“Kamar kin mance da wacece ni Hajiya Turai? Shema’u fa na ke, ka da ki manta da wani abu guda ɗaya, shiru ba ya da wata katara, shintatar shiru abu ne mai matuƙar wahala, amma wanda ya yi shiru ba’a san iya tsaurin tana dinsa ba.”
“Wato dai idan na fahimci zancenki akwai abin da kika taka?”
Nan ma dariyar suka sake yi cike da shewa suna tafawa, yayin da kwanyar kan Hajiya Shema’u ke ƙara faɗi, tana jin tamkar dala da goron dutse suke ɗora mata.
*****
Al’amarinsu Sakinah kuwa tuni sunyi kace-kace da aiki, duk iya ƙoƙarinta na kau da kai don kada a fahimci halin da ta ke ciki abin bai yi ba, Sajidah ce ta dubeta da faɗin.
“Aunty Sakinah mene ya samu idonki ne?”
“Me kika gani?”
Ta sa ke tambayarta itama daidai sanda ta ke karɓar yankan albasar da ke hannun Sajidah.
“Gani na yi idon naki ya yi ja duk ya kumbura.”
“Oh babu komai fa, jiya ne idon ya yi ta yi min ƙaiƙayi ni kuma na sosa.”
Sajidah ta dube ta duban rashin yarda da maganarta, harta motsa baki da nufin sake magana Sakinah ta yi saurin katse mata maganar da faɗin.
“Kinga a yi aiki ba surutu ba, je cikin ɗaki cikin dirowar (drower) gado zakiga baƙar leda ki ɗaukomin, yi sauri dan Allah.”
Sajidah ta mi ƙe tsaye ranta fal haushin katse maganar tasu da Sakinah ta yi ƙoƙarin yi, domin ta tabbata ba gaskiya ta fada mata ba, tasan halinta kuma da ta matsa da tambayarta zata faɗa mata ko mene ne.
Sajidah na ba da baya Sakinah ta saki wata ajiyar zuciyar mai sauti, kafin ta cigaba da aikin nata tana faman saƙe-saƙen abubuwa da dama a cikin ranta.
Sai kusan takwas da rabi Karima ta zo gidan, ita ma kallo ɗaya ta yi wa Sakinah ta fahimci akwai babbar damuwa a tattare da ita, aiki ne kawai da mutane ya sanyata bagarar da zancen amma taci alwashin tabbas sai ta ji musabbabin damuwarta.
Tun wajen sha-biyu da rabi suka kammala komai na dukkan abin da suka san za’a buƙata, tuni sunyi wanka sun shirya cikin wani leshi c-green wanda aka yiwa jan ado, hatta takalmi da jaka zuwa mayafi duk ja suka saka, Karima ce ta yi musu ɗinkin dukkansu duk da cewar ba su san da ɗinkin ba ma, har mai kwalliya (make-up) Karima ta mussamman ta ɗauko wai a fito mata da aminiyarta fili, insan samunta ne ma tafi amaryar kyau.
Bayan sallar juma’a kamar yanda aka rubuta a jikin katin aka daura auren Kamal da Hajiya Shema’u, akan sadaki naira dubu hamsin daurin auren da ya samu halartar dubban tarin jama’a, sabida Hajiya Shema’u mutumce mai tarin mutane ga kuma uwa uba sanannen Mahaifinta babban ɗan kasuwa mai tashen kuɗi Alhaji Mamman Dan Liti.
Tuni gidan ya ɗin ke da ƙawaye da abokan arziki sai faman hira ake yi game da ciye-ciye, ɗaya daga cikin ƙawayen nasu mai suna Zainab ce ta janyo Sakinah gefe suka samu waje guda suna tattaunawa.
Zainab ce ta dubi Sakinan da faɗin.
“Ƙawata jiya-jiyan nan sai na samu mummunan labari wajen Hidaya ta ke faɗamin batun yi miki kishiya, ai kuwa na so sai na zo dole tayan alhini.”
“Wallahi kuwa Zainab al’amarin ne sai addu’a.”
Zainab ta taɓe baki kafin ta cigaba da faɗin.
“To ke wanne mataki kika ɗauka?”
“Kinji ki da wani zance Zainab wanne mataki zan ɗauka wanda ya wuce haƙuri.”
“Hakuri kika ce fa Sakinah?”
“E mana ni da ba hukuma ba wanne bataki zan ɗauka a gare ni wanda ya wuce hakan.”
Zainab ta kwashe da dariya mai sauti, daidai sanda ɗaya daga cikin ƙawayensu ta zo wajen tana faɗin.
“To su Zainab sarakan ƙeta wanne batu kuke tattaunawa haka kike ta sheƙa dariya?”
Zainab ta jawo hannunta tana cike da dariya take faɗin.
“Zo ki zauna ki jiyemin zancen Sakinah dan Allah Hidaya, ta bani dariya wallahi, wai kan kishiyar nan da za’a yi mata, wai nace wanne mataki ta ɗauka? Wai ita ba hukuma ba wanne mataki zata ɗauka?”
“Heeeeeyyyhhh.”
Suka sake kwashewa da dariya dukansu suna tafawa, Hidaya ta riƙe haɓa tana faɗin.
“Kina nufin zuru kika yi musu ita da mijin? To waya ce miki ita a zaune ta ke? Bata labari Zainab.”
Suka sake sanya dariya, Sakinah tayi ajiyar zuciya tana faɗin.
“Kufa kuna da matsala wallahi, kuyi wa mutum magana kai tsaye sai kun tsaya kuna iya shege da abin da kuka saba”.
“A’a yallaɓiya zauna ki ji batun yanda ya ke.”
Zainab ta faɗa tana mai riko hannunta, kafin ta cigaba da magana.
“Kin san Allah Sakinah kwanakin baya ai ni ma da tuni kunji mummunan labari, Abban Zahra ya fitittike shi ya ga wacce ya ke so aure zai kara kaza-kaza, na zuba masa ido sai da magana ta fara kankama na bazama neman taimako nan na hadu da Mallam Kallah wallahi mutumin ba dai aiki ba tuni maganar aure ta kau, yanzu ko batun ba ya yi, ko zancen ƙarin aure baya son a yi masa yanzu.”
Hidaya ta karɓe zancen da faɗin.
“To kin manta ni ma ba kishiya ce ta ke neman fiddani gidan mijina ba, amma dana baki labari kika kaini gare shi ina kishiyar ta ke yanzu? Ai kawai wallahi Sakinah ki zo muje a yi ta ta ƙare kema dan Allah, ni naga ma kaman auren bai dame ki ba wallahi, Allah ni idan kinji yanda na ke ji a raina tamkar ni ake yi wa kishiyar.”
Ta ƙare maganar tana mai jan tsaki, yayin da Zainab ta ƙara keɓe leɓuna tana mai faɗin.
“Uhmm to ba dole muji ciwo a cikin ranmu ba ai duk mun zama ɗaya duk abin da zai samu ɗayanmu dole mu haɗu dukanmu mu kokawa juna.”
“Karai kuwa, yanzu dai ya kike ganin za’a yi Sakinah?”
Cewar Hidaya kenan yayin da duk suka kafeta da na mujiya suna jiran jin ta bakinta, kafin ta kai ga cewa wani abu Karimah ta zo wajen tana faɗin.
“Ku kuma nan kuka jawo Uwargidan tamu ana can ana nemanta kun riƙe ta da surutunku ko?”
“Wanne surutu kuma? Kawai dai muna bata shawarar da zata fishsheta ne.”
Zainab ta faɗa suna masu miƙewa baki ɗayansu, kafin ta cigaba da faɗin.
“Idan kin nutsu sai ki neme ni a waya mukarashe zance, Hidaya muje daga ciki ko?”
Suka juya suna masu barin gurin, Karima ta dubi Sakinah da ke zaune har lokacin a wajen jikinta duk ya yi sanyi, Karima ta koma gun da suka ta shi ta zauna tare da dafa kafaɗar Sakinan tana faɗin.
“Babu fa wanda ya ke neman ki, kawai daman dan na raba ki da waɗannan baƙaƙen kunamun ne, ai na tsinkayo hirar da suke yi miki, to wallahi ko da wasa ka da ki kuskura ki ɗauki zancensu, tun wuri ma kisan amsar basu domin Hidaya da Zainab tuni sun gama ɓaci babu wanda bai sansu wajen bin bokaye ba dan ba zance malamai ba ni, ba zan hanaki zumunci da su ba amma baya-baya.”
“Insha Allah zan yi ƙoƙarin kiyayewa, ni ba ma zancen su ne damuwata ba wallahi, Kamal fa ya ƙi amincewa da batun da mukayi jiya.”
“Ai daman tun da na zo abin ya ke raina nasan ruwa ba ya tsami banza, jiya na sanarwa Jabeer ya ce zai same shi suyi magana ka da ki damu ranki dan Allah, yanzu dai tashi muje a fara shirin zuwa dinner nan.”
“Banjin zan iya zuwa fa Karima sai dai ku kuje kawai.”
“Tab…! Ai kuwa ba isa ba wallahi dole ki je, ƙin zuwanki ai samun wata dama ce agareta kuma sauran mutane zasu ɗauka kishi ya hanaki zuwa, dan Allah ka da ma ki fara wannan batun ta shi muje ciki, yanzu na ga shigowar Aminan Ummanki fa su Hajiya Marka.”
A tare suka miƙe baki ɗayansu suka koma cikin jama’a domin gaisawa da mutane.
*****
Meenah event center da ke Sharaɗa nan Hajiya Shema’u ta kama domin yin ƙayatacciyar dinner ta musamman ita da gwarzon nata Kamal, wajen sosai ya ƙayatu ainun, kallo ɗaya zaka yi wajen ka aiyana mamakin irin dukiyar da aka ɓarnatar a wajen cikin ranka.
Amarya duk da kasancewarta babbar mace ba ƙaramin kyau suka zuba ita da angon nata cikin kayansu kala ɗaya ba, ita farin material ɗan ubansu wanda ya sha adon stone kota ita ɗinkin doguwar riga, sai dan kwalin data ɗaura da takalminta zuwa jaka duka silver ne, shi kuwa gogan tun daga hularsa har zuwa takalminsa farare ne tas, sosai ya yi kyau matuƙa kamar yanda Amaryar tasa ta yi.
Sai bayan sun shiga sun zauna sannan Uwar gida ta samu isowa ita da jama’arta, sosai ita ta fita kunya a wannan wajen, sabida shigowarta ce ta yi sanadiyyar da kallo ya koma sama, domin leshi da ke jikinta da ɗinkin kansa yafi na maryar tsada da kyau da komi itama kuma komai farin ne ta sanya hatta jaka zuwa takalmi da sarƙarta duk silver ne, sai ta zama tamkar ita ce amaryar ma, domin yanayin jikinta da komai tafi kama da amaryar.
Duk wannan aikin Yayanta ne da kuma Karima, su ne su ke ƙoƙarin ganin sun fidda ta kunya, Yayanta duk da yana wata uwa duniya amma bai barta ta yi kuka ba, a kullum ƙoƙarinsa ganin ya faranta ranta ko yaya ne, musamman da maganar auren Kamal ta ɓulla sai ya ji baki ɗaya tausayin ƙannen nasa ya ƙara tasiri a cikin ransa ainun.
Tuni guri ya kaure da kaɗe-kaɗe gefe guda kuma anata ciye-ciye ƙawayen Hajiya Shema’u tuni suka shige fili suna ɓarin nerori, suma dangin Sakinah da ƙawayenta ba’a bar su a baya ba domin tuni suma suka ɓalle bakunan jakunkunansu ko wacce da ga cikinsu ƙoƙari ta ke ta fidda Sakinah kunya a idon sakarkarun Aminan Hajiya Shema’u kamar yanda suke fadi.
Mamaki bai ƙarewa Ƙawayen Hajiya Shema’u ba sai da aka kira Uwar gida ta fito fili ta yi liƙi, nan ta ke Karimah ta sanya mata bandir na ‘yan dubu cikin jakarta ta ce ta je ta liƙa, babu musu ta shiga fili ta fara zubawa Ango da Amarya liƙi, shi kanshi Kamal mamakine fal ƙasan ƙalbinsa na yanda aka yi Sakinah ta samu kuɗi haka, amma kuma ba shi da mai ba shi amsa a wannan lokaci hakan ne ya sanya shi zuge bakinsa ya zuba mata na mujiya.
Ƙarfe goma da wani abu su Sakinah suka dawo gida, can suka baro amare waisu ba lokacin zasu ta shi ba, domin sai a lokacin ma su bikin nasu ya fara, Sakinah kuwa ta ce gida zasu tafi tuni motocin abokan ango suka kawo su gida suka koma.
Bayan sun dawo gida kai tsaye rage kayan jikunansu suka yi tare da nufar banɗaki domin watsa ruwa.
Sai bayan sun nutsu Sakinah ta dubi Karima da faɗin.
“Karima wai duk yaushe kika yi waɗannan hidindimun haka?”
Karima da ke danna wayarta da ke riƙe a hannunta ba tare da ta dubeta ba ta jefa mata tambaya itama ma.
“Hidindimun me fa?”
Sakinah ta ja gajeren tsaki, kafin ta warce wayar da ke hannun Karima tana faɗin.
“Kina wannan aikin ta ya za ki fahimci zancena, ina maki batun kayan da kika bani na sanya da kuma kuɗin liƙi mana, kawai fa shiru na yi miki saboda mutane.”
Karima ta yi gajeriyar dariya kafin ta ce.
“Daman nasan magana ce fal cikin ranki, to kwantar da hankalinki, ni kai ɗinki da siyowa ne aiki na amma kuɗi sun iso ne daga Yaya Jaheed.”
“Ya turo miki babu ko sanarwa?”
“E mana, kinsan Yaya Jaheed akwai bazata ta musamman.”
Sakinah ta yi ajiyar zuciya mai sauti kafin ta cigaba da fadin.
“Ai babu abin da zancewa Yaya sai addu’a a kullum, domin ya yi min dukkan abin da iyaye za su yi wa ‘yayansu, kema ba ni da abin gode miki wanda ya wuce addu’a Karima Ubangiji Allah ya baku zuri’a ta gari kuma wadanda zasu kyautata muku a duk yanayin da kuka kasance.”
“Amin amin, ke ki bar godiyar nan haka, ke halinki kenan idan kika fara godiya tamkar wata tsohuwa shiyasa Ya Jaheed ya ce ba ya so ki sani, shi bai son godiyar nan taki jin kunya kike sanya shi sai ya ji kamar ma kyautar ta yi kaɗan.”
Dariya suka sanya yayin da Sakinah ta kai karshen dariyarta da faɗin.
“Ai ni Yaya Jaheed yana bani mamaki wallahi, shi dai kunyarsa ba du mace ba, ina ga fa shiyasa har yanzu bai tsayar da mata ba, domin shi ba ya iya kallon idon mace ko wacece kuwa, ni na rasa irin kunyan nan Wallahi.”
“Kin san zuwan da ya yi na karshen nan bayan bikina da ya zo Umma ta ce masa ya je yaga ‘yar gidan Kawu Lawal, bayan ya dawo Umma ta ke tambayarsa kaga yarinyar kuwa ta yi maka? Buɗar bakin shi wallahi ko kallonta bai iya yi ba, asalima ba ba zai iya cewa ga kamanninta ba.”
Nan ma dariyar suka sanya, Karima ta ce.
“Ai ni kam naga ranar da Ya Jaheed zai ce yau ga matar da zai aura, ni fa inaga sai dai a yi masa auren haɗi.”
“Wallahi kuwa haka ma Umma ta ce tana ga idan ya dawo hakan zata yi masa, ta gaji da zaman tuzurancin Ya Jaheed, ni dai na ce mata ta yi haƙuri ta barshi ya zaɓo mana da kanshi.”
“Tab…! Ai kuwa banjin zan iya Allah ina ga ko Umma rabon da ya sake haɗa ido da ita tun yana yaro, ko ni nan sai dai mu yi hira a waya fa, idan Umma na yi masa zancen aure inda kika san mace kansa ya ke sanyawa cikin cinyotinsa ko kuma ya ta shi da gudu ya fi ce wai kunya.”
Suka kwashe dariya, Karima ta ce.
“Ya Jaheed manya ni dai zan so ganin matarsa wallahi, Allah dai ya zaɓa masa mace ta gari wacce tasan abin da ta ke yi, ta Kuma fahimci halinsa, amma kuma duk macen da ta kasance matar Ya Jaheed ta ji daɗinta wallahi, sosai zan yi mata murna domin Ya Jaheed namiji ne da babu macen da ba zata so shi ba, ko dan halayensa ka ɗai ya isa a so shi Sakinah.”
“Amin Amin addu’ar da muke yi masa kenan kullum.”
Nan suka cigaba da hirarsu kasancewar a nan Karima zata kwana, Sakina kuwa ba ta tunanin dawowar Kamal gidan a yanzu shiyasa suka shige ɗakin Sakinan suna tattaunawa, da ya ke dukkan baƙi sun nufi gida babu wanda ya ce zai kwana, Sajidah kuwa na ɗakin Farida ta ce yau nan zata kwana susha hira suma.