Yau gabaɗaya ya kasa shiga cikin Class, sai wani malami ya roƙa ya ce yana da wani uzuri ya taimaka ya je ya yi masu karatun.
Ita kanta Suhaila ta ji daɗin yadda ba Farouk bane ya shigo, kasancewar tana shiga cikin ruɗani, da zarar ta ci karo da shi. Suhaila ta dubi Ummi bayan sun fito ta ce,
“Kwana biyun nan sai inji gabana yana faɗiwa da ƙarfi. Allah sai yasa lafiya.”
Ummi ta girgiza kai,
“Mutuwarce har yanzu bata sake ki ba. Ki rage tunani don Allah duk kin sauya.”
Gaba ɗaya Suhaila ta rage yawan magana, haka zalika kullum tana cikin ɗakinta.
Ummi ta shigo ɗakin ta ce,
“Sai ki tashi Momi za ta aikemu.”
Tana murmushi ta tashi kawai ta zura hijabinta.
Wannan karon mota suka shiga Ummi take tuƙawa, suka nufi gidan su Jawahir. Kwata-kwata Suhaila bata ƙaunar zuwa gidan, ta rasa dalilin jin ɓacin rai adalilin shigarsu gidan Anti Laila.
Har ƙasa ta durƙusa ta gaida Anti da Alhaji da suke zaune. Alhaji ya dubeta yana murmushi, kasancewarsa mai yawan zolaya ya ce,
“Amaryar Sadiq ce wannan?”
Gaban Suhaila ya faɗi da ƙarfi, ta duƙar da kanta tana murmushi. Anti ta tamke fuska kamar bata taɓa dariya ba.
“Suhaila maza tashi ki shiga can ɓangaren, ki kirawo min Farouk.”
A natse ta miƙe jikinta babu inda baya rawa. Ita Ummi sarkin rawar kai, tuni ta shige gun Jawahir, ta barta a falon, ita kuma Suhaila kunya ta hanata tashi ta bi bayanta. Dosar hanyar ta yi, tana jin ƙarin damuwa.
Kai tsaye ta murɗa handle ɗin ta buɗe. Yana tsaye jikinsa duk ruwa, ya kafe wani ƙusurwa da idanu, kamar mai karanta wani abu. Tunda take bata taɓa ganin namiji babu kayan sawa ba, don haka ta gigice tana shirin ficewa. Ya juyo yana kallonta da mamaki. Yarinyar tana da sassanyar kyau, ba za a kirata fara kai tsaye ba, zai fi kyau a kira kalarta da _Chocolate_ Colour duk da hasken ya fi rinjayar duhun. Mamaki ne kwance a fuskarsa dalilin da zai kawota har ɗakinsa. Gaba ɗaya ta maƙale jikinta da ke kyarma, ya ce,
“Dawo. Me ya kawo ki ɗakina?”
Ya yi maganar cikin tsare gira. Tana rawar baki ta ce,
“Alhaji ne ya ce wai ka zo.”
Bai bata amsa ba ya gyaɗa kai, itama bata tsaya jiran komai ba ta fice da sauri. Ya saki malalacin Murmushi yana jinjina yadda duk ta zama kalan tsoro saboda kawai ta ganshi babu riga. A zuciyarsa ya ce,
‘Ba ‘yan matan yanzu ba.’
A lokacin da ya fito tuni Suhaila ta shige ɗakin Jawahir. Ta yi kwanciyarta tana jin hirarsu akan maganar auren Ummi da za a tsaida lokaci. Ta jinjina kai tana jin tausayin Ummi, da za ta auri mutum mai wuyan sha’ani kaman Farouk. Gaba ɗaya baya son wargi. Wannan ta yaya zai iya zama da matarsa har su yi hira suna dariya?
Sai bayan Isha’i suka fito. A tsaye suka ganshi a waje yana amsa waya. Cikin kakkausar murya ya ce,
“Amma kuna da hankali zaku kai dare babu direba?”
Suhaila ta ɗan saci kallonsa, tana mamakin gidan da babu nisa? Babu wanda ya ce uffan sai Ummin da take bashi haƙuri.
*****
Sati biyu cur Sadiq ya kwashe a London, ya dawo. Cikin zafi-zafi ya sa aka je nema masa Suhaila. Mahaifinsa Alhaji Sama’ila ya gaya masa yadda suka yi da Alhaji Sambo akan a bashi lokaci zai tattauna da mahaifin yarinyar.
Suhaila da ta ji labarin yadda Sadiq ya haukace sai itama ta ruɗe ta shiga zullumi, dan babu ko shakka Sadiq shi ne gawa na goma da zai baƙunci lahira, muddin bai janye daga ƙudurinsa ba.
Babu shiri Daddy ya kira Abba akan ya zo su tattauna. Isowarsa kenan suka yi Sallah tare, daga bisani suka yi zaman cin abinci.
A falon Daddy suka zauna su biyu suna tattaunawa. Daddy ya dubi Abba cikin damuwa ya ce,
“Kwanan nan na ji labarin wani yaro a Makarantar su ya ce yana sonta, washegari shima ya mutu. Ni yanzu kunyar mahaifin Sadiq nake ji, ga yaron gaba ɗaya ya hargitse Suhaila yake so.”
Abba ya yi shiru, daga bisani ya ce,
“Wai ni ba na gaya mata idan zata fita ta dinga sanya niƙaf ba? A gidan uban wa ta haɗu da Sadiq ɗin?”
Daddy ya girgiza kai,
“Ƙaddara ce. Ka bar ƙaddara kawai, ta wuce duk yadda kake tunani. Sadiqu anya ba abin da ka taɓa aikatawa shekaru masu yawa baya bane, ya dawo yana bibiyarka? Ka tuna wannan furucin da baka ɗauke shi da mahimmanci ba?”
Abba ya yi shiru, daga bisani ya ce,
“Yaya mu bar hasashe. Wannan abin na Suhaila ina ganin daga Allah ne. Mu dage mata da addu’a. Shi kuma Sadiq ɗin ka barshi ya aureta. Insha Allah ba zai mutu ba, mu dage da addu’a. Saboda yanzu ko bayani kayi masu gani za su yi kawai kana son hana su ‘yarka ne.”
Basu gama tatattaunawa ba aka ce ya yi baƙi. Abin mamaki iyayen Sadiq ne wannan karon har da mahaifin Farouk. Don haka suka zauna suka tattauna akan za a haɗa dukka aurarrakin rana guda, nan da wata guda.
Cikin abin da bai fice awanni biyar ba, gida ya hargitse da murna, ita dai Suhaila gaba ɗaya a cikin fargaba take. Abin mamakin kuma Sadiq ya ƙi zuwa gareta. Duk ta fita hayyacinta.
Farouk ne zaune tare da Sadiq suna tattaunawa,
“Sadiq Ka jawo min aiki. Ni bansan wani irin aure ne haka kake son yi a cikin gaggawa ba.”
Sadiq ya saki murmushi ya ce,
“Nima ba auren Allah da Annabi zan yi ba. Farouk ina son infi haka kuɗi da suna da ɗaukaka. Duk da Suhaila ta kai irin matan da nake burin mallaka, sai dai bata da wayewa irin wayewar da nake son samu agun ‘ya mace. Malamina ya gaya min ɗaukakana, da arziƙina suna tattare da Suhaila. Idan na aureta zan zama mutumin da duniya take yayinsa, kai bani ba, hatta zuri’ata sai sun yi shahara na ban mamaki.”
Farouk ya yi tsit yana duban Sadiq yadda yake koro bayani babu abin da ya shafe shi. Idan wani ke bashi labari ba zai taɓa yarda ba.
“Sadiq bin malaman tsubbu kake yi? Yaushe ka zama haka ban sani ba? Tun wuri ka janye ƙudurinka.”
Sadiq ya yi murmushi yana dubansa.
“Kai da tunaninka a zaune nake? Duk wani babba da ka ga ya zama wani, ba a kwance ya zama wani ba, sai da irin muggan dajin nan. Sai ka ga an hasko maka dukka rayuwarka da za ta faru yanzu da nan gaba.”
Farouk ya girgiza kai,
“Allah shi kyauta. Amma ina so ka sani, boka bai isa ya gaya maka me zai faru da kai gobe ba.”
Sadiq ya kauda kansa, daga bisani ya waiwayo ya ce,
“Yanzu dai mu bar maganar nan. Ya shirin zai zama? Party nawa za ayi?”
Farouk ya miƙe yana duban agogonsa,
“Party sai ku wayayyun Abuja. Ni bani da wannan wayewar.”
Sadiq yana murmushi ya miƙe yana zura hannayensa cikin Aljihu,
“To yaushe zamu fara zuwa taɗi, ban taɓa zuwa ba.”
Mamaki ya ƙara kama shi. Ta ya ya ya sami aurenta?
“Nasan tunanin da kake yi. Ka mance Sadiq ɗinka ne? Idan ina son abu duk nisansa ina iya mallakarsa a kwana ɗaya. Haka kawai na ji bana son zuwa wurinta, bare ta dinga zumbula hijabi. Walh da farko da naganta har da niƙaf sai ta burgeni, daga baya da na tuna da akwai abokan da ba zan iya nuna masu ita ba, duk sai na ji ta fice a raina. Bata da wayewa ko alama.”
Farouk ya yi gaba abinsa ba tare da ya furta masa ko kalma ɗaya ba.
****
Yana kallonsu suna ta shirye-shirye, gaba ɗaya baya sa masu baki. Ita kanta Ummi taso ta ɗan keɓe da angonta amma babu fuska. Da aka zo maganar Party ya ce ba zai yi ba, sai da Anti ta nuna masa jan ido sannan ya amince. Haka ta ɓangaren Suhaila gaba ɗaya a girgice take duk ta zama kalan tausayi. Ana saura sati guda biki, gidajen uku suka rikice da shirye-shirye. A lokacin kuma aka fara gabatar da fatittika kala-kala. Farouk bai halacci ko ɗaya ba, sai wanda ana gobe ɗaurin aure. A wannan ranar Inna da Hafsat suka ƙaraso. Inna ta jawo Suhaila gefe guda tana yi mata kallon uku saura tara,
“Ke yanzu auren za ki yi da wannan lalurar? So kike ki kashe masu ɗa ko? Me ya sa ke da mahaifinki kuke da son Zuciya ne?”
Suhaila ta rushe da kuka, bata iya bata amsa ba, har ta wuce tana waigota.
A wannan rana aka shirya shagali na ban mamaki. Suhaila ta ci ado, da kaya iri ɗaya da na Ummi kala ne ya bambanta. A wannan rana Sadiq ya zo da kansa ɗaukarta.
Daga ita sai shi a bayan motar, ya lalubi hannunta ya riƙe, cikin takaici ta zame hannunta.
“Ke ni bana son gidadanci.”
Kalmar ta daketa, ta ɗago a razane tana dubansa, Shi kansa ita yake kallo ya tabbatar tana da kyau, ba wai kyau gama gari ba. Har suka isa babu wanda ya sake magana, sai kalamansa da suke yi mata yawo aka.
Farouk bai iso wurin da wuri ba, hakan yasa aka yi lattin fara shirin. Jawahir ta yi kyau kamar ita ce amaryar. Hatta Anti sai da ta halarci wajen Dinner ɗin.
Farouk ya ɗago ya dubi Suhaila, ya kauda kansa. Bayan ankammala Dinner ɗin kowa ya fara kama gabansa, a lokacin Farouk yana ta neman Sadiq aka tabbatar masa ya ɗauki amarya ya tafi. Bai kawo komai aransa ba ya shige motarsa yana ta tunanin zuci. Kamar ance ya waiwayo ya hango motar Sadiq tana tafiya. A hankali ya dinga bin motar. Ya shiga ruɗani ganin Sadiq ya kama hanyar gidansa. Gabansa ya faɗi da ƙarfi, dole ya ci-gaba da binsa. Sai da ya tsaya na wani lokaci ya jira shi ya shiga tukun, kafin shima ya shigo layin. Maigadi ya buɗe masa Gate kasancewar motar Farouk ba ɓoyayyiyar mota ba ce.
A gurguje ya fito ya faɗa falon, baya nan, sai gyalen Suhaila.
A bakin ƙofar yasa kunnansa. Shessheƙar kukan Suhaila yake ji tana roƙonsa,
“Don Allah ka taimakeni ka da ka wulakanta darajata, kada kayi min haka.”
Ƙafa yasa ya bugi ƙofar ta buɗe. Sadiq ya ɗago daga ƙoƙarin kamota da yake yi, duk ya yi gumi. Cirko-cirko suka yi, Suhaila ta tashi da gudu ta koma bayan Farouk tana jin zuciyarta tana tuƙuƙi. Sadiq bai iya cewa komai ba, ya duƙar da kansa. Farouk ya ƙaraso har gabansa ya ɗauke shi da mari, kafin ya dawo hayyacinsa ya sake sa hagunsa ya ɗauke shi da mari yana huci.
“Idan kai mazinaci ne me zai sa dole sai da matar da zaka aura ana gobe zaka aikata hakan? Sadiq! Anya Abubakar ɗinane wannan ko kuwa ansauya min shi? Don Allah Sadiq ka ƙaryata min kanka don Allah.”
Sadiq ya yi shiru yana riƙe da fuskarsa. Farouk ya juya ya kamo hannun Suhaila suka fito falo. Ya ɗauki gyalenta ya sa mata akai. Gaba ɗaya suka kafe juna da idanu. Ya juya kawai ta biyo bayansa.
Da gudu yake jan motar hakan ya sake firgitata ta riƙe jikinta tana kuka. Yana ajiyeta ya yi gaba abinsa. Ta daɗe taugunne a gefe tana kuka. Ita kanta ba za ta ce ga iya mintunan da ta kwashe anan ba, ta dai san ƙafafunta sun ɗauki zafi. Ummi ƙaraso kanta agigice ta kama hannunta suka koma can wani wurin.
“Ke ina kika shiga? Ga Sadiq can ance Walh anyi zaton mutuwa ya yi, kamar ma gamo ne saboda wai sai ya nuna wani abu yana ihu. Amma anshawo kan matsalar.”
Gaban Suhaila ya faɗi da ƙarfi ta riƙe ƙirjinta. A hargitse ta ce,
“Sis kira min Yaya Farouk.”
Ummi bata kawo komai ba, ta kira shi tare da fatan ya ɗauka. Cikin sa’a ya ɗaga wayar, hannunta yana rawa ta fara magana,
“Ya Farouk wai wai Sadiq…”
Farouk ya katseta yana sake duban Sadiq wanda kamar ba zai sha ba, amma yanzu kuma ya wartsake,
“Suhaila ki kwantar da hankalinki. Ina tare da Sadiq Insha Allah babu abin da zai same shi.”
Suhaila ta sauke wayar tana ci-gaba da kuka. Ta riga ta sani sai Sadiq ya mutu, dole Sadiq ya mutu. Ummi ta girgizata,
“Lafiyarki ƙalau kuwa?”
Ta ɗago cikin kuka ta ce,
“Ummi duk wanda ya ce zai aureni ko ya ce yana sona, yana mutuwa. Baki san wannan sirrin ba, saboda mutum ɗaya kika san ya mutu ana gobe bikinmu ko? Baki san dalilin fitowata daga gidan miji ba ko? To duk mutuwa suke yi. Sulaiman ya mutu ne a sanadiyyar ya ce yana sona. Tabbas Sadiq Shi ne mutum na goma da zai mutu muddin ya kafe sai ya aureni.”
Ummi ta ƙwalalo idanunta, ta firgita ta gigice har ma ta rasa me za ta ce, sai kawai girgiza kai take yi,
“Yanzu Suhaila bari za ki yi shima Sadiq ɗin ya mutu?”
Suhaila ta sake rushewa da kuka ta ce,
“Ba laifina bane, su Daddy sun fi kowa sanin matsalar nan, kuma sun ƙi ɗaukar mataki akai suka amincewa Sadiq.”
Dukkansu sun kasa cewa komai, har suka tafi ɗakin kwanciya. Ummi ta jawo Jawahir ta gaya mata komai. Jawahir ta gigice iya gigicewa. Suka jawo Anti Laila suka gaya mata, a lokaci guda hankalin Anti Laila ya tashi. Gaba ɗaya Allah-Allah suke gari ya waye tun kafin a ɗaura auren, kasancewar ɗaurin auren Sha ɗaya na safe ne.
Jawahir suka kira Suhaila babu irin cin mutuncin da ba su yi mata ba, Anti Laila ta ce,
“Kuma Wallahi ba zai aureki ba, bare ki cinye shi. Allah ya rufa asiri, ashe alamu ne ya nuna shiyasa ɗazu aka yi zaton ma mutuwa ya yi. Ba banza ba na tsaneki Wallahi bana son buɗe idanuna inganki, yanzu ki koma can gidan Asiya ba anan gidan za ki kwana ba. Baƙar mayya.”
Anti Laila ta ɗaga waya ta kira Momi tana gaya mata. Momi ta ce,
“Hmmn yanzu nake shirin kiranki ingaya maki. Nima yanzu Inna take gaya min komai abin ya girgizani. Ki barni da komai, ba za a taɓa ɗaura auren nan ba.”
Suhaila tana kuka ta fito, tana takawa a ƙafa tana sharar hawaye. Ummi da bata yi zaton abin zai zama haka ba,ta juya za ta bi bayanta. Anti ta daka mata tsawa, dole ta koma ɗaki cike da tausayi.
Duniyar ta yi mata baƙinƙirin. Tana tafiya ta ji alamun mutum a kusa da ita, za ta yi ihu yasa hannu ya toshe mata baki.