Farko
“Kaico da kai wannan mutum la’ananne tsinanne, yadda ka ɓata rayuwar yarinyar nan ina roƙon Ubangiji Ya ɓata dukkan lamuranka, ya rushe duk wata walwala da farin cikinka, azzalumi.”
Dattijuwa ce ‘yar kimanin shekaru hamsin da biyu zuwa da biyar take furucin, muryarta cike da amon da ke bayyana tsananin ƙunar da zuciyarta ke yi, kai ka ce mutumin ne tsaye a gabanta, sai dai a zahiri ba ta san ma a duniyar da za ta same shi ba.
Matashiyar budurwa Asma’u mai shekarun haihuwa goma sha biyar ta ɗago daga durƙuson da ta yi, idanunta jajir saboda tsananin kukan da ta share tsayin sa’o’i tana yi, ta dubi dattijuwar da ke tsaye a kanta, a karon da dukkan su ba za su iya lissafa ko na nawa ba ne sai ga hawaye suna rigegeniyar sauka kan kuncinta.
Tsananin tausayinta ne ya ci gaba da ratsa zuciyar mahaifiyar ta ta yadda cikin ƙanƙanin lokaci da faruwar abin duk ta bi ta fige ta lalace tamkar ba Asma’unta mai yawan kuzari, fara’a da walwala ba, a yanzu ƙunci yana nema ya ɗai-ɗaita rayuwarta, don haka ita ma sai ga hawayen suna fita daga idanunta.
“Ki yi haƙuri Asma’u, Allah ne kaɗai zai mana sakayya tsakaninmu da mutumin nan.”
A nutse ta sunkuyo gare ta tare ta kamo kafaɗunta a ƙoƙarinta na ganin ta raba ta da wajen. “Tashi mu je ɗaki tunda aman ya tsaya kin ji?”
Kamar Asma’u ba za ta iya tashi ba saboda yadda ta bi ta galabaita amma da ta tuna cewa wani na iya shigowa gidan ya riske su a halin da suke, dole ta ƙoƙarta ta miƙe da taimakon Innar, ta sada ta da tsukakken ɗakin bukkarsu.
Inna ta zaunar da ita a kan tabarma, ta janyo filo ta jinginar da ita tana ci gaba da jera mata sannu cikin tsananin nuna alhini da tausayawa, sannan ta samu guri ita ma ta zauna gefenta.
A matsayinta na uwa ba ta saurara ba ta ci gaba da kwantar mata da hankali tare da ƙoƙarin ganin ta samar musu mafita kan lamarin, fatanta ɗaya kada a samu ko da qarin mutum xaya da zai san AN YI WA ƊIYARTA ASMA’U FYAƊE HAR TA SAMU CIKI.
Babban abin da ke qara tayar da hankalinta bai wuce tunanin ta yadda za ta fuskanci mutanen xan ƙaramin ƙauyen da suke rayuwa ba.
Asma’u ba za ta taɓa kuɓuta daga mummunan zargin karuwanci daga mutanen ƙauyen Somayi ba, idan kuwa ta bayyana gaskiyar abin da ya faru babu mai ƙara duban ɗiyarta da nufin aure har duniya ta tashi.
Inna Hauwa ta sa havar zaninta tana share ƙwallar da ta taru ta cika mata idanu.
“Ni dai ina ganin babu mafitar da ta wuce mu tattara mu bar ƙauyen nan tun kafin mu fuskanci wulaƙanci da cin zarafin da ke jiran mu muddin aka san kina da cikin nan, na san kina sane da abin da ya faru da Habi da mahaifiyarta kan shegen da ta ɗauko ko?”
“Inna amma ni ai ba da son raina komai ya faru ba kamar Habi da ita dama can lalatacciya ce dubunta ta cika.”
A karon farko Asma’u ta yi magana cikin gursheƙen kuka da tsananin takaicin jahilcin da ke dabaibaye da mutanen qauyensu, tana jin kaf faɗin duniya babu inda ake ƙyamar macen da ta san namiji ba ta hanyar aure ba ake kuma hukunta ta mummunan hukunci kamar karkararsu.
Inna Hauwa ta dube ta bayan ta yi shiru na xan lokaci, kana ta ce “Asma’u abin da nake so ki fahimta; su ba za su fahimci haka ba, ba za su iya bambance ƙaddararki da ta Habi ba, duk ɗaya za su xauke ku.”
“Ni kam Inna a kan mu bar ƙauyen nan gara a faɗa wa Maigari abin da ya faru, wallahi na gwammace in zauna babu aure har ƙarshen rayuwata.”
“Idan za mu faɗa wa duniya tun farko ya kamata a ce mun faɗa, ba yanzu da cikin nan ya fito ba, lokaci ya gama ƙure mana Asma’u, ba mu da wata mafita da ta wuce ƙaura daga Somayi.”
Asma’u ta sa kuka, babu abin da take jin takaici irin rabuwa da ƙauyen da aka haife ta, gidansu, ƙawayenta da wasannin da ke saka ta nishaɗi koyaushe a dandali, ta yaya za ta iya rayuwa ba tare da waɗannan abubuwan ba?
Kamar Inna ta shiga zuciyarta ta ga abin da take tunani ta ce, “Ki bar tuna komai face irin wulaƙancin da za mu fuskanta Asma’u. Wallahi ba na son zuwan wannan ranar, ranar da maƙiyanmu za su yi mana dariya musamman maneman auren da kika ƙi.”
Babu shakka zantukan Innarta gaskiya ne, akwai wata rana da ba za ta mance da ita ba…
Ranar da aka kore ta daga ƙauyen a kan gaskiyarta, amma ba ta tafi ba ta bayar da haƙuri aka bar ta ta zauna, sai gashi a yau za ta gudu da ƙafafunta.
Ranar ta samu saƙon Maigari ne a kan neman gaggawar da yake mata, lokacin da ta iso zaurensa kafatanin dattawan qauyen da wasu daga cikin matasa suna zaune wasu a tsaye, dukkan alamu kuma sun nuna saboda ita aka yi taron. Gabanta na faɗuwa da fargaba marar adadi ta yi zaman raƙuma inda Maigarin ya nuna mata da yatsarsa kanta a sunkuye.
“Nan da kike gani ƙarar ki aka kawo Asma’u. Da mahaifiyar taki zan tura a kira min, sai na ga gara ki zo da kanki.”
Jin cewa qararta aka kawo ya tayar mata da hankali don ba ƙaramin laifi mutum ke yi a kai shi gaban Maigari ba.
“Wato ɗan guntun karatun da kika yi gun mahaifinki kafin ya bar duniya har ya sa kin fara girman kai ko, kina ɗaukar kanki wata mai ilimin da babu kamarta cikin ƙauyen nan? An ce kin ce wai kiran Sallar da Ladan ya ke ba dai-dai ba ne, shi ma Liman akwai gyara cikin karatun Sallar sa.”
Sai yanzu ta gane dalilin kiran; wata rana ne Tabawa ta shigo gidansu daidai lokacin da Ladan ke kiran Sallah kasancewar masallacin manne yake da jikin gidan su, kamar ko wane lokaci ta saba jin katoɓarar Ladan, bisa tsautsayi ranar kawai ta yi maganar gaban Tabawa a ƙoƙarin son fahimtar da Tabawan yadda ake kiran Sallar, Tabawa ta kwantar da kai tana koyo, to ashe a ƙarƙashin zuciyarta akwai mugun abu.
Shiru Asma’u ta yi ta kasa cewa komai don ba ta da abin cewar tunda an riga an juya mata magana. Tana ji Waziri ya amshe.
“Ranka shi daɗe ni fa tunda uwata ta haife ni a garin nan ban tava ganin gidan da ake wa dokar da muka shimfiɗa karan tsaye ba irin gidan Malam Tanimu musamman bayan ransa.”
Maigari kuwa ya qara hasala don haka ya sake jefo mata kallon banza.
“Wannan kam ai mun jima da sani, Malam Tanimu bai bar baya mai kyau ba, ba a rufa sati ba a kawo ƙarar iyalinsa fadar nan ba, don ma dai ban fiye sauraron abin da ba shi da muhimmanci ba, duba dai yarinyar nan yadda ta murje ido fiƙi-fiƙi wai kaf mazan karkarar nan ba ta ga sa’an aurenta ba, idan ban manta ba har Muntari yaron wajena da Salele ɗan wajen sarkin noma sun nemi aurenta amma fafur ta ƙi, ni ban san me take nufi ba.”
“Waziri ya tari numfashinsa, “Me take nufi da ya wuce tsinannen girman kai da mugun hali da ta tsotsa a nono, in ba ka manta ba garin gabas aka auro uwarta.”
“To ai ko sai dai ta koma can tushen fitsara da rashin albarka ta zauna, mu a nan ba ma buƙatar ta, tunda ta ce jahilai muke ta bar mu da jahilcin ya kashe mu, kwanaki uku na ba ki Asma’u ki haɗa naki-ya-naki ki bar min ƙauyen nan.”
Ba korar ce ta baƙanta wa Asma’u rai ba, an jima ba a ci zarafinsu da mahaifiyarta irin ranar ba. Sannan ba ta san laifin me ta yi wa Waziri ba yake ta burin ya ga an cusguna mata.
Gargaɗin da Inna ta yi mata kan tofa wani abu da zai iya zama jayyaya tsakaninta da su ya sa ta ja bakinta ta yi shiru a wajen duk da irin suyar da ranta ke yi. Tana ji tana gani suka ƙare mata cin fuska tas! Musamman Waziri, sai ma ta ɗora da bayar da haƙuri tare da roqon Maigari ya yafe mata a bar ta ta zauna a ƙauyen da alƙawarin ba za ta sake wani abu makamancin wannan ba.
Muryar Inna ta dawo da ita daga duniyar tunaninta.
“Asma’u ki yi haƙuri da abin da ya same ki, haka nan Allah Ya rubuta miki, ni ina tare da ke.”
“Na sani Inna, idan duk duniya za a juyan baya ke ba za ki guje ni ba, ban damu ba kowa ma ya tsane ni, amma babu inda za mu je.”
“Ba zai yiwu ba Asma’u, muddin za ki zauna da cikin nan a jikinki har ki haife shi sai dai mu yi nesa da jama’a zuwa inda babu wanda ya san mu, bayan kin haihu sai mu san yadda za mu yi da ɗan ko ‘yar don ba zamu tava dawowa da abin da kika haifa ƙauyen nan ba.”
Asma’u ta fashe da kuka a can ƙarƙashin Zuciyarta tana Allah Ya isa ga mutumin da ya jefa su a wannan hali, wanda har yau ba su san ko waye ba, amma tana da tabbaci kan duk inda yake sai ya gamu da sakayyar Allah kan zaluncin da ya mata.
“Yanzu Inna idan muka bar ƙauyen nan ina za mu koma?”
Kafin ta amsa mata suka jiyo sallama a zaure alamun za a shigo, nan da nan su biyun suka fara rigegeniyar share hawayen da ke zubowa daga idanunsu.
Tabawa ce ta shigo idanunta a kan fuskokinsu, yanayinsu kaɗai ya gwada mata sun sha kuka sun gaji musamman Asma’u, don haka sai ta yi zargin wani abun marar daɗi suke ƙoƙarin ɓoye mata.
“Ma’u lafiyarki, me ya sami idanunki suka kaɗa suka yi jajir haka, kamar ma kuka kika yi ko?”
Ala-tilas Asma’u ta ƙirƙiri murmushin ƙarfin hali kana ta ce da ita, “Inna Tabawa kan abin da dai da aka saba ne, surutun da ake min kan fitar da miji a ƙauyen nan, ya ake so in yi? Ni fa wallahi Muntari ko Salele bana son ko guda cikin su?”
Sam Inna Hauwa ba ta yi mamakin ɓadda bamin da Asma’u ta yi wa Tabawa da matsalar da dama cikinta suke rayuwa tsawon lokaci ba kasancewarta yarinya mai hikimar gaske. Tabawan kuwa ta taɓe baki, dama dai ta san tatsuniyar gizo ba za ta wuce ƙoƙi ba.
“Hoɗijan! To ai ko kin san babu ta inda za ki samu sassauci matuƙar a kan wannan maganar ne, gaskiya ake faɗa miki, kin san da Malam Tanimu na raye babu yadda za a yi ya bar ki ki ganɗame a gabansa haka, ko ita Hauwa’un don ba ta san illar zamanki a gabanta a shekaru irin naki ba ne, baliga irin ki tubarkallah da ke kin kai munzalin aje ‘ya’ya uku fa, ki duba ki ga sa’anninki mana da aka aurar a karkarar nan, ai shan ruwan gidan nan naku ma ya kusa haramta.”
Shiru Asma’u ta yi, maganganun Tabawa sai suka ankarar da ita wani abu da ba ta tava kawo shi ko da gefen tunaninta ba, tabbas da a ce tana da masaniya kan gobenta, ma’ana ta san irin wannan hautsinannen lokacin zai zo musu da ta yarda ta auri duk namijin da ya zo neman aurenta ko da ba ta son sa.
Tabawa ta qaraci surutunta ta fice daga gidan. Tabbas kuma wannan ɗan abun da ta gani sai yaje kunnen Maigari, don duk abin da Tabawa ta ji ko ta gani tamkar mijinta Malam Iro ya ji ne, shi kuwa jinsa jin kowa da kowa da ke ƙauyen ne, har ma da maƙotan ƙauyuka.
Babu ɓata lokaci Inna ta miqe ta fara haɗa musu kayan su cikin ghana must go.
“Dakata Inna don Allah.” Asma’u ta faɗa sa’ar da ta fahimci abin da Inna ke shirin yi
Inna Hauwa ta tsaya cak da abin da take tana kallon ta Asma’un ta ce.
“Inna don Allah ki ware min kayana ni kaɗai ki mayar da naki cikin adaka, babu inda za ki je, ni ya kamata in tafi ba kuma tare da ke ba, da izinin Allah babu abin da zai same ni sai alkhairi. Zan je in haife abin da ke cikina, na miki alƙawarin muddin muna numfashi zan dawo gare ki a Asma’un da kika sani kuma kika tarbiyyantar.
Fashewa da kuka Inna Hauwa ta yi “Ba zai yiwu ba in bar ki ki shiga duniya ke kaxai Ma’u bayan ina nan da rai da lafiyata kuma cikin hankalina, na tabbata Ubangiji ba zai gafarta min kan haka ba, duk inda za ki je qafata qafarki muna tare duk rintsi, ke kaɗai kika rage min kamar rai da ajali, baki da kowa sai ni, haka ni ma bani da wani xan da ya rage min sai ke, sannan ga larurar da ke tare da ke ya zan barki ki tafi wani gari mai nisa ke kaɗai a wannan halin?”
“Inna ki yi haƙuri ki bar ni in tafi ni kaɗai zamanki a qauyen nan shi ne rufin asirinmu gaba ɗaya, na san abin da kike gudu, ina mai tabbatar miki zan kasance ‘ya mai tsare mutuncinta a ko ina, zan kula da kaina, kuma ina ji a jikina zan dawo in tarar da ke.”
Suka rungume juna suna kuka babu mai rarrashin wani. Ba ƙaramin abu ba ne zai raba uwa da ‘yanuwarta.
Alatilas Inna ta amince, ta tattara kuɗaɗen da suke wajenta duka ta ba ta, duk da cewa ba wasu kuɗi ba ne masu yawa, fatan Asma’u dai kuɗin su kai ta inda za ta je.
“Da zarar kin isa garin Kano ki tambayi makarantar Malam Yahuza mai Dala’ilul Khairati, ki shaida masa ke ɗiyar Malam Tanimu ce babban abokinsa na Somayi, ki tsaya ki nutsu sosai ki yi masa bayani yadda zai gane, don rabon su da Malam shekarun da yawa.”
Danƙari! A tunanin Asma’u da Innarta Kano kamar sauran garuruwa ce da suka sani, wato da zarar ta sauka garin ta tambayi makarantar Malam Yahuza Mai Dala’ilu za a nuna mata, tunda shi ɗin fitacce ne. Babu wanda zai sanar da su irin girman da Kano take da shi, babu wanda zai faɗa musu a Kano akwai unguwanni, kasuwanni, ƙauyuka, al’ummar da ba su da iyaka masu ɗabi’u da halaye kala daban-daban ba.
Very good like to see more
Thank
Masha Allah please acigaba
Za ki ci ba da samun samun Episode a kai-akai