata daina kallonki matsayin mahaifiya irin halayen da kike nuna matan nan” ita dai Inna kanta na gefe bata ce komai ba har yanzun.

Tsaki Baffai yaja a hasale ya miqe ya fice a ɗakin dan in ya cigaba da zama zasu iya samun mastala.

Ɗakin magaji ya wuce, ganin Baffai sai Magaji ya tashi ya zauna yana cewa “Baffai da kanka ba ka qirani ba”

Baffai cikin murmushi yace “bakomi baban baffa, yanzu dai shawara nazo muyi game da yar uwanka, yanzu kaga sunyi wannan jarabawa wai na gama firamare(primary) to kana ga ya za’ayi ta wuce gaba ina tunanin zai fi ba”

Magaji ya ce “Baffai gaskiya ya kamata kam ta wuce gaban inya so sai a lallaɓa Baabaa ta ajiye batun aure a gefe tunda ko saurayi ba ta da shi, kuma sai dai a nemi na zuwa a dawo dan makarantan kwanan nan sai a hankali”.

Baffai ya ce”amma Magaji samun abun hawan da zai ke kai ta ya dawo da ita ba matsala ba”

Magaji yace “babu matsalan komai Inshà Allah Baffai, kawai a nema mata wanda zai ke kai ta yana dawo da ita nasan za’a samu ko yawale aka wa magana sai ake biyansa duk sati ko wata”

“Shikkenan in taji sauqi sosai sai kuje kuyi komai anan cikin Ashakan” cewan Baffai cikin gamsuwa da shawaran yaron nasa.

Magaji yace “to Baffai Allah ya qara mata lafiya ya kuma qara buɗi da girma”

Da “Ameen” Baffai ya amsa sai suka ci-gaba da tattaunawa kamun can Baffai ya miqe yana faɗin “Magaji ba na fita to kasan akwai wani ruga nan gefen mun nan tom akwai wata baiwar Allah ba taji daidiba an aiko naje”

Miqewa shima Magajin yayi yana cewa “a dawo lafiya Baffai Allah bata lafiya” Tare suka fito a ɗakin.

Suka bi gidan baabaa mero suka gaisa kamun Baffai ya fice ya tafi rugan dake gefen nasu.

Baabaa mero ta kalle sa ta ce “yanzu kai Magaji ka gaya wa kanka gaskiya biyewa baffanku kake yi ko, in na maka maganan aure sai ka haɗa fiska kaman shanun huɗa(garma), kaman wani mara ishashshen lafiya, to dan Allah in ma lafiyan ne baka da shi ai ka gaya mun na nema maka magani, yo me abun kunya a ciki ni da na haifi ubanka mene ban sani ba, kawai kace mun Baabaa abun baya tashi ko bakajin buqatuwa, shikkenan magana mai sauqi niko na bazama na nema maka magani yacce zaka koma kaman doki dan qarfi, amma ka girma ka riqa ka balage kaqi aure wai kai boko ba bokoko a wuta aradu sa’annin ka akwai masu yara huɗu wasu har shida ma, shikkenan ya rage maku kai da Baffan naku in ma baqin ciki yake wa kansa na ganin jikokin sa to kansa ya wa sai nan gaba zaku san soyayya ce nake muku shi yasa na matsa kuyi aure…

<< Jahilci Ko Al’ada 2Jahilci Ko Al’ada 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×