Skip to content
Part 1 of 4 in the Series Kangin Rayuwa by Fatima Rabiu

Fachankan wani K’auye ne dake k’aramar hukumar Jigawa, rayuwar K’auyan abun sha’awa ce, sai dai suna da k’arancin addini harda ma na boka, bawai babu Makarantun ba, a’a sunfi ba sana’arsu mahimmanci, da yawan y’an matan garin talla suke yi, sai kaga budurwa tana tallar abinci da dai sauransu, sana da kin kai shekara sha uku ko hud’u za’a fara shirye-shiryen aurar dake, da yawansu suna durkusar da yaransu, sai kiga yarinya k’arama ta tsufa da wuri, gara ma mazan garin idan suka dage suka gama secondary, tofa shikenan yaro ya gama karatu, wasu iyayan su tura yaro neman kud’i Kudu, ko sauran garuruwa, ko a kai yaro almajiranci.

Kai tsaye mu kutsa cikin labarin.

Haka ce take kasancewa a gidan Alhaji Sani Mai Goro, Babban gida ne wadda ya kasance ginin k’asa ne mai d’auke da d’akona Takwas, ko wanne d’aki da akwai mamallakinsa, Sani mai Goro yana da mata uku, Inna Suwaiba, sai Inna Khande, sai kuma Inna Indo, Inna Suwaiba ta kasance macece mai son kud’in tsiya bata da hakuri dan duk wadda ya tab’a ta gidan sai an jisu tana y’ay’a biyu Hamza, sai Binta, wacce tayi aure wajan K’auyan, sai ko Inna Khande, ita bata shiga harkar kowa a gidan da wuya ana abu a gidan ta tanka, idan ba an tab’o yaranta ba, yaranta uku Ismail, wadda suke kira da Ilo, sai Sule sai kuma Abubakar, wadda suke kira da Abu, Inna Indo kuwa y’ar rigima ce itama ga habaicin tsiya, ko baka tab’a ta ba idan tasu sai kunyi rigima da ita, itama tana da yara biyu Iro, sai Mamman.

Cikin yaran nasu Iro dana mata d’aya, Sa’ade da yaron ta namiji wadda ya fara zama saurayi, mai suna Hamisu, Hamisu baya jin magana son matan tsiya ne dashi kamar mi ga bin matan banza tun yana k’arami yaso ayi mai aure, saboda muguwar sha’awar da yake da ita, iyayan sunki mai auren sunce sai yaje neman kud’in idan ya dawo yayi auren shine ya fetsare yak’i zuwa neman kud’in, ya tsaya a gari a jan magana.

Sai kuma matar Mamman mai suna Maryama macece itama makirar gaske baka gane gabanta bare bayanta, duk abinda take ciki da ita sai yaranta mata su biyu, Bishira da Habiba suma basa jin magana ga rashin kunyar tsiya ba wadda suka ragamawa a cikin gidan koda kuwa Kakanin su ne, wadda suke d’an shakkarsa shine Kakansu Sani mai Goro.

Sai ko Abubakar shi yana da Mata d’aya shima mai suna Hadiza, itama dai y’ar rigima ce ga cika bakin tsiya, idan ta ganka da abu tofa ta kama jin haushi da hassada kenan itama sai taga tayi irinsa, tana da d’iya mace guda d’aya duk duniya tana son Na’ima ta d’ora burin duniya akan d’iyar ta Na’ima, saita auri mai kud’i kuma a birni, bata cika shiri da matan gidan ba.

Sai kuma sule wadda yanzo yaran suke kiran su Kawu kamin su kira sunan nasu, shi kuma shine kadai Allah ya d’an d’aukaka shi ya fita daga gidan yana aikinsa a can birni yana samun kud’i sosai yana da shigo a katin Kwari Baban shago ne har abun ya hab’b’aka sosai yanzu haka yana da shago sama da guda biyar sosai arzik’insa ya k’ara bunk’asa, shi yasa gidan Sani mai Goro suna ji dashi iyayansa sunsu su had’a shi aure da y’ar dangi, sai dai mai gidansa wadda ya fara bashi tsaron shigo ya bashi d’iya mai suna Bilkisu ya aura, babu yadda suka iya akayi auran, kuma ya gina gidansa a birnin Kano mai shegen kyau na gani na fad’a, yanzu haka Bilki ta haifa mai yara biyu mata sai namiji d’aya, Khairat, sai Ifteesan, sai ko Babban yayansu wadda suke kira da Ya Khaleefa, Bilkisu bata son y’an K’auye shi yasa bata cika zuwa ba tana da yawan kyauta amma tana mugun son yaranta kamar mi suma yaran sun taso cikin gata kuma suma basa son y’an K’auye sun raina so gani suke ai kamar su d’in basa da gata, Ya Khaleefa yanzu haka baya ma k’asar yana Engila yana karantar Lor ne yaro ne kyakkyawan gaske miskili ne na gidan gaba, dan duk gidansu ba wadda ya kaishi kyau, shi bashida wulak’anci sai dai baya son yawan magana idan ya fad’i magana da wuya ya maimaita ta, shi yasa K’annansa suna mugun shakkarsa.

Shi yasa da yawan yaran Bilki basu san y’an uwansu dake K’auye ba.

Su duka yaran Sani mai Goro sun tara iyali.

Shi yasa Ahalin gidan Sani mai Goro suna ji da Sule, dan ko yanzu kusan shi ke rik’e da su, danma ayyika sunmai yawa sai ya d’an dad’e baizo K’auyen ba, kuma harda had’i daya samu mace wacce bata damu da danginsa ba, nata kawai ta sani.

Sai kuma Hamza yayi aure Matansa biyu a gidan suke zaune Matarsa ta farko ita ce Aysha, wacce suke ma lak’abi da A’i, macece mai marar san hayaniya gata da kawaici, tunda ta auri Hamza ta tsinci kanta a gidan Sani Mai Goro, take fuskantar K’alu bale daban daban, saboda shigowarta gidan ta dad’e bata haihu ba, har sai da uwar mijinta ta fara yada mata magana a bisa zugar matanan gidan, suma kuma sauran mutanan gidan suka had’e kai suka jefa mata karantsa, har sai da Inna Suwaiba taba Hamza umarnin k’ara aure, ba’a dad’e ba Hamza ya sake auro Hajara y’ar garin Fachankan d’in ce itama, sai dai fa tunda Hajara ta shigo gidan A’i abubuwa suka sake chab’e mata, saboda Hajara munafuka ce ta gidan gaba, duk wani abu da tasan zata k’ara jefa tsanar A’i a zuciyar mazauna gidan tofa sai tayi, saboda ta tsane A’i tana mugun kishi da ita, ga bin Malamai da Bokaye, duk wasu kud’in Hajara da buga-bugar da take duk akan Bokaye suke k’arewa, tana zuwa gidan bata dad’e ba ta samu ciki, iya murna sunyi murna an nunama Hajara gata, inda aka k’ara taso A’i gaba da habaici, wani lokacin kwana take kuka.

Haka ta raini cikinta ta d’ora ma wannan ciki buri taso ta sami d’a namiji, sai dai Allah baiyi ba, dan ko mace ce ta haifa, duk da haka taga gata kamar mi, amma ita ba haka ta so ba, hakan yasa ta k’ara shiga Malamai da Bokaye domin haihuwa ta gaba ta samu d’a namiji, sai dai haihuwar ce tayi mata dogon zango dan ko tunda ta haifi Asma’u, wacce suke ma lak’abi da Nana, haihuwar ta tsaya cak.

A dai-dai wannan lokacin ne kuma Allah ya azurta A’i da samon ciki itama, wai wai karkuso kuga irin tashin hankalin da Hajara ta shiga a wannan lokacin, sosai Hajara ta shiga tashin hankali wadda fad’ar shi ma b’ata baki ne, sai ya kasance bata zama a gidan kullum tana kan hanyar zuwa wajan Boka da Malamai, akan duk yadda za’ai kar A’i ta haifi cikin dake jikinta, koda kowa A’in zata rasa ranta ne.

Sosai ta kashe mak’udan kud’i dankar A’i ta haifi abinda ke cikinta, a wajan A’i sosai take ganin tashin hankali tunda samu cikin take yawan wasu mugayan mafarkai masu ban tsoro, ga cikin yazo mata da laulayi mai wahalar tsiya, gashi anyi mata ture da aljanu sosai suke firgita, danma tana yawan addu’a duk addu’ar ba wani iyawa tayi sosai ba, saboda garin basu damu da ilimin ba.

A’i ta rame ta fige dan har an fara mata surutu Inna Suwaiba duk da haka bata kyale ta ba, kullum ita da Hajara suna jifanta da mugayan kalamai dan Inna Suwaiba har cewa take,

“Tunda A’i kika shigo gidan nan d’ana bai k’ara tara abun arzik’i ba, ke tunda ma kika samu cikin nan komai ya samo sai kin yamoshe mai, haba ciki sai kace wacce take rainon cikin aljanu”.

kullum idan Inna Suwaiba ta fad’i haka A’i sai dai ta shige d’aki taci kukan ta.

Da zarar dare yayi kuma babu ita bayin bacci, ba k’aramar fargitata ake ba duk don cikin ya zube, sai dai Allah baiyi ba, cikin kuwa saima wani girma da yake ita kuma tana tsotsewa ta koma kamar mai ciwon K’anjamau, a inda Hajara ta k’ara fantsama wajan Bokayanta dan taci burin itafa kodai A’in ta mutu ko kuma abinda ke cikinta ya mutu.

Sadda cikin A’i yakai watan haihuwa, a dai-dai wannan lokacin ne Hajara ta amso wani mugun asiri, tsaye take a d’akinta cikin talatainin dare, zindir take tsaye haihuwar uwarta tasa wani kasko a gabanta tana wasu irin surutai da wani irin yare, kaskon yana ci da wuta ga wani irin hayak’i dake fita ta cikin kaskon, hayak’in mai matuk’ar warin tsiya kamar na bori, wasu irin darussan tsafi take karantowa, kamin kace mi d’akin ya d’au wata irin girgiza da wasu irin koke-koke, wani irin hayak’i ne na dunk’ule waje d’aya, can Hajara ta ware idonta dayayi jawur kamar garwashin wuta, tana zare ido, kwata-kwata ba d’igon tsoro ko imani a ranta, ta bud’e baki ta ce.

“Ina so kar A’i ta haihu lafiya kodai ita ta mutu ko kuma abinda ke cikinta, danna rantse sai A’i ta bar min mijina ni d’aya”.

Tana gama maganar wannan hayak’in yabi k’ofar d’ankin Hajara ya fice kai tsaye d’akin A’i ya nufa, A’i dake kwance da k’aton cikinta bata dad’e da samun bacci ba dama hayak’in na gama shiga d’akin ya dunkule ya zama wata irin halitta mai ban tsoro, hannunsa yayi anfani dashi yayi tsayo kai tsaye goshin A’i ya nufa wani haske ya fito daga hannun aljanin nan ya shigi A’i.

Dan da nan A’i ta farka a firgice, idonta ne yayi mata tozali da wannan mummunar halitta, ba shiri ta kulle idonta tana sakin wata irin gigitacciyar k’ara, cikinta ne yayi wata irin juyi tare da muguwar murd’awa kamar mararta zata rabe gida biyu, wata irin k’ara ta k’ara saki tana juye-juye, ga muguwar halitta dake kanta.

Jin ihun A’i sai k’ara yawa yake yasa Hajara dake d’akinta tana jiran tsammani, ta rarami zaninta ta d’aura tana dariyar mugunta, cike da makirci ta fito tsakar gida, tana sakin salati tana cewa,

“kuna ina mutanan gidan nan wai bakwa jin A’i ne kamar fa nak’udarta ta tashi?”, da yake mijinsu Hamza baya nan sunje fatauci ne.

Ba shiri ta k’ara matsawa kusa sa d’akin A’i dake ihun azaba har yanzu Inna Suwaiba ce ta fara fitowa tana sakin wani shegin tsaki tana cewa “wai nikam duk an cika mana gida da karaji haba”

Hajara ce ta kalleta ta ce “wai fa kamar nak’uda take”

“Sai kuma aka ce ta damu mutane da shegen ihu, ko ko mu haka muke yi idan haihuwar tazo mana ita bazata iya yin hakurin da mukayi ba, sai rakin tsiya, ko nufinta mu d’auke mata ciwon, sadda taje ta kwanta da mijin tana jin dad’i uban wani yasa ni”

Inna Suwaiba ta idasa maganar tana kunfan baki.

Inna Khande ce ta ce “shin zamu matsa mu taimaka mata ko ko tsayawa zamuyi maganar da bata da anfani ne?”.

Ba wadda ya sake magana gaba d’ayansu suka shige d’akin A’i, dake kwance ta galabaita sosai ga mummunar halittar dake tsaye tana firgitata duk da shigowar su Inna Suwaiba, hakan baisa Halittar nan b’acewa ba, ba wadda ke ganinta sai ita A’in da kuma wacce tayi sanadiyar shigowarta d’akin.

Wani murmushin mugunta Hajara tayi tana matsawa jikin A’i sosai dai-dai kunnanta ta rad’a mata yadda ba wadda zaiji ta ce “hmm A’i kenan ke nufin zan barki ki haihu lafiya ne saura ki haifi namiji ki gaje komai ko mu?, ai inahh A’i dole yau sai kin bak’unci lahira wallahi”.

Wata irin zabura A’i tayi hawaye masu zafi na d’iga ta idonta tana bin Hajara da kallo, wani murmurshi ta sakar mata ta fara magana abun tausayi cewa take

“innalillhi A’i ki daure kin kusa sauka ki daure kinji”,

Kallonta kawai A’i take bakinta ya kasa furta komai tsabar makirci ji yadda take nuna mata, abunda ke damunta d’aya abunda zata haifa ta bari a wannan murd’and’an gida, lallai duk abunda zata haifa ta bari ba k’aramar hawala zaisha ba, shi yasa ba shiri wasu hawayen suka sake zubo mata, suna bin kumatunta.

Wata irin juyawa mararta ta sake yi wadda yasa tsabar azabar da take ji yasa ihun ma ta kasa sai dai jujjuya kai da take, ta damk’e janin dake jikinta da mugun k’arfi, sosai tasha wahala kamar zata mutu da abunda ke cikin nata sana Allah yasa ta sillab’o d’iya mace, kyakkyawar gaske su kansu Inna Suwaiba sun girgiza da ganin kwawun yarinyar kamar y’ar aljanu yarinyar, tunda ta fito duniya ko tari batai ba bare kuka, sai ido da take bin su dashi Hajara ita kanta ta girgiza dan har kusan sakin layin tayi, taso abunda ke cikin ne ya mutu amma jin shuru yayi yawa ta b’angaran A’i yasa suka kai dubansu gareta, ba shiri suka saki salati ganin babu alamar rai a tare ita, jikinta ya saki idonta na kallon sama fuskarta na fitar da wani annuri kamar tana murmushi, Hajara kuwa wani irin mashahurin farin ciki ne ya ziyarce ta, ganin cewa fa A’i rai yayi halinsa.

Kangin Rayuwa 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×