Skip to content
Part 33 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Tafiyarsu babu daɗewa Nasir Nasar ya zo hannayensa ɗauke da manyan ledodi, fuskarsa ɗauke da shimfiɗaɗɗen murmushi.

Kai tsaye ɗakin ya shige jin bai ganta a falo ba, ya shiga ɗakin, da mamakinsa ya ganta zaune a gaban gado tana murza ɗaurin ɗankwali ta saka wani material fari mai feshin jajayen fulawa.

Hannayensa ya harɗe a ƙirjinsa yana ƙiyasta adadin haɗuwar da Hafsa ke da shi, yakan ji mamaki idan aka lissafa masa adadin auren da ta yi da kuma yaran da take da su.

“Kana tsaye ne kana yabon kyauna. Madadin ka zo ka faɗa min yadda na yi kyan kai tsaye.” Maganarta ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula.

Hakan kuma ya sa ya taka ƙafafuwansa ya tsaya a bayanta yana kallonta ta cikin madubin, da sauƙo da fuskarsa daidai tata, suna kallon fuskokinsu a cikin madubin.

“Kyau da kanki idan ya kalle ki zai falfala da gudu ne Hafsa. Shi yasa a faɗe shi a kanki kamar ya yi kaɗan, balle kuma a yanzu da ya haɗu da kyakkyawar fuskar Nasir Nasar, nasan abin zai zarta kalaman faɗa a baka.” Ya yi maganar yana kanne idanuwansa ɗaya, da kuma kai bakinsa saitin kumatunta ya sumbace ta.

Murmushi ta yi tana girgiza kanta. Tana son faɗar wani abu, wani abu mai girma amma kuma bata san ta ina zata fara ba, za dai ta yi shiru ne har zuwa lokacin da buƙatar hakan ta taso.

“Ga kazar amarcinki nan na kawo miki.” Ya yi maganar yana nuni da hannunsa ga inda ya ajiye kajin.

Kai ta gyaɗa tana miƙewa a tsaye a kan ƙafafuwanta, kafin ta juyo ta fiskance shi tana kallonsa.

Sai kuma ta sosa girarta guda ɗaya tana faɗaɗa murmushi a kan fuskarta.

“Ka yi ƙoƙari sosai.” Ta faɗa tana giftawa ta gabansa, wadda ƙamshin turaren da ke jikinta ya ƙara hautsina nutsuwarsa, har sai da ya kamota ya dawo da ita.

“Ina ganin ya kamata a haƙura da cin kazar nan har sai an kula da Nasir.” Ya yi maganar yana cusa kansa tsakanin wuyanta da shaƙar ƙamshin turarenta.

“Ka taɓa ganin inda aka bar farilla a ka yi Nafila?” Ta zame jikinta daga nasa tana ƙara rangwada jikinta da salon tafiyarta na shu’umanci.

Kamar ba Nasir Nasar ba haka ya saki baki yana kallonta har ta zauna a kan kafet ɗin da ke ɗakin ta fara buɗe ledojin da tun kafin ta buɗe su ƙamshin kazar ya cika hancinta.

Ƙananun idanuwanta ta lumshe tana lasar laɓɓanta da harshenta “Ƙamshi mai daɗi.

Kasan a komai nawa ina martaba kaza musamman ta amarcina da nasan ko ban cita ba sai an fanshe a kaina. Shi yasa bana mata cin wasa.” Ta yi maganar tana kai cinyar kazar bakinta ta yaga tana lumshe ido da taunawa.

Shi kam kallonta yake zuwa yanzu ya fara sanin wacece Hafsa, mace ce da bata san mene ne kunya ko baƙunta a al’amarinta ba. Duk abin da ke zuciyarta tana fitowa ne ta faɗe shi kai tsaye.

Matsowa ya yi shima ya zauna a kan kafet ɗin yana kallonta “Ba zaki min ta yi ba ne?”

A lokacin ta gama da cinyoyin kazar da fiffikensu, ta fara yagar gangar jikinta.

“Wannan ai duk tawa ce, ka duba idan ka zo da wata sai ka ci.”

“Kamar ya?”

Ya yi maganar a mamakance, hakan yasa ta ɗago ta kalle shi “Ina nufin idan ka shigo da biyu ɗakin nan, to zaka ci ɗaya ne nima na ci. Idan kuma ɗaya ka shigo da ita, hakan na nufin tawa ce ni ɗaya.” Ta kai ƙarshen maganar da ɓalle murfin yought tana kaiwa bakinta.

Shafa kansa ya yi yana tauna laɓɓansa da yake jin su a bushe, wadda kuma zirga-zirgar aure ta hana shi samun nutsuwar ya ci wani abin kirki na azo a gani. 

Daga nan ya shiga buɗe ledar yana ganin babu komai a cikinta sai ƙasusuwan da Hafsa ta yiwa rugu-rugu kamar kura ta samu nama.

“Ina ɗayar da ke ciki?” Ya jefa maganar yana kallon ledar, dan ya san tabbas kaji uku ya siyo ɗaya a leda daban biyu a leda daban.

Ya miƙawa Uwargidansa leda ɗaya sannan ya shigo musu da ɗayar.

Sai dai kuma baiga komai ba bayan ƙasusuwa a gabansa “Kina nufin duk ke ɗaya kika ci kaji har guda biyu manya?” Ya yi maganar da tsananin mamaki.

Sai dai ga ƙarin mamakinsa yaga Hafsa ta miƙe tsaye “Banda abinka Nasir kai da zaka  ci mutum mene ne abin damuwa a kan batun kaza?

Ka sha yought ka ɗauro alola mu yi sallar amare ka fanshe kazarka kawai.” Daga haka ta shige toilet tana banke ƙofar da ya ke binta da sakeken baki yana ƙara mamakinta.

Kafin kuma ya yi murmushi ya ciza bakinsa “Zata ga kuwa fanshe kaza. Zan nuna mata maza ma suna suka tara, bata san wane ne Nasir ba.” Ya yi maganar yana ɗaukan jarkar yought ɗin yana tuttulawa a cikinsa.

Sai da ya shanye sannan Hafsa ta fito fuskarta ɗauke da ruwa wadda ke bashi tabbacin alola ta ɗauro itama.

Dan haka shima ya ajiye gorar ya shiga toilet ɗin, kafin ya dawo ta gyara wajen ta shimfiɗa musu dardumar yin sallah.

Shi ya ja su raka’a biyu, bayan sun idar ya ke ƙoƙarin tashi tsaye, hakan yasa Hafsa ta zaunar da shi ta ɗauki hannunsa na dama ta ɗora a kanta “Ka roƙi alkhairina a zaman aurenmu daga wajen Allah, ka kuma nemi tsari daga sharrin da ke tare da ni.” Ta yi maganar tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta.

Ganin kallon da yake mata na rashin fahimtar maganarta da inda ta dosa yasa ta fahimci ta auri miji da ke zaune zero ne a kan addini.

“Zan karanto ma addu’ar sai kana faɗa. Wannan sunnah ce ta aure.” Kai ya gyaɗa mata.

Ta shiga karantowa yana nanatawa har suka gama.

Daga haka suka miƙe gaba ɗaya, shi ya fita zuwa sashensa yane ce mata yana zuwa. Ita kuma ta shiga toilet ta wanke bakinta kana ta sake yin wanka, da ra fito mai da kuma turare, sai wata rigar baccin da za a kirata da akwai da babu, domin babu wani abu da ta ɓoye a jikinta, asalima iyakarta rabin cinyarta bata saƙƙo mata ba.

Ta ƙara feshe jikinta da turare mai sanyin ƙamshi, ita da kanta tasan ta fitinu da duk wani salon da zata haukatar da Nasir a yau ɗin.

Ƙofar da aka turo yasa ta ɗago kanta daga kallon madubin da take da juya jikinta.

Tun da ya shigo ɗakin ƙamshin da ya ke ji ya fara haukata shi, har kuma zuwa lokacin da ya ɗora idanuwansa a kan Hafsa. Ji ya yi notinan kansa da suke sarrafa rayuwarsa sun harba.

Musamman maganin da ya sha na ƙarin ƙarfin maza kafin ya shigo gidan ya taimaka wajen ƙara hautsina rayuwarsa.

Bai tsaya komai da tunanin komaiba ya afka mata kamar mayunwacin zaki. Haukansa ya ƙara ta’azzara ne a lokacin da hancinsa ya sake shaƙo masa ni’imtaccen ƙamshin da ke jikinta wadda zai iya cewa bai taɓa jin ƙamshi kamarsa ba a iya tsawon rayuwarsa.

“Ya Allah ! Hafsat wannan ƙamshi zai iya haukata ni da yawa.” Ya yi maganar yana cusa kansa a tsakani wuyanta. Har yaga abin ba zai masa ba ya ɗagata ya kwantar a kan gadon, ya kashe wutar ɗakin.

Hafsa kam jin kanta take asama ganin yadda Nasir ya haukace a kanta, ya zame mata kamar wani kare sai bi yake yana shinshinata saƙo da saƙo. Tana kuma ƙara haukata shi ta hanyar gwada masa ƙwarewarta a fannin.

Hakan yasa ya cusa kansa ba tare da tunanin ya bi a hankali da ita ba, a tunaninsa ai bazawara ce uwar wane kakar wane.

Wadda kuma a ta wajen Hafsat an sha gyara har da ɗinki irin na zawarawan da suke son mallake mazajensu, banda ƙarin kayan ni’imar da ta sha na tsuketa. Gashi dama halittarta irin mai tsukewar nan ce da in aka daɗe take haɗewa.

Bata san lokacin da ta kwantsama ihu ba, sai dai wai a banza an mintsini kunkuru a baya. Domin ihun da ta yi sai ya ji kamar tana masa busa ne a kunnuwansa, busar da take kama da gangin na ƙara azama gare shi.

Tun tana ƙoƙarin ƙwace kanta da daidaita numfashinta, har abin ya gagari ƙarfinta, tana lissafin adadin mintinan da ya kamata ace ya samu gamsuwa ya kawo ya barta. Sai taga lissafin ya haura tunaninta.

A gogewarta da mu’amala da mazan aure har huɗu tasan iyakarsu basa wuce mintuna goma. Garama Sayyadi da ya kasance na musamman a duniyarta da yake kaiwa mintina ashirin a kanta. Idan suka huta ya ƙara dan ƙorafin da take masa.

Sai ga Nasir ya fatattaketa ya watsar da komai na kuzarin da take da shi. Lissafinta ya tsaya cak a lokacin da ta fara jin bakinta ya bushe kamar ba a taɓa halittar wani abu mai kama da yawu a cikinsa ba.

Numfashinta ya ɗauke cak ta daina jin komai da sautin komai, tana fatan rayuwa ta sake haska mata a karo na biyu domin ta waiwayi bayanta….

*****

Hhhh da alamu Hafsatu ta ci kaza mai tsada fa. Lolz. Idan na samu cmnts da yawa zan na muku posting kullum dan naga kamar bakwa maraba da dawowata.

Oum Nass

<< Jini Ya Tsaga 32Jini Ya Tsaga 34 >>

1 thought on “Jini Ya Tsaga 33”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.