Skip to content
Part 13 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Washegari

Asma’u na cikin ɗaki tana linke kayanta da ta wanke suka bushe, taji an turo ƙofar a hankali, ƙamshin turaren Ma’aruf da a yanzu ta riga ta shaida shi ya gauraye ko ina cikin ɗakin nata, ba sai ta duba ba ta san shi ne, ta dakata da abin da take yi cikin sanyin jiki har ya ƙaraso daf da ita, ba tare da ta kalli sashen da yake ba ta ce, “Ina kwana?”

Ya amsa, sannan ya ce da ita.

“Asma’u in banda hujjojin da kika kawo na san kema kina son zaman gidan nan kuma sam ba a takure kike ba, shin bayan amincewar Zubaidah me ya rage da yake sa ki shakku ko tsoro?”

Maimakon ta ba shi amsa ita ma sai ta jefo masa tata tambayar “Kenan kana nufin Zubaidar tana so in ci gaba da zama kamar yadda kaima kake so?”

“Ƙwarai, ita ce ma ta turo ni wajenki.” Ya faɗa a gajarce. Ta ce, “Ni kam bani da ta cewa, ku tuntubi Hajiya duk abin da ta faɗa shi zan bi.”

Ya jawo kujerar nan ta roba ya kwashe wasu kayanta daga kai ya ɗora mata saman gado sannan ya zauna. “Babu damuwa zan yi hakan da kaina, sannan ina so ki sani ko kaɗan ba ma nufin ki zauna matsayin ‘yar aiki a gidan nan, ki sa a ranki za ki zauna ne tare da ‘yan uwanki, ni na zama yayanki, Zubaidah kuwa dama Antinki ce, zamu riƙe ki bisa amana babu tauye ‘yanci, zan sa ki a makaranta ki samu ilimi sosai da zai amfani rayuwarki, da fatan ke ma za ki riƙe mu amana da zuciya ɗaya.”

Farin ciki ne a zuciyarta, sai dai ba ta bari fuskarta ta nuna hakan ba, a furucin bakin Ma’aruf ta fahimci abin da yake nufi har cikin zuciyarsa ne, idan kuwa haka ne za ta iya cewa a karo na uku ta samu mutum uku da suke ƙaunarta fi sabilillahi.

“Asma’u za ki iya faɗa min wani abu game da labarinki? Ba ina nufin in san asalinki ba, kawai ina son jin damuwar da ke ɓoye a bayan zuciyarki, wataƙila in iya taimaka miki, ko da da shawara ne.”

Asma’u ta dube shi sai kuma ta sunkui da kai, “Bana jin cewa labarina zai maka wani amfani, labarin bashi da daɗi, sai tarin takaici da tuna min wasu abubuwa masu muhimmanci da na rasa a rayuwata, wanda kuma bana jin zan same su har abada.”

Ma’aruf ya nazarce ta na ‘yan daqiqu kafin ya ce, “Me yasa kike tunanin ba zan amfana da komai daga labarinki ba, me yasa kika yanke ƙauna kan samun muhimman abubuwan da kike jin kin rasa, kina da tabbaci kan rasa su?” Cikin mintuna Asma’u ta bashi labarinta a taƙaice.

Haƙiƙa Ma’aruf ya tausaya mata fiye da lokacin da ya ji labarin a bakin Zubaidah don ita akwai ma abubuwan da ba ta sani ba.

“Lallai kin yi rashi mai ciwo Asma’u, sai dai duk a ciki ina ganin mahaifanki ne kawai ba za ki sake samun kamarsu ba, don su ba a iya maye gurbin su, amma sauran abubuwan duk masu sauƙin samuwa ne matuƙar kin riƙi Allah, kin riƙe gaskiya da mutuncinki, idan har za ki bani dama zan tsaya miki wajen binciko mutumin da ya keta miki haddi, za a hukunta shi hukunci mai tsanani.”

Asma’u ta share hawayen da suke fitowa daga idanunta. “A wani lokaci can da ya shuɗe ni da Innata mun so hakan, daga baya muka barwa Allah komai, dama kuma shi ne mai sakamako. A wancan lokacin daga ni sai Inna muka san abin da ya faru, hakan dama shi ne burin Innata, dalilin kenan da ya sa na bar ƙauye na dawo nan, Alhamdulillah. Na gode da son taimako na.”

Sosai ta ƙara ba Ma’aruf tausayi ya ce, “Are you sure Asma’u, yanzu kin amince za ki zauna tare da mu, ga ni ga Antinki da sabon Babyn mu?” Asma’u ta kasa duban sa sai murmushi kawai ta yi tare da gyaɗa kai, shi kuma ya miƙe tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa yana duban ta cike da jin daɗin da ya rasa ko na menene, ba zai ce ga wani dalili da ya shi damuwa da yarinyar cikin ƙanƙanin lokaci ba, ko da yake duk wasu lamuranta masu tsayawa ne a rai matuƙa.

*****
Ko kaɗan ba su samu matsala da Hajiya ba wajen amincewarta kasancewar an sa Ma’aruf cikin maganar. Hajiya Yagana na matuƙar jin nauyin surukinta, tana kuma girmama shi, sai dai ta yanka wa Zubaidah sharuɗɗa masu zafi kan riƙon Asma’u tsakani da Allah babu cutarwa, ta ja kunnenta sosai gami da tuna mata wace ce Asma’u da rayuwar maraici da rashin gatan da ta tsinci kanta a ciki.
Zubaidah ta yi mata alƙawarin in sha Allahu babu abin da zai biyo baya sai alkhairi.

Ba a ɗauki dogon lokaci ba kuwa Zubaidah ta fara zuwa makaranta, sai rainon Khalifa ya koma hannun Asma’u duk da cewa ita ma ayyukan da ke kanta suna da yawa, don tuni ita ɗin ma ta fara zuwa tata makarantar a nan unguwar, Islamiyya ce haɗe da boko, kuma PRIVET SCHOOL, ko da aka kai ta ma bayan an mata interview aji shida aka cilla ta saboda ƙwazonta, a ƙoƙarin Ma’aruf ta zana jarrabawar tafiya sakandire kai tsaye, haka kuwa aka yi.

Sammako ta ke yi ta kammala ayyukanta sannan ta yi wanka ta sanya uniform ta tafi. Sai ƙarfe ɗaya na rana a ke taso su, tana dawowa za ta tarar Zubaidah ta sa direba ya kawo mata Khalifa daga makarantarsu don yaron ya fara wayo, ba ya rigima kuma sam bai damu da nono ba, idan yana barci mantawa ma suke yana gidan su yi ta sabgoginsu.

Idan Asma’u ta samu sarari ta kan ziyarci Hajiya ta jima a gidan musamman ranar da babu school. Kawo yanzu tun daga kan suttura, kayan kwalliya da ita kanta kwalliyar sai dai ta goga da su Ummita domin tana fita tana ganin yadda ‘yammata suke gyara kansu.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta sauya tamkar ba ita ba, don ta fara samun nutsuwa, kyawu da dirin da Allah Ya mata suka ƙara bayyana, samari kuwa suka fara kawo mata hari, sai dai Asma’u ba ta taɓa muradin sauraron ko wane kalar namiji ba, sannan alfarma da girman gidan da take zaune gami da kwarjinin Ma’aruf a unguwar suka ƙara siya mata martaba, ko a cikin samarin ma ba ko wane kwashi kwaraf ke zuwar mata ba, yadda ta saje cikin ‘ya’yan masu hannu da shunin unguwar haka manemanta yawanci ‘ya’yan waɗanda suka ci suka tada kai ne. Sai dai wannan sam ba shi ne a gaban Asma’u ba
A makarantar su ta yi ƙawa, ita ma ‘yar unguwar ce, don layi ne kawai ya raba tsakanin su da Maijiddah, ajin su ma ɗaya, ta su ta zo ɗaya don dukkan su ba su da kwaramniya.

Har kwanan gobe Asma’u tana kaffa-kaffa da alaƙarta da Ma’aruf da Zubaidah, sam ba ta yarda Zubaidah ta ganta tana keɓewa da mijinta, duk da shi kuma ya mayar da hakan ba komai ba, domin duk sa’ar da ya so ganin Khalifa idan yana wajenta haka zai shigo ɗakinta ya zauna bakin gado ya ɗauke shi yana masa wasa ba tare da kawo komai a ransa ba. Hijabi da niƙab yanzu sun zama wani ɓangare na sutturar Asma’u, sun zame mata abin ado, don ko wanka ta yi idan ba ta sa dukkansu ba ba ta jin daɗi.

Zaman gida ya fara qaranci a gurin Zubaidah, domin bayan ta gama dukkan lectures ɗinta ma sai ta gama yawonta sannan take dawowa gida. Zuwa yanzu Asma’u ta shaida shaƙiƙan aminan Zubaidah musamman Ruƙayya, Bushira da Suwaiba Fashion.

Tun kafin ta saka ƙafarta cikin falon ta tsinkayi muryoyinsu, gabanta ne ya faɗi! Bisa amanna da ta yi kan zuwan Ruƙayya gidan ba ya taɓa zame mata alkhairi, don duk zuwan da za ta yi bayan ta tafi sai ta samu sauyin fuska daga Zubaidah, ko ta yi ta mata faɗa marar dalili.
Su dukan su suka yi mata caa da ido in ka ɗauke Zubaidah da ta nutse cikin kujera hankalinta na kan wayarta. Da sassarfa Asma’u ta isa gare su har da russunawarta ta ce, “Sannunku, ina wuninku?” Bushira da Suwaiba suka amsa fuska sake, Ruƙayya kuwa ɗibanta ta yi ta watsa kwandon shara.

Ba ta tsaya ba, ta wuce su a qoqarinta na isa ɗakinta, tana jiyo sa’ar da Ruƙayya ta ja tsaki tsuut! Lamarin da ya ja hankalin Suwaiba kanta ta ce, “Ya ya dai shegiya naji kina tsaki, ke da wa?” Bushira ce ta cafe, “Ita da yarinyar nan ne, kawai ta ɗauki karan tsana ta ɗorawa ‘yar mutane babu laifin tsaye ba na zaune.”

“Yar mutane fa kika ce, kin san asalinta ne? To ita kanta Zubaidar ba ta san daga inda ta fito ba.”

<< Kaddarar Mutum 12Kaddarar Mutum 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×