"Ibteey kiyi sauri ku tafi kinga rana har ta bud'e bana so kiyi dare" Umma ta fad'a tana fitowa daga d'aki da leda a hannun ta, mik'ewa tsaye Ibteey tayi ta gyara mayafin ta tace, "To Umma ai na shirya". "Ina Jidda?". "Umma kin san jiya anyi ruwa gwara ta huta sabida yanayin jikin ta." D'an jim Umma tayi tana kallan Ibteey kafin tace, "Bana san fitar ki ke kad'ai". D'an murmushi Ibteey tayi tace, "Babu komai Umma ki tayi min addu'a, na tafi kar lokacin sallah yayi" ta fad'a tana. . .