Skip to content
Part 17 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Zubaidah ta hau sama sosai, yadda take ji a ranta son samunta ko kwana kar Asma’u ta ƙara yi a gidan ta ce, “Kina ji na Asma’u? Maza shiga ki tattaro duk wani abu da kika san naki ne ki zo ki same ni a nan.” Kuka take yi sosai ta shiga ɗakin ta haɗa kayanta cikin akwatu, yau dai ƙarshen zamanta a gidan ya zo, sai dai hakan shi ne mas’laha tsakaninta da Zubaidah da shi kansa Ma’aruf, haƙiƙa ta so shi, kuma tana son shi, sai dai ta yarda su rayu a MAFARKI kawai, me yiyuwa ma da zarar ta kwana biyu a gidan Hajiya za ta manta da shi.

Lokacin da ta fito suna tsaye cirko-cirko suna jiranta yayin da Ruƙayya na ta faman ƙara yi wa Zubaidah famfo, a yadda take faɗa mata idanun Ma’aruf sun gama rufe wa kan Asma’u, a shirye yake ya aure ta. Tabbas biri ya yi kama da mutum, abubuwa da dama sun faru a kan idonta wanda ya kamata a ce ta fahimci inda suka sa gaba, sai dai ba ta fahimta ɗin ba sai da yaƙin ya fara cinta har gida.

Kishi bala’i ne, ko da Asma’un ta fito Zubaidah ta ƙarewa halittun jikinta kallo sai ta ga yarinyar ta yi wani irin gogewa, kyau, diri daga ita har Ruky babu abin da za su gwada mata, musamman Ruƙayya da hancinta ya baje a kan faffaɗar fuskarta da ta sha man bleaching.”

“Je ki wajen mota ki jira mu.”

Wai yau Zubaidah ce ke mata magana haka kamar ba ta taɓa ganinta a rayuwarta ba, tabbas ta yi dana sanin sanin Ma’aruf a rayuwarta, ina ma ƙaddara ba ta haɗa su ba. Ta kai minti biyar tsaye a jikin mota hawayenta na zuba tana sharewa sannan suka fito, direba ya taso da sauri ya buɗe musu ƙofofin motar suka shiga, shi ma ya shiga ya tashe ta, Zubaidah da Ruky ne a baya, ita kuma tana gaba gefen direba, maigadi ya buɗe get suka fice daga gidan.

*****
“Aunty ina muka nufa ne? Na ga an kauce hanyar gidan Hajiya?” Asma’u ce ta yi tambayar zuciyarta a karye kuma cike da fargabar martanin da zai biyo baya, ba tsoro take ji ba, domin yanzu ta riga ta bar mata mijinta. Babu wanda ya amsa mata tambayar har suka wuce gwauron dutse da ƙofar ruwa, sai ga su a cikin tasha. Sai yanzu Asma’u ta tabbatar da abin da Zubaidah ke shirin yi.
Motar tayi parking, nan da nan sai ga ‘yan kamasho sun lulluɓe su.

“Hajiya Zinder ne, ina za ku je?”

“Zinder ne, mutum ɗaya ne zai tafi, ga ta nan a gaba, amma ba ma son tsaye-tsaye, ka tabbatar motarku ta gama cika tafiya kawai za ku yi.”
“In sha Allahu Hajiya, fasinja biyu kawai muke jira.” Zubaidah ta ce. “Yauwa ɗaga but ka ɗauki akwatunta tana nan.”

Ɗan kamashon ya zagaya ya ɗaga but ya ɗauki akwatun Asma’u ya je ya je ya sa a na waccan motar mai tafiya, ya dawo Zubaidah ta ba shi kuɗin motarsu sannan ta fito da wasu damin kuɗin ‘yan dubu-subu daga cikin jakarta a cikin baƙar leda ta miƙa wa Asma’u, kuɗin ba kaɗan ba ne, Asma’u ta qi karɓa, don haka ita kuma ta jefa mata a kan cinya.

“Ki zauka kar ki yi wa kanki, na tabbata za su ishe ki duk wata rayuwa da za ki yi a ƙauyenku, wataƙila daga yau babu mai arziƙinki, ki yi haƙuri ki yafe min, ban so mu yi irin wannan rabuwar ba, amma babu yadda na iya, domin ina son gina katanga tsakaninki da mijina, ban da wauta irin taki ina ke ina Ma’aruf? Ni na tabbata ma yaudarar ki kawai zai yi, fita maza ki je ga motar can ta kusa cika.”

Asma’u ta buɗe motar ta fita ta zagaya ɓangaren da Zubaidah ta ke, ta miƙa mata kuɗin. “Aunty Zubaidah ga kuɗin nan, ni babu abin da zan yi da su, duk abin da na yi muku ba don kuɗi na yi ba, kun nuna min karamcin da kuɗi ba zai iya siyen shi ba, na gode, na gode Allah Ya saka muku da alkhairi, ki jaddada min godiya ta gun Hajiya, na roƙe ki wannan alfarmar.”

Ruƙayya da ke gefa tana hararar ta a zuciyarta faɗi take “Munafukar Allah ta’ala, yau ƙarshenki ya zo.”

Zubaidah ta ce, “A a Asma’u ke yarinya ce, har yanzu baki da wayo, ki riƙe kuɗin nan, ki adana su, na tabbata babu wasu kuɗin kirki a hannunki, kuma dole kina da buƙatarsu a halin yanzu, za su yi ki miki amfani nesa ba kusa ba, don rayuwa ba za ta taɓa yiyuwa babu kuɗi ba, duk wani ‘yanci da jin daɗi yana tare da su, sannan kuɗinki ne da Ma’aruf yake bani ina ajiye miki, ki yi haƙuri ki karɓa, hakan ba wai yana nufin mun biya ki abin da kika mana ba.”

Da ta fuskanci dai Asma’un ba ta da niyyar karɓa sannan tana neman ɓata musu lokaci, ga mota na shirin tashi sai ta buɗe murfin motar ta fito ta kamo jakar hannun Asma’u ta buɗe ta tura mata kuɗin a ciki ta mayar ta zuge ta sake rataya mata jakar a kafaɗarta.
“Hajiya ke kaɗai fa ake jira.” In ji ɗan kamasho. Asma’u ta juya ta nufi inda motar take idanunta suna ta tsiyayar da hawaye, abubuwa biyu zuwa uku su ke ɗaga mata hankali, na farko yadda za su yi rabuwa irin wannan da Hajiya Yagana, ba ta taɓa tsammanin rabuwarsu a nan kusa ba, sai kuma babban tashin hankalin da za ta riska a ƙauyensu idan ta koma, sannan gidan wa za ta dosa a matsayin da take yanzu? Duk lokacin da ta tuna ko da suna ƙauyensu sai gabanta ya faɗi, don haka a cikin motar ta canza shawarar babu ita babu komawa Somayi.

Tun kafin a ƙarasa da ita mararrabar ƙauyukan ta sauka, ta sake shiga wata motar da za ta nufi garin kakanninta ba tare da tunanin za ta riske su ko akasin haka ba, ko ma dai meye dole can za ta nufa tunda dai ba za ta shiga duniya ba, kai a shirye take ta zauna ko da a dokar daji ne, ba za ta sake yunƙurin barin ƙauye ba, domin tana jin a halin da take ciki shi ne yafi dacewa da ita, sannan yanzu ba ciki ne a jikinta ba bare ta riski kwatankwacin wancan ƙalubalen da ya sabbaba mata zuwa birnin Kano.

Mota ta sauke ta, ta tare kabu-kabun da zai shiga da ita ƙauyen, ta hau da kayanta duka. Ko rabin awa ba a yi ba suka iso garin Gabas, babu wani ci gaba a ƙauyen fiye da shekaru uku da ta san shi, duk inda ta gifta mutane duban ta suke kamar ba su taɓa ganin halitta irin ta ba.

Asma’u ta sa kai cikin wani gida bayan ta yi sallama, wata tsohuwa da ke kwance a wata rumfar kara ta zabura ta tashi, har tana tsorata wasu garken kaji da suka yi sansani suna tsattsagar dusar gero, suka watse suna ihu.

“Kamar Ma’u nake gani, na rantse da girman Allah ita ce, Arzuka! Arzuka!! Fito maza ga Ma’u ta dawo, la haula wa la ƙuwwata illah billah.” Ta nufo ta tana ƙoƙarin sauke mata akwatun da ke kanta.

<< Kaddarar Mutum 16Kaddarar Mutum 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×