Ta kara kallon gidan cikin tsananin mamaki da daurewar kai da al'ajabi.
Ta kara daga takardar hannunta ta duba da kyau, kuma a karo wanda yafi na shurin masaki, ta dai ga lallai da gaske dai shine gida mai lamba ta tamanin da biyar a cikin unguwar Filemmu a cikin garin Keffi.
Gidane gashi nan dai gashi nan, babu yabo babu fallasa za ace. Amma ga wadda ta tashi a tsakanin gidajen Aso Rock, Maitama da su Wuse a garin Abuja, take kuma zaune a babbar unguwa a cikin birnin Lagos, wannan unguwa ce ta talakawa, talakawan ma na. . .
I luv ur books soo much