Skip to content
Part 1 of 3 in the Series Kaddarata by Umar bin Ally

Iyayena yan asalin jahar Maiduguri ne amma yanzu suna zaune ne a garin Kano anan aka haifeni na girma nayi karatuna bantaba zuwa garin iyayena ba wato Maiduguri a tsawon shekaruna ashirin da biyar da haihuwa.

Wata rana kawai aka wayi gari ina son zuwa dan naga yan uwana dake can nanemi izini a gurin iyayena suka bani damar naje suka kuma ji dadin hakan domin sukansu saudayawa sun nemi naje din amma sam naki zuwa.

Nan take kuwa nasa rana na fara shirye shiryen tafiya hardai ranar tazo nakama hanyar tafiya akan hanyarmu na tafiya mukai wani rashin sa,a yan fashi suka tare mu suka kwace komai namu tundaka kan kudaden hannunmu hatta da wayoyin mu mundai yi sa,a basu taba lafiyarmu ba.

Bamu shiga Maiduguri ba sai tsakar dare gashi bansan gari ba gashi ba kudi ahannuna ga wayata ma babu duk an kwace su gashi bansan adreshin inda zani ba haka nakwana a tashar dan bansan inda zani ba.

Gari na wayewa na fara tunanin ta ina zan fara abinda ya fara fado min a rai shine Fatima zarah kawata ta Facebook wacca tafiyar tawa ma zan iya cewa itace sila na fake da yan uwa na ne kawai dan a barni na taho amma na zone kawai dan na hadu da ita.

Fatima Zarah mun hadu ne da ita a shafin sada zumunta na Facebook. Sannan mun saba da juna babban burin zuciyoyin mu shine muhadu da juna maimakon nanemi waya nakira gida sai na matsa kusa da wani mai sayarda agoguna da kuma gyaransu. Na cire agogon hannuna na sayar masa dashi wanda shi kadai yan fashinnan suka bari dashi meyuwa basu kula dashi a hannu na bane ya saye shi akan naira dubu uku nakarbi kudin nashiga wani cafe da nagani akusa dani nasayi awa daya nayi login account dina na Facebook saidai nayi rashin sa,a lokacin bata online

Haka nayita jiranta ina kallon screen din computer har awa daya yakare batahau ba nasake biyan kudin wata awar shima saida yarage baifi minti goma ba sannan naga tahau

Wani farin ciki naji ya lullubeni nayi sauri naimata magana babu bata lokaci tadawomin da amsa na fada mata nashigo garinku tayi farinciki sosai kasan cewar gidansu yana kusa da tashar bata wani bata lokaci ba tazo kai tsaye muka wuce zuwa gidansu

Aka kawomin abinci da abinsha iri iri naci nasha muka zauna mukaita hira harda yan gidansu kaikace dama can munsaba dasu inanan dai agidan nasu har akayi sallar la,asar

******
A nasu bangaren kuwa yan uwana da nataho gurinsu tunda mukai waya dasu akan nataho sukaita jira hardai sukaga dare ya fara yi kuma sunkira number ta sunji bata shiga sai hankalinsu ya mutukar tashi suka kira gidanmu suka shaida musu suma nasu hankalin yatashi haka suka kwana basuyi bacci ba.

Washe gari kuwa tun safe suka fito nemana lungu da sako amma basu sameni ba sukayi sa,a suka samu motarda ta kawomu aka shaida musu abinda yafaru damu ahanya na yan fashi aka shaida musu amma munshigo gari lafiya.

Sai bayan sallar la’asar din natuna da su cikin sauri na karbi wayar fatima zarah nakira gida nasha fada sosai sannan aka turomin da number gidan da zan sauka nakirasu cikin gaggawa saigasu sunzo mukayi sallama da gidan su Fatima Zarah muka muka tafi.

Sati daya nay I agarin amma kullum muna tare da Fatima Zarah yan uwa na basu wani samu lokacin hira dani ba har lokacin dawowata yayi a ranar da zan dawo Fatima Zarah ta rakoni tasha muna zaune muna hira kafin mota tacika kaawi naga ta kura min idanu tana ta kallona nadanyi dariya cikin tsokana ace mata menene kiketa kallona haka budar bakinta tace dani tunani nake na kara tambayarta tunanin me kuma ta lunshe ido ta budesu akan fuskata tace dani ina tunanin wacce irin me sa,a ce ni arayuwa da nasamu maikilawa da lamarina kamarka

Dariya mukayi gaba dayan mu adaidai lokacin da motarmu ke shirin fara tafiya naga tayi saurin juyawa zata tafi cikin sauri na riko mayafinta ina fadin bazaki tsaya kiga tafiyata ba kasa juyowa tayi bataso naga hawayenda ke zuba saman kyawawan kumatukanta tayi sauri ta share hawenta ta kakalo wani murmushi sannan tajuyo.

A lokacin da na kalli cikin idanuwanta nagansu cike da hawaye wani abu naji yasoki zuciyata naji tamkar nafasa tafiyar jinayi nima hawayen yana shirin fara zuba daga idanuna nayi saurin juyawa nashiga mota ban juyo ba saidai ina kallonta tacikin madubin motar tanata zubarda hawaye

Nadawo gida kullum tunaninta yana ta kara karuwa a zuciya ta a zahiri dai abota ce tsakanin mu amma ina ganin kamar soyayya mukeyi saidai bawanda ya taba furtawa dan uwansa kalmar so tsakanin mu idan natuna da hakan sai ince gaskiya ba soyayya muke ba.

Wani lokacin kuma sainaga ai shi furta kalmar so bawai shine soyayya ba dan saudayawa wasu sukan furta kalmar ne a iya bakinsu baikai zuciyaba mutum zai furtama kalmar so abaki azahiri kuma ya cutar dakai

Sannan kuma mun shaida bamuda mai son mufiyeda iyayenmu amma kuma ba zuwa sukayi suka fada mana ba amma kuma munshaida bamuda soyayyar gaskiya da tafi tasu

Idan natuna da haka saina ce eh tabbas soyayya mukeyi kuma soyayya ta gaskiya wacce bata bukatar wasu kalamai su bayyana ta.

Wata ranar juma,a 22/4/2015 muka samu wani mummunan labari kan cewa amkai harin ta’addanci a Maiduguri sannan yankinsu Fatima Zarah yan ta’adda sun kwace shi sunkashe mafi yawa na mutanen wajen suna kuma rike da yankin ma’ana yana karkashin jagorancinsu.

Hankalina yayi matukar tashi musamman da nakira number Fatima Zarah naji baya shiga narasa abinda yake min dadi narasa sukuni kullum ina cikin tunani tsahon kwana bakwai ina cikin wannan hali wata ranar asabar an aikeni kasuwa dan nasayo wasu kayayyaki muna cikin tafiya a cikin adaidaita sahu kawai sai ga wata budurwa ta tsallako titi ko dubawa bataiba kadan ya rage me mashin din nan ya bigeta ta fadi kasa alokacin nayi matukar fusata nafito cikin fushi raina abace amma abinda nagani yasa na kame kam KO kyaykywar motsi nakasa.

Fatima zarah nagani adurkushe ta dafe kai cikin tsananin tsorata nabude bakina cikin tsananin mamaki da kokonton shin abinda nake gani gaskiya ne kodai gizo takemin kamar yadda tasaba zarah nafada acikin raina ashe har maganar tafito fili dago kai tayi ta kalleni cikin tsananin farin ciki ta rugo gareni tana kuka saiji nayi ta rungumeni cikin matsanancin kuka tana fadin banida kowa bansan ina iyayena sukeba.

Ganin kowa nawajen kallonmu yake hakan yasa na janye jikina daga nata nace da ita muje gida kihuta idan kin nutsu saimu karasa magar ban ma karasa kasuwar ba nasa mai adaidaitar yadawo damu gida.

Muna zuwa nayiwa mamata bayani nadanan kuwa aka bata abinci taci tasha akace taje tayi wanka bayan tafito kanwata Halima ta dauko mata kaya daga cikin kayan ta tasaka ni dai burina kawai ta kintsa nazo naji labarinda take tafe dashi amma sai mama tace abarta tahuta zuwa gobe sai mu saurareta dan akwai gajiya ajikinta wannan kwana dayan da akace najira jinsa nayi tamakar shekara guda saboda zumudin naga goben nan tayi atakice dai bansamu nayi bacci ba haka nayita juyi har gari ya ways ina dawowa daga salllar asuba kuwa nazo na zauna afalo ina jiran naga fitowarsu

Mamace tafito karfe bakwai na safiya ta shiya abin karin kumallo kanwata Halima kuwa ta fito misalin karfe takwas da rabi cikin rada nake tambayarta ya ta tashi ne tace min a,a mama ta hana mu tashinta cewa mu barta har sai ta tashi da kanta bata farka ba sai karfe goma sha daya na safiya tayi wanka taci abincinci da muka ga alamun tadan dawo hayyacinta sai muka zo dan mufara jin labarin da take dauke dashi.

Kaddarata 2 >>

5 thoughts on “Kaddarata 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×