Tafiyarsu babu daɗewa Nasir Nasar ya zo hannayensa ɗauke da manyan ledodi, fuskarsa ɗauke da shimfiɗaɗɗen murmushi.
Kai tsaye ɗakin ya shige jin bai ganta a falo ba, ya shiga ɗakin, da mamakinsa ya ganta zaune a gaban gado tana murza ɗaurin ɗankwali ta saka wani material fari mai feshin jajayen fulawa.
Hannayensa ya harɗe a ƙirjinsa yana ƙiyasta adadin haɗuwar da Hafsa ke da shi, yakan ji mamaki idan aka lissafa masa adadin auren da ta yi da kuma yaran da take da su.
"Kana tsaye ne kana yabon kyauna. Madadin ka zo ka. . .
😂😂😂😂😂 gaskia wananan kaza da tsada take…. Kila bakin gobe ba bakin rashin kunya