Skip to content
Part 4 of 5 in the Series Kasaitar So by Nana Haleema

“Ibteey kiyi sauri ku tafi kinga rana har ta bud’e bana so kiyi dare” Umma ta fad’a tana fitowa daga d’aki da leda a hannun ta, mik’ewa tsaye Ibteey tayi ta gyara mayafin ta tace, “To Umma ai na shirya”. “Ina Jidda?”. “Umma kin san jiya anyi ruwa gwara ta huta sabida yanayin jikin ta.” D’an jim Umma tayi tana kallan Ibteey kafin tace, “Bana san fitar ki ke kad’ai”. D’an murmushi Ibteey tayi tace, “Babu komai Umma ki tayi min addu’a, na tafi kar lokacin sallah yayi” ta fad’a tana niyar ficewa daga falon.

“Ibteesam!” Umma ta kira ta daga baya cikin sanyin murya, juyowa tayi tace, “Na’am Umma na”. “In dare yayi ki kwana kya dawo gobe kar ki tawo da daddare kinji ko?”. “To Umma insha Allah sai na dawo” ta fad’a tana ficewa Umma ta bita da addu’a. 

A hankali take takawa ta fito daga gidan tana D’an kalle-kalle, sunkuyar da kanta tayi tana murmushi ganin wanda take so ta gani sun had’a ido, shima murmushin yayi ya nufo ta yace, “Ibteey na sai ina?” Ya tambaya cikin sanyin murya yana mata murmushi. D’an d’agowa tayi ta kalle shi kafin ta sake sunkuyar da kai tace, “hotoro zanje gidan Dada.”

Murmushi yake jifan ta dashi yace, “Ina Jidda zaki tafi ke d’aya?”. “Kasan anyi ruwa ga yanayin ciwon ta ya saka nace a k’yale ta.”

Gyara tsayuwa Khalid yayi yace, “Bana san fitar ki ke kad’ai kin sani ko?”. “Na sani yanzu zan dawo ba jimawa zanyi ba” ta fad’a a d’an k’agauce dan ta gaji da maganar.

“To sai kin dawo” ya fad’a har lokacin idon sa a kanta, murmushi tayi kawai ta fara tafiya da d’an sauri dan so take ta isa titi da wuri ta samu mota, kallan ta yake har ta b’acewa ganin sa kafin ya d’auke kai ya kalli wanda ya tsaya a gefen sa yana kallan sa, “Mtswww munafuki meye?”. Ya kwashe da dariya yace, “Wannan kallo da kake binta dashi Khalid ai sai ta fad’i.” “Hmmm yarinyar ce akwai kyau wallahi” Khalid ya bashi amsa yana lumshe ido tare da bud’ewa. 

“Hmmm ai tunda har tana sanka ai zance ya k’are Khalid in nine kai wallahi da yanzu nayi batun aure dan barin irin su Ibteey a k’asa wani minister na zuwa zaiyi wuff da ita.”

Khalid ya kalli abokin sa kafin yayi murmushi yace, “Kai kana tunanin akwai wanda Ibteey zata so bayan ni? Kai kasan san da take min kuwa?.” “Na sani mana kai kuma ba irin wannan san kake mata ba.”

D’an yatsine fuska yayi ya saka hannu d’aya yana sosa kansa kafin yace,”Ina santa mana amma gaskiya auren mace mai qiba baya tsari na”. “Haba Khalid kasan da hakan kuma kake b’ata mata lokaci?”. “Kai yarinyar tana so na ne over in yanzu nace mata ba auren ta zanyi ba tsaf zatayi ciwo, zo muje gida” yana gama fad’ar hakan yayi gaba shima yabi bayan sa.

Ibteesam kuwa tafiya take a hankali cikin nutsuwa har ta fita bakin titi duk da tazarar su babu yawa, a kan titin ta tsaya tana kallan wanda zaiyi hanyar da zata bi tana kuma kallan agogon hannun ta, wani mai napep d’in ta hango babu kowa ta saka masa hannu ya tsaya tace, “Hotoro bos stop”. “Hajiya kud’in ki dari biyu”. “Zan bada dari uku amma drop”. “To hajiya” yana gama fad’ar hakan ta shiga yaja napep d’in. 

Tun daga kan gada ana traffic ne har danger state road, “Hajiya ko zamu bi ta baya ne nan traffic yayi yawa wallahi sai mu kusa la’asar a nan wajan”. “Eh muje d’in naga wajan a cakud’e.” Juya kan Napep d’in yayi yabi k’asan gada suka wuce.

Tafiya suke hankalin ta na kan titi shi kuma yana kallan titi yana tuk’in sa a hankali, parking taji yayi sai a lokacin ta dawo daga duniyar tunanin duniyar da ta tafi dan a zahiri kallan titi take amma a zuciyar ta wani tunanin take daban ta kalle shi tace, “Lafiya ka tsaya?

Juyowa yayi ya kalle ta yayi murmushi, “Hiii” aka fad’a ana kallan ta daga k’ofar Napep d’in, zatayi magana kenan aka fesa mata hoda a fuska ta lumshe ido ta zube akan kujerar, Wizzy ya kalli mai napep d’in yace, “good job” ya fad’a yana yi masa jinjina. 

Murmushi mai napep d’in yayi yace, “Godiya nake Oga”. Cak Wizzy ya d’auke ta ya saka ta a mota ya d’auki hanya a guje.

*****

Tsaf ya shirya cikin dogon jeans black mai zanen fari ya saka riga fara mai ma6allai a gaban rigar ya kawo farar picap ya saka a kansa,  wayar sa ya d’auka tare da jakar sa ta tafiya ya fito daga d’akin nasa, a hankali yake sakkowa daga saman yana yi yana kallan agogo dan ganin ya kusa missing flight, cak ya tsaya tare da komawa baya yana kallan Amina da take zuba wani ruwan magani a cikin miyar agusi d’in da take ajjiye a akan dining table d’in, wani irin takaici ne ya kama Zaid tsanar ta ta sake yi masa dirar mikiya lokaci d’aya, a fusace yake sakkowa daga saman yana wani irin wuci kamar zaki, ganin sa ya saka ta firgita tayi baya da sauri tana b’oye maganin a zanin ta, bai jira wani abu ba yana k’arasowa ya d’auki miyar ya watsa mata a jikin ta, ihu Amina tayi sabida miyar da zafi tana zazzage rigar ta, sakin flasks d’in yayi a kan tiles d’in kafin ya juyo a fusace ya nuna ta da yatsa yace, “In kika sake wani abun ya sami mahaifina zan iya kashe ki” ya fad’a yana zaro mata manyan idon sa wanda suka koma jajaye sabida b’acin rai da k’unar zuciya.

Daddy da ya jiyo ihun Amina ya fito da sauri ya sakko k’asan, cak ya tsaya yana kallan ta jikin ta duka miya ga Zaid ya saka ta a gaba yana nuna ta da yatsa, “Zaid!” Daddy ya kira shi a fusace yana kallan sa da b’acin rai a bayyane a fuskar sa. “Zaid meyesa baka da kirki ne? Me yake damun ka? Uban me Amina ta tare maka ne a gidan nan ka sako ta a gaba haka eyeee,? Inda mahaifiyar ka tana raye wani yake mata irin abinda kake mata zaka ji dad’i?” Daddy ya fad’a cikin fad’a yana nuna shi da yatsa. Kallon sa Zaid yayi yana jin wani irin b’acin rai yana taso masa daga k’asan zuciyar sa tsanar Amina kuwa dad’a nitso cikin zuciyar sa, a kanta kad’ai Daddy yake masa fad’a har haka ya za’ayi bazai tsane ta ba, “Bata hak’uri” maganar Daddy ta katse masa tunani. 

Da sauri ya d’ago kai ya kalli Daddyn nasa jikin sa ya soma wani irin rawa dan shi a rayuwar sa sam bai san wani abu wai shi hak’uri ba, bai tab’a bawa wani hak’uri ba sai dai shi a bashi koda shine bashi da gaskiya k’arfin ikon sa yana sakawa a bashi hak’uri, “Kayi abinda nace Zaid” Daddy ya sake fad’a cikin murya mai amo yana kallan Zaid, Saurin dafe kan sa yayi yana jin wani irin jiri yana neman d’aukar sa, jikin sane ya soma wani irin rawa kamar an jona masa wutar lantarki, “Ka bata hak’uri Zaid in ba haka ba zaka had’u da b’acin raina wanda baka tab’a gani ba.”

Bakin sane yake rawa yana so yayi abinda Daddy yace amma ya kasa bakin sa yayi masa wani irin nauyi wanda bai tab’a yin irin sa ba, “baza kayi abinda nace bane Zaid?” Daddy ya sake fad’a a tsawace yana kallan sa da b’acin rai.

“I’m….so..rr…y” ya fad’a a rarrabe cikin rawar murya, yana fad’ar hakan ya wani runtse ido kamar wanda ya aikata babban sab’o yana yana girgiza kai, “Abuja” abinda ya iya fad’a kenan sanyayeya juya a fusace ya fita daga falon.

“Musa! Musa!! Musa!!!”. A guje ya Musa ya tawo jikin sa na rawa dan yadda yaji muryar Zaid d’in ba k’aramin rud’a shi yayi ba, “Na’am gani” ya fad’a yana dan rank’wafawa, bai magana ba sai bud’e motar da yayi kawai ya shiga ganin hakan shima Musa ya shiga suka nufi hanyar airport, tunda suka shiga yake jan tsaki fuskar sa a tamke kamar koda yaushe sai wuci yake yana girgiza kai, in ya tuna ya bawa Amina hak’uri sai yaji kamar yayi hauka sabida takaici da bak’in ciki.

Koda suka k’arasa baiyi magana ba ya bud’e motar ne kawai ya fice ya shiga ciki, da kallo Musa ya bishi kafin yace, “Oh albasa batayi halin ruwa ba”.

Daddy kuwa yana fita ya matsa kusa da Amina ya rik’e hannayen ta duka biyun yace, “Kiyi hak’uri dan Allah insha Allah hakan baza ta kuma kasancewa ba, na rasa abinda yake damun Zaid a kanki amma zan kamo bakin zaren kada ki bari abinda ya faru ya dame ki dan Allah badan ni ba”. Share hawayen da suka ciko mata ido tayi ta d’an yi murmushi tace, “Babu komai kar ka damu, da ka sani baka yi masa tsawa ba kasan yanayin jikin sa yanzu sai hakan ya tayar masa da ciwon sa.”

Ajiyar zuciya Daddy yayi dan shima tunda yayi masa tsawar yaga yadda yanayin sa ya canja jikin sa yayi yake tsoron Allah yasa kada hakan ya zama silar tashin ciwon Zaid, “dole ne na tsawatar masa sabida kar ya sake kuskuren aikatawa nan gaba  in yaga yayi ba’a yi masa tsawa ba gobe ma kuma yi zaiyi, babu abinda zai same shi ki kwantar da hankalin ki.”

“Duk da haka sabida yanayin ciwon sa ka daina masa irin wannan tsawar.” “Amina kowa fa yana da fushin nan, kowa yana da zuciya amma mu muna sarrafa ta yadda ya kamata shi waye da bazai sarrafa zuciyar shi ba? Komai fushi haka rayuwa zatayi,? Dole a dinga tsawatar masa yasan ba komai ake samu ta fushi da zafin zuciya ba, kiyi hak’uri dan Allah.

“Haka ne, bara naje nayi wanka na canja kaya na” ta fad’a tana zame hannun ta daga rik’on da yayi mata ta wuce d’akin ta tana wani irin murmushi mai kama da murmushin nasara.

Wayar sa da tayi k’ara ya saka ya ciro ta daga aljihu ganin mai kiran ya sanya gaban sa fad’uwa dan indai kaga kiran sa to ba alkhairi bane ba, “Hello Yaya” ya fad’a a sanyaye. “Ka rik’e hello d’in ka Abubakar, ashe d’an ka bashi da mutunci? Ashe bayan shaye-shaye har da daban ci yake yi bamu sani ba? Tsabar tsinancewa irin ta Zaidu mu zai saka y’an daba su yiwa dukan tsiya dan kawai munzo gidan su,? Sun fasa min baki shi kuwa Bala ma sun targad’a shi a hannu kaga kenan nan gaba kashe mu zai saka ayi”. Shiru Daddy yayi yana sauraran sa jikin sa duk yayi sanyi, “To sai ka aiko da kud’in magani tunda d’an iskan d’anka ne yayi mana wulaqanci.”

Ajiyar zuciya Daddy yayi yace, “Allah ya baku hak’uri insha Allah zan kawo shi ya baku hak’uri.” “Ku rik’e hak’urin ku bama so amma dole ka aiko da kud’in magani”. “To zan turo insha Allah”. “Ka kyautawa kanka” ya Fad’a yana katse kiran.

Ajiyar zuciya Daddy yayi jiki a sanyaye ya koma sama yana tunanin halayyar Zaid, ya rasa a ina ya d’auko wannan halayyar tasa.

Saukar sa a airport na Abuja bai jira driver ba kawai ya d’auki drop d’in taxi ya tafi gidan su da yake mai tama, a k’ofar gidan ya sauka ya bawa mai taxi d’in kud’in sa shi kuma ya nufi gate d’in gidan yayi knocking, dake mai gadin gidan yasan da zuwa sa yayi sauri yazo ya bud’e yana yi masa sannu da zuwa, a ciki ya amsa kafin ya shige cikin gidan yana wata irin tafiya cikin k’asaita, direct inda yake mallakin sa a gidan ya nufa ya bud’e ya shiga, falon yana nan tsaf a gare sai k’ura kad’an, d’akin ya wuce ya ajjiye jakar hannun sa ya fad’a band’aki, wanka yayi tare da alwala ya fito ya shirya cikin jallabiya kofi colour mai hula a baya, sallah ya tayar bayan ya idar ne ya fito ya shiga kitchen.

Kettle ya kunna ya dafa ruwan zafi ya had’a tea ya dawo falo ya d’an kad’e inda zai zauna kafin ya zauna ya fara shan tea d’in a hankali, sai da ya kammala sannan ya d’auki key d’in mota ya sauko dan ya bawa Mai gadi umarnin a wanke masa motar sa da take gidan, yana fitowa ya shiga motar aka bud’e masa gate ya fita ya nufi unguwar Zone 6.

A dai-dai wani d’an gida plat mai kyau ya tsaya tare da danna horn d’in motar tasa, mai gadin gidan lek’o yaga motar da bai sani ba sai ya kulle k’ofar ya fito, sauke glass d’in Zaid yayi ya kalli mai gadin tun kafin yayi magana yace, “Kace mata Zaid ne” ya fad’a a dak’ile yana Kawar da kansa gefe.

Cike da mamaki mai gadin yake kallan sa ganin ko irin sallamar nan ma babu sai wata magana da yake yi a gadarance kamar gidan sa, bai musu ba ya juya ya shiga cikin gidan jim kad’an ya dawo ya bud’e masa gate d’in ya shiga cikin gidan, parking yayi ya kashe motar ya fito ya nufi k’ofar da zata sada ka da falon gidan, da sallama ya tura k’ofar ya shiga yana kallan falon, da fara’a ta amsa ta mik’e tana fad’in, “Ga Zaid sannu da zuwa” ta fad’a cikin nuna zallar farin cikin ta da nishad’i. 

Sakin fuska yayi kad’an ba tare da yayi murmushi ba ya zauna a kan kujera tare da d’ora k’afa kan d’aya yace, “Ina wuni”. “Lafiya lau Zaid ya gida ya Daddyn naka?”. “Lafiya” amsa yana kallan tv dake gaban sa. “Masha Allah, Zahra kawo masa ruwa da abinci” ta d’an d’aga murya ta fad’a. “No Mom ruwan dai but abinci kam I’m okay.” “Aikam baka isa ba abinci kam sai kaci shi, kai ka isa ma kazo ka tafi baka ci komai ba.” 

Shiru yayi baice komai ba wacce aka kira da Zahra ta fito cikin nutsuwa ta ajjiye abincin a gaban sa tace, “Ina wuni Yaya Zaid”. D’ago kai yayi ya kalle ta kafin ya d’auke kai yace, “Ya karatu?.”  “Alhamdulillah” daga nan sukayi shiru babu wanda ya sake magana. Mom ta bud’e abincin ta zuba masa tace, “To bismillah”. Kallan abincin yayi jellop d’in pasta da nama a cikin ta tayi masa kyau a ido sosai hakan ya saka ya d’auki spoon ya dibi kad’an ya kai bakin sa, a hankali yake taunawa ya sake d’iba ya ci sai ya ajjiye spoon d’in jin wayar sa na vibrating, d’aukar wayar yayi tare da cewa, “okay in ta farka ku bata abinci naje gidan Mom sai zuwa gobe zan shigo” ya fad’a bayan ya saka wayar a kunnen sa.

Bayan ya kashe wayar Mom ta kalli d’an k’anwar tata tace, “ina kazo a garin namu?”. “Nan kawai” ya bata amsa a takaice. “Lah aikam naji dad’i takanas ka tawo Abuja sabida ni? Kai Allah yayi maka albarka ya nuna nuna min auren ka.” Murmushin gefen baki yayi kad’an baice komai ba, “yaushe zaka kawo min sirikar tawa?”. Kallan ta yayi kafin ya d’auke kai yace, “hmm Mom kenan.”

Murmushi tayi tace, “Ina zaka je goben kuma?” Ta fad’a tana kallan sa cikin kulawa, ajiyar zuciya yayi kafin yace, “Kaduna”. “Allah ya kiyaye” a ciki ya amsa da amin ya mik’e ya kalle ta sosai kafin yace, “Mom kin rame har yanzu tunanin ne?” Ya tambaya cikin kulawa duk da ba ita yake kalla ba. “Hmmm Zaid kenan yau shekara sha takwas ban sake saka yarinya ta a ido na ba, ta mutu ko tana raye Allah ne ya sani” ta k’arasa fad’a a sanyaye.

“Mom addu’a ai itace magani ba tunani ba, dan Allah ki daina saka tunani a ranki Allah ya bayyana miki ita.” “Allah ya biye bakin ka Zaid, da tana nan ai da auren ka zan bata kaga daman sunan Maman ka gare ta” ta fad’a da d’an murmushi tana kallan sa, “Mummy kenan, Allah yasa a ganta d’in” ta amsa da amin shi kuma mik’e tsaye, “Badai tafiya ba?” Ta fad’a tana hararar sa. “Eh Mom akwai abinda zan zana in na koma gida” ya fad’a tare da fito da kud’i masu yawa ya ajjiye mata a gefen kujera ya fara tafiya ta biyo bayan sa har bakin motar sa sukayi sallama tare da godiya.

Kano

Sanye take da blue black din hijjabi har k’asa hannun ta rik’e da wayar ta tana tafiya a harabar gidan, Amina kenan mata a wajan Ambassador Abubakar dadtijuwa mai jikin yara dan in ka ganta baza ka d’auka tana da shekaru ba sabida yanayin jikin ta na fulani, ganin ta ta fito Musa yayi saurin bud’e mata mota ta shiga baya suka fita daga gidan.

Gidan Uncle Sani suka nufa dake cikin unguwar court road suka shiga gidan nasa mai kyau, yana parking ta fito ta kalle shi tace, “Musa ka jira ni yanzu zan fito” bata jira amsar shi ba ta shiga cikin gidan da sallama.

Dukkan su suna zaune a falon da alama ita ake jira, “Haba Amina tun d’azu ake jiran ki sai yanzu kika k’araso?” Wata mata ta fad’a da alama itace matar Uncle Sani dan tana zaune a kusa dashi, “Kuyi hak’uri wancan d’an banzan yaron ne ya b’ata min rai wallahi shiyasa jikina duka babu kuzari” ta fad’a tana zama a kan kujera.

Saifullahi k’anin Daddy yace, “wannan yaron da zan samu dama wallahi sai nayi masa yankan rago” ya fad’a yana wani irin had’a fuska sabida takaici. “Ai yau dole a samu mafitar da zamu kawar da yaron nan kafin mu koma kan uban sa, in muka fara gamawa da uban munyi a banza dan ko kwabo baza mu samu a gadon sa ba amma in muka kawar da Zaid d’in daga baya muka kawar da Uban shikenan ciki lafiya baka lafiya” Uncle Bala ya fad’a yana kallan su gabad’ayan su.

Hajiya Batula ta gyara zama tace, “Ni a shawara ta me zai hana mu had’a auren sa da Eman kaga ta hanyar ta zamu samu komai ya shiga jikin sa sosai, misali wanda muke so a saka masa a d’aki ai nasan dai bazai hana ta shiga d’akin sa ba tunda matar sace, ta wannan hanyar zamu gabatar da komai cikin tsari”. “Ehhh tabbas wannan shawara ce mai kyau amma shi yaron zai amince da auren tane? Kun san halin sa fa” Uncle Saifu ya fad’a. 

“Zancen bazai amince ba ai wannan bai taso ba indai mukayi niya sai munyi ko yana so ko baya so,  wannan sharawa tayi da ita kuma za’a amfani dole a aura masa Eman ko yana so ko baya so, ta hanyar ta zamu samu dukkan abinda muke so dan a hankali zamu saka ta dinga d’auko mana takardun kadarorin su kafin mu idda nufin mu a kan su.” Uncle Sani ya fad’a cikin gamsuwa da maganar matar sa.

Eman dake zaune  a wajan yarinya y’ar shekara ashirin da hud’u kana kallan ta kaga jinin su Daddy sabida zubin su da ta d’auko, wani sanyin dad’i ya kama ta ta sunkuyar da kai tana murmushi tana hango ta suna zuba love ita da Zaid dan tun ba yanzu ba tana san Zaid kawai tana dannewa ne sabida wulaqancin sa.

<< Kasaitar so 3Kasaitar so 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.