Skip to content
Part 34 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Idanuwanta ba su buɗe ba har sai da hasken rana ya hudo ta windon da ke ɗakin ya haske idanuwanta.

Ta fara buɗe idanuwanta da take jin nauyinsu da kuma gajiyawar da suka yi. Daga kwancen da take tana iya auna adadin kassarewar da gaɓɓoɓin jikinta suka yi da mafi wahalar kasala da kuma gajiya. Ƙasanta kuwa kamar an baɗa mata barkono an bishi da attaruhu an zazzaga mata.

Yunƙurin tashi take ganin agogon bango na biga ƙararrawar ƙarfe tara na safiya. ‘Wata irin lalacewa haka na yi? Wadda ko a daren aurena na farko ban ji lalacewa da wahala haka ba?’ Ta yi maganar a ƙasan zuciyarta.

Domin idan har ba mantawa ta yi ba da asuba Sayyadi ya zo ya tasheta, ya na kuma taimaka mata a kan ta shiga ta yi wanka, tana iya tuna masifar da ta zazzaga masa da cewar ya raraketa yana takura mata a kan ta zo ta yi sallah.

Sai gashi yanzu mijin da ya raraketa da gasken gaske ya tsallaketa ya fice. Ta tabbata a yanzu ne take da buƙatar a taimaka mata, musamman idan aka yi duba da kuskuren da ta aikata na zuwa a ɗinketa da matsetan da a ka yi.

Ƙofar da aka shigo a ka turo ne, yasa ta mayar da kallonta ga mai ikon shigowa ɗakin. Ga mamakinta Nasir Nasar ne shar da shi cikin adon dakakkiyar shadda kalar ruwan zuma, ya kafa hula a kansa mai ratsin adon shaddar. Sai takalmin da ke yana daidaita agogo a hannunsa da kallon lokaci, shima dai agogon kalar kayansa ne.

Baki ta hangame ganin yadda fuskarsa ke fita da sheƙi da annashuwa. Sai dai kuma ya tsaya tiris a jikin ƙofar yana yamutsa fuskarsa da faffaɗan bakinsa, miƙeƙƙen karan hancinsa na tattarrewa a waje ɗaya.

“Wai har yanzu ba ki tashi kin gyara jikin ki ba? Wane irin abu ne amarya guda tana kwance har ƙarfe tara an aiko abinci baki miƙe ba.”

Idanuwanta ta ƙanƙance ciki a ranta tana kokawa da kalmomin da suka cancanci amsar da zata bawa Nasir Nasar wadda zata yi daidai da shi.

Sai dai duk maganar da ta ƙiyasta sai taga ai ba zata huce ba.

“Da Allah ki tashi ki tsaftace wajen nan, haba idan wani ya zo kuma ai sai ki bada ni. Ke ba wai sabuwar budurwa ba balle kice kina jiran a tallafa miki ko a taimaka miki, abu ne da kika daɗe da saninsa da kuma wuce ajin koyarwa a kansa.”

“Kan Uba!” Ta yi maganar a ƙasan zuciyarta, tana tariyo kalar tijarar da zata masa amma kuma ba wai a yanzu ne zata bashi ba.

Ta san dai ƙaryar bariki a ce ya fatattaketa bai ji mamakin yadda ya sameta ba, musamman idan ta auna maganarsa da kuma tunaninta a waje ɗaya.

Tana jin raɗaɗi da zafin da jikinta ke yi mata, a lokacin da ta yunƙura dan ta miƙe zaune, sautin ƙasusuwan jikinta suka fara kiran Ƙassshh… ƙasshh… Ɓalll.. Kamar ana haɗa ƙashin da ya karye a waje ɗaya.

Amma hakan bai daɗeta da ƙasa ba, ta miƙe da dukkanin wani kuzarin da ya rage mata a jikinta, sai dai kafin ƙafafuwanta su daidaita ta ji ɗakin ya fara juya mata yana mata yawo, dole sai da ta dafe bango tana lumshe idanuwanta.

Shi kam mutuwar tsaye ya yi, yana haɗiyar wani yawu, a lokacin da ta ganta a miƙe ƙyam a tsaye babu kaya a jikinta. Yana ganin yadda mamanta suke a miƙe a cike da su kamar za su fasa ƙirjin nata.

Shifa mamakinsa ya yi yawa, tun a jiyan da ya kasance da Hafsa yake ɗora zararrukan tambaya da tunani a kan kasancewarta bazawarar da ta auri maza har huɗu, take da jimillar yara har guda biyar.

Da ace ba ita ta faɗa masa da kanta ba, tabbas zai ƙaryata batun haihuwarta da auren maxan da ta yi, yana kuma ƙara ganin wautarsu na rabu da mace kamar Hafsan da suka yi.

Takowa ya yi yana lasar laɓɓan bakinsa da nufar inda ta ke, yana ƙoƙarin ya kamata dan ya mayar da abin da ya taso masa na ganinta da ya yi a hakan.

Sai dai ganin kallon da ta masa da kuma shigar da idanuwanta da ta yi a kan nasa, ya ji wani rauni da kasala ta ƙara kama shi.

Ƙarasa ta yi kusa da shi tana goga masa ƙirjinta a gabansa, tana faralla idanuwanta sama zuwa ƙasa “Barka da safiya Angon Hafsa.” Ta faɗa a lokacin da take faɗaɗa murmushi a fuskarta da goga hancinta a kan wuyansa.

Hakan yasa kamar an kunno shi, yaji kansa ya harba da wani irin abu har zuwa ƙafafuwansa.

Rarimota ya yi da niyar kaita gado, sai dai cikin dakiya ta tattara duk wani kuzarinta ta tsaya ƙam a kan ƙafafuwanta, tana taro shi da riƙe kansa a tafukan hannunta.

“Haba! Ka silace mana, wannan zafin nama haka kamar baka taɓa isa waje irin wannan ba? Naga kaima ba wai farko bane balle kace ɗokin fara shiga ya zautar da kai da sake maimaici da tsakar rana, ga amaryar da ta kasa tashi ta gyara jikinta.”

Ta ƙare maganar tana hura masa iska a kunnensa.

Jikinsa ya  ƙara yin luƙus duk da ya fahimci maganarta, amma shi ba wai ta dame shi ba ne, so ya ke ya sake kai wa duniyar daɗin da ya je a daren jiyan.

Shafa ƙirjinsa ta yi tana ƙara goga mata jikinsa “Jiya ka nuna ƙwarewarka ta gaske. Ka bari yau ka ga bajinta ta.” Ta yi maganar tana ɓalla maɓallan rigarsa, wadda hakan yasa ta ji ya yi amanna daɗin da zai iya ji a yau ɗin ya ninka wadda ya ji a daren jiya.

Tura shi ta yi baya ya faɗa kan gadon yayin da ta biyo shi, ta ci gaba da shafa shin, wadda ya kai ƙarshe da son isar inda ya ke so, numfashinsa ya fara yi sama da ƙasa.

Wadda yasa ta tauna lifs ɗinta tana murmushi.

A lokacin da yake tunanin komai ta zo masa, sai ya ji cak da bugowar ƙofar banɗakin.

“Zan tsaftace jikina ɗan saurayi, yanzu lokacin wanka ne da kwalliya da cin abinci.” Ya ji sautin maganarta da ta zama kamar garwashi a kunnensa.

Yana kallon yadda gabansa ke harbawa kamar zai tsinke daga inda yake, numfashinsa na kaiwa da kawowa. Mararsa na ɗaurewa tamau kamar zata fashe saboda fitina, musamman da sinadarin maganin da ya sha bai sake shi gaba ɗaya ba, duk da daren jiya ya raba shi ne yana wala wala a kan Hafsan.

Ba’a taɓa kunno shi irin haka ba a rayuwarsa, ya sani.

Da ƙyar ya miƙe tsaye yana dafe da mararsa ya fara biga ƙofar banɗakin “Hafsa ki fito dan Allah. Kin riga da kin kunno ni, kin kuma san ba zan iya ba ne.” Ya yi maganar da muryar da ke fita daga maƙoshinsa.

“Haba dai kai da ba ɗan koyo ba yaushe zaka tsaya a kunno ko. Gida biyu ai maganin gobara ne, na yafe ka kaiwa uwargidan ka boom ɗin masifar da ka kwankwaɗo.

Ni dai musulma ce ko sallar asuba baka tashe ni ba, ka tsallake ni ka tafi, kuma yanzu ina tsaftace jikina da gasa ƙasusuwan da ka so kashe min su ne. Ga fitinanniyar yunwar da fitinarka ta gama haddasa min ita.”

Ta gama maganar tana ƙara gudun ruwan da ke zuba a kwamin wankan.

Ƙofar ya fara bibbigawa da ƙarfinsa yana jin kamar ya cireta dan haushi “Idan na kamaki zan miki ba daɗi ne ai.”

“Karka damu ai na shirya maka angona.” Ta yi maganar tana yin luff a cikin ruwan.

Shi kam a fusace ya yi waje yana nufar sashen Zahra uwargidansa, sai dai ga mamakinsa ya sameta da mutane da yawa ƴan taya murna, mafi yawa a ciki ƴan uwansa ne.

Bai bari sun ganshi ba, ya juya ya nufi sashensa, ya haɗa ruwan lipton da lemon tsami wadda dama baya rabuwa da shi.

Shi kansa yasan shi fitinanne ne, sai kuma ya haɗa fitinar tasa ta hanyar bankawa kansa magani.

Yau kuma Hafsa ta kai shi ƙololuwa a tado masa da fitinar, ya kuma barshi kamar gantalale.

Ruwan lipton ɗin da ya sha bai masa magani ba, hakan yasa a haukace ya sake dawowa sashen Hafsa ya tararta zaune a kan abin sallah ta idar, tana jingine da kanta a kan abin sallah.

Kallon da yake mata sai da yasa gabanta ta buga da ƙarfi, amma sanin idan ta fito da tsoronta kamar ta bashi dama ne.

Nufota ya yi “Kin san nafi ƙarfin ki kunno ni kuma ki bar ni. Idan ba ki san wane ne Nasir Nasar ba, yau zan nuna miki ko waye ne.”

Ya nufeta da ƙarfinsa yana fincike hijabin da ke jikinta.

“Ikon Allah! Abin har da fashi kuma Malam Nasir?” Ta yi maganar da sautin shu’umancinta, sai dai da alamu bata san ya fita a hayyacinsa ba.

So yake ya bata wahalar da zata daɗe tana nanata shi, ganin dai idan ta tsaya tsaf zai haɗe gabanta da bayanta, yasa ta fidda numfashi tana shafa shi da ƙoƙarin ruɗar da tunaninsa.

“Wannan abin daɗi ai ba sai an haɗa da yaƙi ba. Bari na taimaka ma.” Ta yi maganar tana gyara masa kwanciyarsa.

A matsayinsa na sokon da ke yunwace da kaiwa inda yake son kai, ya sake bada amanna akan zata taimaka masa ne, sai dai ya sake kuskurowa.

Domin ciɗak ta gudu a ɗakin ta rufe ƙofar da mukulli.

“Wallahi ba zaka kashe ni da raina ba Nasir!” Ta yi maganar tana dafe ƙirjinta da maida numfashinta.

Ya yin da shi kuma yake buga mata ƙofar da ƙarfi yana cewa ta zo ta buɗe masa.

“Wato ka haukata mata da yawa, ka farke su son ransu, abin da baka sani ba, ni kaina fitina ce Nasir.” Ta yi maganar tana buɗe manyan kulolin abincin da Zahra ta aiko mata da shi, tana sambaɗa mata albarka da yadda take da tsarkakkyakkiyar zuciya…

*****

Tofah! Amarya na gudun ango. Kuna ganin zata tsira kuwa?

Oum-Nass

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jini Ya Tsaga 33Jini Ya Tsaga 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×