14 Ga Rabi’ul Auwal.
Ranar bikin Asma’u ta ga mutanen da ko a mafarkinta ba ta taɓa kawowa za su zo ƙauyen su ba, Maijiddah da mamanta ma sun zo. Hajiya Yagana da ɗaukacin ‘ya’yanta in ka ɗauke Zubaidah hatta Nasir ya zo ɗaurin aure. Ranar ɗaurin aure ƙauyen Somayi ya cika da manyan Alhazai, Malamai da matasa ‘yan birni abokan Ma’aruf. A gidan Maigari aka yi komai inda waliyyin ango ya damƙa sadaki ga waliyyin amarya naira dubu hamsin.
An gudanar da komai yadda ya kamata bisa addini da al’ada daga dukkan ɓangarorin biyu. Bayan an ɗaura aure aka tafi da amarya tare da wasu daga cikin danginta cikin motoci zuwa Kano gidanta kuma gidan da abokiyar zamanta Zubaidah take.
Kai tsaye aka wuce da ita sabon ɓangaren da Ma’aruf ya gina a cikin gidan, komai da komai iri ɗaya ne da ɓangaren da Zubaidah take, sannan komai da yake a can akwai shi a nan. Asma’u dai dama kuɗin wajenta har sadaki duka ta haɗa ta ba Hajiya, ba ta san yadda ta yi da su ba, amma dai ga furnitures nan ‘yan uban su masu kyau da tsadar gaske.
Su Munari, Ramatu da wasu daga cikin matan Maigari da manyan ‘ya’yansa mata ne suka rako amarya, tabbas idanunsu sun ga abin da ba su taɓa gani ba, don tun suna nuna ƙauyancin su a fili har ma suka zo suka saba, to duk abin mamakin da suka gani ba za a kara mintuna ba sai sun ga wanda ya fi shi. Asma’un da ta taso tare da su a ƙauyen ƙayau da ko injin niqan hatsi babu, yau ita ce za ta rayu cikin wannan aljannar duniyar, tabbas duk inda ɗan’adam ya rayu ƙaddararsa ba ta wuce shi.
Ƙafafun Asma’u na taka lallausan kilishin da ke malale a ƙasa, bakinta yana karanta addu’o’i da hamdala ga Ubangiji marar iyaka, ta san wannan duk ni’imarsa ce da Yake wa wasu cikin bayinsa. “Godiya ta tabbata ga Allah a cikin ko wane irin hali, “Ya Ubangiji ina roƙon Ka wanzar da zaman lafiya tsakanina da abokiyar zama na, Ka tsarkake zuƙatan mu, Ka ƙara min haƙuri da juriya wajen bin sunnar Ka, Ka ba ni ikon kyautatawa mijina Allah.” Maijiddah ta kama ta ta zaunar da ita kan gado, har yanzu tana cikin lulluɓi, ba za a ce ga yanayin da take ba, ita ba kuka take ba, domin kuka ta gama shi tun a gida lokacin da za ta rabu da wadancan tsofaffin da suma suka sha kukan rabuwa da jikar su guda ɗaya da ta rage a duniya. Ranar Asma’u ta sha kukan rashin mahaifanta musamman Inna da suka shaƙu. Hajiya ta leƙo ɗakin ta ce su fito da ita zuwa sashen Zubaidah.
Sun shiga uwar ɗakin Zubaidah, ita kaɗai ce zaune a kan gado fuskarta babu yabo ba fallasa. Yanzu ba sa tare da manyan ƙawayenta. Hajiya ta tashi tsaye sosai wajen raba tsakaninsu don idan suna tare babu sauƙi, Ruky fitinar duniya ce sai dai fatan Allah Ya shirya. Tana da yaƙinin ita kaɗai ce za ta sa Zubaidah ta bijire mata ta bijire wa mijinta don haka ta dage da addu’a kan Allah Ya raba ƙawancensu.
Tun kafin su shigo ta gargaɗi Zubaidah kan nuna wata halayya da ke nufin tayar da fitina, “Zan faɗa miki gaskiya a matsayina na mahaifiyarki Zubaidah, sam bai kamata ma ki ƙwallafa rai kan ke kaɗai za ki rayu da namiji ba, wannan kuskure ne babba ga duk wata ‘ya mace, baki nemi zaman lafiya ga rayuwarki ba, haƙurin nan dai shi ne, tare da sa wa a ranki cewa bautar Allah ki ke, duniyar ma duka guda nawa take? Don Allah mu gujewa son zuciya, mu so wa ‘yan uwan mu abin da muke so wa kan mu, rayuwar nan da kike gani wallahi mai sauƙi ce amma fa ga wanda ya ɗauke ta da sauƙin, idan kuwa ka ɗauke ta da zafi sai ta ƙona ka don ta fi wuta ƙuna.”
Da yanayin nan dai na ba yabo ba fallasa Zubaidah ta karɓi amana da gabatarwar amaryarta Asma’u. Bayan fitar su ta share wasu hawaye masu zafi da suka fara tuttuɗowa daga idanunta. To ya za a yi? Ita fa dama rayuwar nan dukkanta haƙuri ce, dole sai an danne, an kawar da kai, an kai zuciya nesa uwar gida Zubaidah Mukhtar.
Murfii.
Jirgin saman Egypt Air Line da ya sauka a Aminu Kano International Airport da misalin ƙarfe sha zaya na ranar talata da ta yi daidai da biyu ga watan Mayun shekara ta dubu biyu da ashirin da uku. Yana ɗauke da fasinjojin ƙasashe a ƙalla uku ciki har da ƙasar Dubai. Daga cikin fasinjojin akwai Ma’aruf da amaryar sa Asma’u bayan da suka zagaye ƙasashe huɗu ciki har da ƙasa mai tsarki Saudi Arabia.
Nabil ɗan ƙanin mahaifin Ma’aruf ne ya zo taryen su da sabuwar mota Vibe baƙa wuluk, suna tako matakalar jirgin cike da shauƙin junanasu, a lokacin watannin su biyu har da ɗorin kwanaki da aure inda Asma’u ke ɗauke da tayin cikin sati huɗu da kwanaki biyu.
A cikin motar ma suna gidan baya maƙale da juna, hira suke irin ta masoyan da suka shaƙu matuƙa. Nabil da ke tuƙi baya jin ko da motsinsu bare ya iya sauraren abin da suke faɗa, har suka iso gida. Har falo ya shigar musu da kayansu kana ya fita.
Jim kaɗan suna zaune a falon ya sake dawowa yana rungume da Khalifa a kafaɗarsa, ya sauke shi yana faɗin, “Ga Daddy ya dawo.”
Zubaidah ce ta faɗo ran Asma’u, anya ta kyauta, ko kuma ta ce sun kyauta? Tun ranar da ta zo gidan sati guda kafin su yi tafiya zuwa yanzu ba za ta ce ko da sau ɗaya sun gana da Zubaidah ba. Khalifa ya tako da gudu ya ƙanƙame Daddynsa, sannan ita, Asma’u ta rungume yaron tsam a ƙirjinta, lokaci guda duk ranta ya jagule. Zubaidah fa ɗiyar Hajiya ce, don me zamantakewar su za ta kasance irin haka? Da wannan tunanin ta kwanta a ranta, don haka ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tonon tattauna maganar da Ma’aruf.
“Daddy ina jin kamar muna aikata ba daidai ba, kamar bai kyautu a ce Zubaidah na gidan nan tsayin wani lokaci ban taɓa zuwa na gaishe ta ba, ba ka taɓa haɗa mu mun zauna inuwa guda ba, bana tsammanin hakan zai haifar da ɗa mai ido.”
Shiru ya mata tsayin wasu sakanni, ta lura kamar ba shi da niyyar magana don haka ta sake cewa, “Kana jin me nake faɗa kuwa Daddy?” “Ke waye ya faɗa miki cewa tana gidan nan tuntuni? Ya tambaye ta. Ai kuwa ba ta san lokacin da ta tashi ta zauna tana kallonsa cikin firfito da ido ba, “To tana ina?” Ya juya mata baya alamun ba ya son ci gaba da maganar. Jikinta ya yi sanyi sosai ta tashi ta koma inda ya juya fuskarsa “Me yake faruwa ne Daddy? Me ka yi mata? Sam ba zan ƙyale ba, Zubaidah fa kamar ‘yaruwa take a waje na.”
“Look Asma’u! Kar ki ɗaga min hankali don Allah, tunda ‘yaruwarki ce ki je may be tana sashenta sai ki ganta.” A tsorace take kallon yadda yake magana cikin ɗaga murya, yana kuwa rufe bakinsa ta sa kuka. Abin da ya tsana duk duniya.
“Shit! Asma’u wai meye haka ne?” Ba ta kula shi ba ta tashi ta koma makwancinta tana rera kukan a hankali. Dole Ma’aruf ya koma rarrashinta. “Asma’u ni fa ko kaɗan bani da laifi kan lamarin Zubaidah, me take so in zama ne a kanta? Tunda aka yi auren nan ban ƙara ganin fuskar mutunci a wajenta ba, duk yadda na so in rarrashe ta ta ƙi saurare na, idan na shiga inda take kullum ba ta da burin da ya wuce ta ga ta wulaƙanta ni ta zage ni, ni fa mijinta ne.” Ba tare da ta dakata da kukan da take ba ta ce, “To amma yanzu tana ina please?”
“Tun kwanaki uku da ɗaura aure ta kwashi kaya cikin akwatu ta fita, na je gidan Hajiya ba ta je can ba, ke duk inda nake tunanin zan gan ta na je ban same ta ba, idan zan kwana ina kiran wayarta ba za ta ɗaga ba, sai dai ma daga ƙarshe ma ta kashe wayar, har muka yi tafiyar nan ba ta dawo ba. Ban faɗa wa Hajiya ba don ba na so ran ta ya ɓaci ta yi fushi da ita, muna gaf da dawowar nan ne na ga saƙonta wai ta dawo ta gane gaskiya, za ta zauna da ke, yanzu meye laifina a nan Asma’u?”
Ta share hawaye. “Yanzu tana gidan nan kenan?” “Ni ma ban sani ba, don ba zan tabbatar ba tunda ban leƙa sashen ta ba, ga dai Khalifa da shi ta tafi, shaida kenan.” Tashi ta yi zaune tana fuskantarsa. “Ka san mene kuskuren ka? Jiya da muka dawo ya kamata a ce ka je ka duba ta tunda har ta tura maka saƙon cewa ta dawo.”
Ya ce, “Amma ni ba ki duba irin ɓata min ɗin da ta yi ba? Ban jin cewa zan yarda ta ci gaba da gara ni irin yadda ta so, ɗan’adam ne ni, ina da zuciyar da ba ta jurar wulaƙanci a cikin ƙirjina, kin gane ko?”
Asma’u ta dube shi sosai mutum ne mai sauƙin hali, amma wasu lokutan yana da wuyar sha’ani, sai dai ya zama dole ya san cewa; a yanzu shi ƙasurgumin mai laifi ne a wajen Zubaidah.“
Ai kai babba ne a kan ta kuma namiji, ka yi tunani dole ta ji babu daɗi kan abin da ya faru, haka lamarin nan yake ga ko wace ɗiya mace, dole a irin wannan yanayin sai ka zage damtse ka jure shariya da tutsunta ka lallaɓa ta har ta sauko, don girman Allah yanzu a daren nan ka je gare ta ka nuna mata tana da matuƙar muhimmanci a gare ka, ka ji?”