Skip to content
Part 4 of 10 in the Series Jini Ba Ya Maganin Kishirwa by Qurratul Ayn Salees

Yana fitowa daga wankan kai tsaye gaban mudubi ya nufa, tun kafin ya kai ga ƙara sawa idanuwansa suka tsinkayo masa ƙananan kaya ya she akan gado riga da wando,  da dukkan alamu Sakinah ce ta ajiye masa su, sai faman wani tashin ƙamshin dad-daɗan turare su ke yi, ɗan taɓe baki ya yi kaɗan kafin ya ƙarasa  gaban gadon ya fara ƙoƙarin sanya wa.

Yana kammala shirin kai tsaye falo ya nufo, lokacin Sakinah ta kammala  jere masa abincinsa tsakiyar falon, kai tsaye wajen abincin ya nufa ya zauna, yayin da Sakinah ta yi murmushi tare da tsugunnawa ta fara zuba masa abincin, har ƙasan ransa bai yi ni yar cin abincin ba, amma to zali da ya yi da abincin da yafi so da ƙauna ga kuma tashin ƙamshin abincin na musamman ya ke jinsa a yau, nan ta ke ya ji kamar an yashe masa cikinsa har ya ƙagauta da son fara ci, sai faman haɗiyar yawu ya ke.

Sakinah ta ajiye masa abinci a gabansa, nan da nan ya fara aikawa cikin bankin cikin, ba Sakinah ba shi kansa ya yi matuƙar mamakin irin abincin da ya ci, kai ka ce wunin ranar bai ci komai ba ne, sabida irin tulin tarin abincin da Hajiya Shema’u ta ciyar da shi a yau, bai yi tsammanin zai sake kallon wani kalar abinci ba a ɗan ta ƙaitaccen lokaci kamar wannan ba, amma sai ga shi lokaci guda ya share abinci faranti guda.

Sosai Sakinah ta ji daɗi a ranta, sabida rabon da ya ci abinci da yawa haka tun kafin ya fara maganar aurensa, farin cikinta kasa ɓoyuwa ya yi har sai da ta kai ga furta.

“Mijinah abincin ya yi maka dadi sosai, da dukkan alamu bakinka ya yi kewar girkin gimbiyarka ko?”

Kamal ya yi ajiyar zuciyar kawai tare da miƙa hannu ya ɗauki ruwan da ta zuba masa cikin kofi ya sha kaɗan ya ajiye kafin, tare da ɗan yin gajeren murmushi kafin ya ce.

“Ni ma dai na yi mamakin yanda aka yi na ci abincin da yawa haka, kuma kin san cewar a ƙoshe na ke wallahi, amma dad-daɗan ƙamshin girki ya ja ni na wafce abincin ciki biyu.”

A tare suka yi gajeriyar dariyar, kafin su yi shiru ko wanne daga cikinsu yana saƙe-saƙe cikin ransa, Kamal ya katse shirun da faɗin.

“Kin duba kayan dana kawo miki kuwa?”

“Wayyo..! Wallahi shaf na sha’awafa inata faman aiki ne tun sanda ka fita ka barni, ko da ya ke yanzuma bata ɓaci ba, bari na ɗauko mugani tare kallon ya fi daɗi ma.”

Ta kai maganar tana mai kanne masa ido ɗaya, ta miƙe tsaye tare da ba shi baya ta nufi cikin ɗaki, baki galala ya bita da kallo cike da guntun murmushin da bai san yana yinsa ba, sai daga baya ya yi gajeren tsaki tare da ɗan bugun kansa kaɗan yana girgiza wa.

Ɗaya bayan ɗaya ta fito da akwatunan kafin ta zauna tana mai da numfashi a hankali, daga baya kuma ta hau buɗe kayan tana gani, ci ke da tsantsar farin ciki duk wanda ta ɗa ga sai ta ce.

“Masha Allah, kamar kasan kuwa zan so wannan.”

Ƙananun kaya saiti biyar ta gani ciki, tare da dogwayen riguna guda uku, nan da nan ta miƙe cike da ɗauki ta fara gwadawa, wai ya gani idan zasu yi mata kyau, tun Kamal na basar da ita har dai ya biye mata, har da su dariya da hira kala-kala cike da nishaɗi, Sakinah ta ji tamkar su dauwama a haka, nan ta ke wasu al’amuran watannin baya suka fara katantanwa a cikin kwakwalwarta, kwallar da ke ƙoƙarin zubar da ruwa kan fuskarta ta yi saurin sharewa tare da saurin kau da tunanin da ke shirin bijiro mata, a daidai lokacin kuma suka sinkayo sallama bakin ƙofar falon.

Sakinah ta amsa sallamar tana mai nufar ƙofar falon, ganin Sajidah tsaye ya sanya ta buɗe baki cike da dariyar jin daɗi ta ke faɗin.

“Shigo mana kamar wata baƙuwa, sai ki tsaya kina faman kwaɗa sallama haka.”

Sajidah ma dariyar tayi kafin ta bata amsar.

“Kin ji kuma Aunty Sakinah, ko ba baƙuwa ba ce ai sallama ta zama dole a gare ni, domin jajjada koyarwar addinin islama.”

“Kin yi gaskiya sarkin zance.”

Kamal ya bata amsa yana mai miƙewa tsaye daidai lokacin aka fara kiraye-kirayen sallar isha’i.

“Kin zo a daidai, na miƙe a daidai ga kiran sallah can ana yi, ya ki ka baro Abba da Umma, ya jikin Sajjad kuma?”

“Alhamdulillahi duk suna gaishe ku, na jima da zuwa fa ina wajen Hajiya muna gaisawa tun ɗa zu.”

“Masha Allah da kyau hakan, ni dai zan wuce masallaci to.”

“A dawo lafiya Yayana.”

Cewar Sakinah kenan ta faɗa da murmushi akan fuskarta, a cikin ransa ya amsa tare da fi ce wa da sauri daga falon, Sajidah ta zauna ƙasan kafet tana faɗin.

“Wash Allah na, duk na gaji wallahi Aunty Sakinah.”

“Kamar wacce ta yi tafiyar wuni guda, ban son raki fa.”

Sakinah ta ƙarashe maganar tana hararar Sajidah.

“Ba za ki gane ba ne Aunty Sakinah, wai nan kayan lefe ne ko me?”

Ta yi tambayar tana mai kai wa kayan cikin akwatunan kallo, kafin ta kai dubanta kan Sakinah.

“Ba dai ma gwadawa ki ke yi ba?, kai Aunty Sakinah ke ma dai sai a hankali wallahi.”

“To me kuma na yi? Kayan faɗar kishiya ne ba lefan wata ba, bare ki ce na gwada kayan wata.”

“Tab..duk da hakan kuma ki ke gwadawa? Kai Aunty Sakinah ko kishi babu, sai wani faman harkokinki ki ke yi, Allah da ni ce ko kallon kayan ba zan yi ba wallahi.”

“Ke dai ki ka sani, ni kuwa babu abin da zai dame ni yarinya, gara ma tun yanzu ki koyawa kanki kyakkyawan kishi, ka da ki biyewa sharrin zuciya da jin daɗin sautin bugun gangar sheɗan ki sanyawa kanki baƙin kishin da zai kai ki ga halaka.”

“Kamar ba auren So ku ka yi da Yaya Kamal ba, ai dole zaki ji kishi fa Aunty Sakinah, ko ya ya ne.”

“Wannan ai shi ne asalin kishi kin ji ko, ki duba kissoshin matayen Manzon Allah (S.A.W), suna yin kishi ne da dukkan gaskiyar soyayyarsu akan mijinsu, ƙara ƙaimi suke a kullum wajen rige-rigen kyautata masa da dukkan abin da suka san ya fi so da ƙauna, domin samun gurbi a mazaunin zuciyarsa, ina son kwatanta ko da kwatan-kwacin hakan ne, na san ba zan taɓa yin ko da rabi-rabin kaso ɗayan yanda suka yi ba, amma ko daidai da gwayar zarra ne ina son na kwatanta Sajidah.”

“Hmm..to Allah ya ba da iko, ya samu a danshin ku, amma gaskiya Aunty Sakinah ke ta musamman ce a zamanin abu ne mawuyaci samun kamar ki.”

“Amin, ban son iya shege kuma, akwai waɗanda suka fini sosai Sajidah ke kanki idan kin daure wata ƙila ki fini ma.”

“Gara dai da kika ce wata ƙilan.”

Sajidah ta bata amsa cike da tsokana, yayin da Sakinah ta ɗan bugi bayanta kaɗan , suka sanya dariya dukansu, ka fin su rufe akwatunan Sajidah ta taimaka mata suka mayar da su ɗaki.

Kai tsaye Sajidah ɗakin saukar baki ta shige domin yin alwalar sallar isha’i, haka ma Sakinah ɗakinta ta nufa zuciyarta fari tas har wani murmushin jindaɗin zuwan Sajidah ke kufce mata.

Bayan sun idar da sallah har ɗaki Sakinah ta kaiwa Sajidah abinci da dukkan abin da zata buƙata tana faɗin.

“Ki kwanta da wuri ɗan Allah, sabida tashin wuri za mu yi gobe don yin aiki.”

“Insha Allah, ni dama kin bar abincin na gaji wallahi bacci kawai na ke da buƙata yanzu.”

Harara Sakinah ta jefa mata kafin ta ce.

“Ka da ma ki fara wannan tunanin malama, ki ci abinci ka da ki soma kwanciya haka kinji?”

“To zan ci amma kaɗan.”

“Ke ki ka ji yo kuma wannan, kin ga tafiyata.”

Ta kai maganar tana mai fice wa daga ɗakin tare da rufo mata ƙofa, ta koma nata ɗakin domin yin shirin bacci, sabida itama yau agajiye ta ke jin jikin nata, ga shi har lokacin Kamal bai dawo ba, ko ya dawo yana gun Hajiya ne bata sani ba? Domin tasan shi bamai hirar waje ba ne, bare ta ce ya tsaya hira wajen abokai ne.

<< Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 3Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 5 >>

1 thought on “Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.