Skip to content
Part 22 of 26 in the Series Kauthar by Jeeddah

Ta kara kallon gidan cikin tsananin mamaki da daurewar kai da al’ajabi.

Ta kara daga takardar hannunta ta duba da kyau, kuma a karo wanda yafi na shurin masaki, ta dai ga lallai da gaske dai shine gida mai lamba ta tamanin da biyar a cikin unguwar Filemmu a cikin garin Keffi.

Gidane gashi nan dai gashi nan, babu yabo babu fallasa za ace. Amma ga wadda ta tashi a tsakanin gidajen Aso Rock, Maitama da su Wuse a garin Abuja, take kuma zaune a babbar unguwa a cikin birnin Lagos, wannan unguwa ce ta talakawa, talakawan ma na tilis!

Ta juya tana kara karewa unguwar kallo, kwatoci da kwalbati ne kawai ta ko’ina, wani irin wari da hamami ya cika unguwar har yana sanya kanta juyawa. Ta yamutse fuska cikin wani irin yanayi.

Idan ba sa’a ba dai gaskiya Anty Aisha kuskuren gida tayi, watakila mai binciken ne bai bincika mata da kyau ba. Amma ta yaya za ace mahaifiyarta ce take zaune a wannan kaskantaccen waje? Ji take yi kamar ta juya baya, ko ta kira Anty Aishar domin ta kara tabbatarwa, wata zuciyar kuma tana hanata.

Haka ta daure ta taka kafarta da take saye cikin flat sandal na Coco and Chanel baki, wanda ya gama wankewa da ruwan kwata da cakwali saboda daga can bakin titi aka sauketa. Mota mai kafa uku ma bata iya shiga wannan waje balle ainihin mota, sai dai kuwa mashin wanda ita kam ba zata taba hawa ba. Tuni ta gama kudirewa a cikin ranta idan ta fita daga nan zata jefar da takalmin ta nemi wani.

Ta kai hannu cike da kyankyami ta tura kyauren gidan wanda tsatsa ta ci iya cinta har ta banbareshi daga jikin bango ya zamana kara shi kawai aka yi, sai aka daura wani tsumma daga sama ya zama kamar labule aka yiwa kofar gidan.

Data saka kafarta cikin gidan kuma sai taji kanta har juyawa yake yi. Tarkace da shirgi babu kalar wanda babu. Gabadaya tsakar gidan bata wuce taku goma ba zuwa sha biyu, kuma gabadaya yashi ne malale babu ma zancen suminti. Dakuna biyu ne a jere, su dukansu babu ma kofa suma sai labule aka musu da buhu.

Murya a shake ta kwala sallama, har cikin ranta tsabar mamakine dankare. Ashe dama da ake cewa akwai wadanda suke rayuwa a cikin irin wannan yanayin da gaske ne, ba kanzon kurege ba? Ta jinjina Girma da Kudira irinta Ubangiji mai Girma! Lallai da ake cewa Allah daya, gari bamban.

A ranta kuma ta kudirce irin taimako da tallafi da zata bawa mazauna wannan gida dama wannan unguwa baki daya.

Ta kara yin sallama a karo na biyu ganin ba a amsa ba tana kara duba gidan.
Wata mata ta daga labulen dakin ta fito, da dankwalin atamfa a hannunta tana kokarin rufe kanta daya cike da furfura yayi wani cukus-cukus kamar gidan tsuntsaye.

Sai suka yi cak! ita da Kauthar din suna kallon-kallo. Babu wanda ya iya motsin kirki a cikinsu su duka.

Domin kuwa idan har abinda idanuwanta suke gani gaskiyane, kuma ba gizo idanuwan nata suke yi ba, to tabbas kuwa Adidat ce take gani tsaye a gabanta. Amma Adidat ko kuwa Maman Adidat din? Domin Adidat din data sani a baya sam bata yi kama da wannan ta gabanta ba.

Wannan ta gabanta, a tsufe take, a yamutse, bata tunanin ko Hajiya Hadiza zata nuna mata tsufa.

Wani zani ne na atamfa a jikinta saboda tsabar kodewa da yayi, ko kalar atamfar ba zaka iya fadi ba, ta dora wata shirt a saman zanin, wuyan rigar yayi mata wani bororo saboda ya mata yawa, sai kokarin daure dankwalinta take yi amma ta kasa yin hakan saboda yadda jikinta yake rawa.

Kauthar ta kara juyawa tana kara kallon gidan da matar, wadda ta samu karfin gwiwar iya fara takawa ta karasa gaban Kauthar.

Hawaye suka cika mata ido, ta daga hannu favyake rawa tana nunata, “wa… na… ke… gani kamar…. Kauthar?”

Ta jinjina kai tana kokarin sakin murmushi amma yaki fita. Musamman da taga Adidat din tana layi da tangadi kamar wadda ta gama shan giya ta bugu, tana neman faduwa kasa. Tayi gaggawar sanya hannu ta tarota, suka fadi kasan a tare, tana jikinta. Yadda kasan jaririya da mahaifiyarta, haka suka yi, Adidat din akan cinyar Kauthar wadda har a lokacin kallon rashin yarda da mamaki take jifanta dashi.

Hawayene suka cika mata idanu suka fara zuba suna diga akan cinyar Kauthar, murya cike da kuka da dumbin danasani da nadama take ce mata, “am sorry Kauthar! I’m so sorry daughter, ki yafe min!”

Kukan da take yi ya cika gidan, sai ga wasu yara matasa biyu, mace da namiji sun daga labulen daki sun fito suna tambayarta lafiya?

Kauthar ta bisu da kallo cikin sanyin jiki, daga ganinsu babu tambaya kaga tsatson Adidat. Macen ta fi namijin girma da alama itace babba.

Adidat na kuka matsananci ta kamo Hannuwansu ta hada dana Kauthar, muryarta bata fita, yaren ma hadawa take da turanci da Hausa da Gade (yaren mutanen Nupe da Ebira), Kauthar bata fahimtar abinda ke fita daga bakinta. Amma da alama su sun fahimta.

Nan da nan sai taga murna da farinciki sun dabaibayesu, suka rungumeta suna tsallen murna.

Kafin kace me sun rikice da yare, sai ga makota sun fara shigowa suma suna tambayar abinda yake faruwa. Duk dai bayani daya ne ake musu cikin yarensu wanda tasan baya wuce ace diyar Adidat ce tazo, don kuwa da an musu bayani sai taga suma suna murna, wasu suna hamdala har da masu hadawa da guda.

Samu suka yi suka tattagi Adidat, macen da taji suna kira Zainab ta kamata suka shiga dakin da suka fito.

Kawai sai taji wasu hawaye suna fita daga idanuwanta data ga wajen da suke rayuwa. Babu komi a dakin sai buhun suminti da aka shimfida wanda shi a karan kanshi ya gama dagargajewa ya ji jiki, dakin babu ko filasta, yashi ne kawai.

Haka ta duzguna ta zauna, tana kallonsu wadanda suke ta rawar jiki har sun rasa abinda zasu dauka su bata.

Adidat ta kunce habar zaninta ta zaro kudi ta mikawa Yusuf tace yaje ya samo ruwan sanyi da lemu, ta daga hannu da sauri tana niyar cewa a’ah kada su damu kansu, amma Adidat din ta hana.

Haka ya fita ya dawo babu jimawa da lemun fanta na kwalba, ruwa kuma ba a samu na gora ba sai na pure water. Ita a kasheta ma ba zata iya cewa ga lokacin data sha fiya water ba, ta cira ledar ta fara sha don kuwa ko babu komi tana jin kishirwa.

Nan da nan kuma sai ga yan’uwa da dangi sun fara sallama a gidan da kwanukan abinci iri-iri, kafin kace me, gida ya cika ya tumbatsa. Data duba hagu da dama taga dai wai duka wadannan yan’uwan mahaifiyarta ne, sai ta samu kanta da kokawa. Ashe tana da dangi itama, ta rayu kamar wata marar galihu?

Sosai ta ci abinci, zuwa bayan la’asar mutanen sun fara tsagaitawa. Wata ta aika da katifa aka kai mata, anan dakin aka shimfidata aka shimfida wankakken bed sheet. Tana shingide akan katifar, Adidat kuma da su Zainab suna zaune daga kasa suna cin abincikan da aka kai suna hirarsu sama-sama wadda yawanci tambayar Kauthar ya take ne da sauransu. Ta kula kwata-kwata bata tambayeta kowa ba daga gida, itama sai bata yi mata hirar ba.

Kallonsu take yi cike da tausayi, yadda suke cin abincin hannu-baka-hannu-kwarya, kamar wadanda suka kwana suka yini da yunwa.

Mamaki take yi akan irin rayuwar da suke yi, tambayoyi fal zuciyarta da ranta, amma ta kasa furtasu.

Sallamar namiji suka ji daga tsakar gida, nan da nan taji su duka sun nutsu, duk wannan walwala da hira da suke yi ta dauke dif kamar daukewar ruwan sama.

Tayi mamakin wanda ta gani ya shiga gidan, AbdulFatah ne ya shiga yana rike da sanda ta marassa kafafu, kafarshi ta dama a yanke take.

Ya shiga gidan fuska a matukar cune yana muzurai da harare-harare. Zainab da Yusuf suka tashi suka je suka durkusa a gabanshi suna gaidashi. Ya amsa fuska ba yabo ba fallasa, idanunshi kur kan Kauthar da Adidat.

Yare ya fara rerawa Adidat cikin alamun tambaya, ta amsa tana nuna Kauthar. Ta fahimci zancen har Mahaifinta ya taba don taji suna ambatar sunanshi.

Sai da suka gama Adidat ta kalleta da dan murmushin yake a fuskarta, tace, “ki gaishe da mahaifinki Kauthar, babansu Zainab ne”

Ta tashi itama kamar yadda taga su Zainab sunyi, ta durkusa ta gaidashi, ya amsa da kyar kafin ya cangala ya shige daya dakin.

Adidat ta dan kalleta lokacin data koma dakin ta zauna a gefen katifa, tace, “kada ki damu da shi kinji? Haka yake gabadayanshi.”

Murmushi kawai tayi ta dan jinjina kai.

Adidat ta tashi ta dauki kwano daya daga cikin sauran kwanukan abincin da suka rage, ta bi bayanshi dasu.

Tana ji suna ta zabga yare wanda da alama dai fada ne jin yanda muryarsu take hawa da hauhawa, tun suna yi a hankali wadda Adidat din ce baka jin muryarta sosai sai kadan-kadan, har dai itama ta bude murya ta fara fada. Sai taga su Zainab sun nuna ko a jikinsu, abincinsu ma suka cigaba da ci hankali kwance. Don haka itama sai ta kawar da hankalinta daga kansu.

Hankalinta ya koma ga AbdulMalik kuma, ko ya yake? Shi da kanshi ya kaita airport da safiyar ranar. Yaso kwarai yayi rakiyarta, ta nuna mishi ita kadai take so taje, bashi da zabi wanda ya wuce ya kyaleta taje din.

Tasan yana can yana zuba idon son ganin kiranta tunda ta mishi alkawarin tana sauka zata kirashi.

Ta laluba cikin jakarta ta ciro wayarta ta bude. Illa kuwa ta ci karo da tarin missed calls dinshi da sakonni, ta samu kanta da murmusawa a tausashe, dama tasan za a rina.
Bata yi wata-wata ba ta maida mishi kiran. Tana karata a kunne ta jiyo muryarshi kamar mai jira,

“Ai nayi zaton har kin manta dani kuma Kauthar!”

Tayi yar dariya a tausashe, “in manta da kai kamar yaya Yaya Abdul? Ai kaima kasan fa hakan ba zai taba yiwuwa ba!”

Yace, “ai alamun naki ne suka nuna hakan. Ke da kika yi mun alkawari kuma kika ki cikawa”

Tace, “to yanzu dai naji duka na dauki laifina, kayi hakuri”
Tana jin sautin murmushin daya saki, “naji, na karba, na kuma yafe miki”
Suka saki yar dariya a tare.

Bai bari ta sake cewa komi ba ya tareta da, “daga jin muryarki dai nasan an dace?”
Ta gyada kai tana murmushi kamar yana ganinta, “Alhamdulillah kam, gani a gaban Mommy da sauran kannena.”

Shima ya tayata murmushin, zata iya rantsewa ma wanda yafi nata fara’a da jin dadi, don kuwa murnar tashi ta gaza boyuwa, yace, “Alhamdulillah, Ma shaa Allah!! That’s good, great, Alhamdulillah! Kin same su lafiya?”

Ta jinjina kai tana karewa dakin da suke zaune kallo, gefe daya daga jikin bango tururuwa ce tayi dandazo sahu-sahu suna dibar sauran abincin dasu Zainab suka zubar wajen ci,

Bakinta ya furta “kowa lafiya lau, duk suna gaisheku kuma” ba don abinda take so tace kenan din ba.

So take ta mishi bayanin halin data tsincesu, so samu ace kada su kara wayar gari a cikin wannan gidan. Amma idan ta tuna ko dama can a hakan suke raye ba tare da wata matsala ba, sai taga don karin wasu yan kwanaki ai ba zai damesu ba. Don haka tayi shiru.

Sunyi hira dashi sama-sama har sai da wayarta ta fara mata kashedin babu batiri, sannan suka yi sallama dashi.

Ta kashe wayar gabadaya ta juya tana tambayar Zainab inda za a kai mata cajin waya.
Ta bata amsa da sai dai ta jira zuwa dare idan an tada inji gidan ko wanene? Sai ta kai mata, don unguwar ko wuta babu. Ta jinjina kai kawai, ba don ta natsu da jin hakan ba.

Da dare ma haka aka dinga shiga da kwanukan cin abinci gidan. Ta samu tuwon shinkafa lafiyayye da miyar ridi, yaji nama da kifi da ganda, wanda aka kai daga gidan Yayan mahaifin Adidat.

Don gajiya kam tana dauke da ita sosai. Da so samu ne ta watsa ruwa mai dumi a jikinta, ta bi lafiyar katifa ta kwanta. Amma tasan hakan ba zai yiwu ba. Tun shigarta bandakin gidan na farko, bata kara mararin lekawa ba. Da kyar ta iya tsuguno tayi abinda zata yi tayi alwala tayi sallah. Tsakaninta da Allah ba zata iya yin wanka a ciki ba. Don haka da aka gama musu shimfida anan tsakar gidan aka sanya gidan sauro, ita da Adidat suna kan katifa, Zainab kuma tayi shimfidarta a kasa, Yusuf kuma ya fita waje wajen matasan unguwar. Babansu kuma yana can daga cikin dakinshi.

Dare ya fara rabawa, amma unguwar kamar a lokacin ma gari ya waye saboda hayaniya.

Adidat ta kama hannun Kauthar cikin nata, kai daga ji babu tambaya kasan taga rayuwa daga yanayin taurin hannunta kawai da kwarzane-kwarzanen da yayi.

Kallon Kauthar take yi idanunta cike da kwalla, tace mata, “kiyi hakuri Kauthar!” a karo na barkatai. Ta daga baki zata ce mata ‘babu komi’ kamar yadda ta saba fadi, amma ta girgiza mata kai, alamun ta kyaleta ta fadi abinda take son fada, don haka ta kyaleta din.

Tace, “ina so ki san cewa, dai-dai da rana ban taba mantawa dake ba, kuma da ace da yanda zanyi, wallahi da kin rayu tare dani ko da ace babu auren mahaifinki a kaina, to amma na riga nayi wasa da damata, na riga na kwabar da garina nayi sakiyar da ba ruwa. Ba zan ce sharrin shaidan bane ya sanyani aikata abinda na aikata ba, nasan nima da halina na kwadayi da son zuwa matsayin da ba nawa ba.

Cikin talauci na taso Kauthar, dangina gabadayanmu babu mai kudin da zai dauki nauyin wani a cikinmu, kowa ta kanshi yake. Shi yasa koda na samu na tafi makaranta, na yanke shawarar da yardar Allah, ba zan taba auren talaka ba. Sai Allah Ya hadani da AbdulFatah a makaranta, mun so junanmu kwarai da gaske, sai dai mu dukanmu talakawane tilis, don ta wani bangaren ma gwara ni akan AbdulFatah din.

Daga farko na kudire zan zauna dashi a hakan duk da talaucinshi. Amma shi sai ya dinga nuna min hakan ba zai yiwu ba. Ni kuwa na dinga mishi naci da nuna mishi tsantsar kauna. Ina tunanin da hakan yayi amfani ya dinga nuna min in samu samari masu kudi in mu’amalance su, a wajensu sai in samar mana abinda zai rikemu tunda dai bamu da tabbacin samun aiki da mun gama makaranta.

Nasan wannan gurguwar shawara ce, amma a haka na biye mishi. Nayi samari iri-iri amma duk basu mishi ba, a haka dai har Allah Ya hadamu da Isma’il wanda a take yace shine wanda yake so.

Bamu so lamarinmu ya kai har a kai ga aure ba, wallahi bamu so hakan ta faru ba.
Ni tun bayan auren ma naso in kwantar da hankalina inyi zamana a dakina tunda dai babu abinda na nema a gidan Isma’il na rasa. Wannan dalili Yasa na yanke duk wata mu’amala da AbdulFatah, na kuma yi nasarar hakan tunda babu ta wata hanya da zai iya lalubata. Tunda dangina tuni suka yi watsi dani, yan’uwana yarena suka so in aura ni kuma na ki, don haka suka zame hannunsu daga lamurana, ni kuwa nace tafi nono fari.

To ban san ta yadda aka yi ya sake laluboni ba, bayan wasu yan shekaru da haihuwarki sai ga shi ya fara bibiyata, amma naki kula mishi. Ya so ya dinga yi mun barazana, amma sai nayi biris dashi.

Da yaga hakan ba zata fissheshi ba, sai ya ce min ya hakura dani har ga Allah, kuma yana yi mun fatan alkhairi a rayuwar aurena. Wannan dalili yasa na saki jiki dashi, muka cigaba da gudanar da mu’amalarmu ta abokai. Da wannan dama yayi nasara ya zugani har nayi mishi rakiya wajen Nuhu ba tare da sanin kowa ba, muka ari kudade wadanda a cewarshi jari zai kafa dasu tunda babu niyar aure a cikin ranshi.

To kuma kwatsam sai ga zancen auren Isma’il ya taso. Hankalina yayi matukar tashin dana kasa samun madafa ko tunani mai kyau, hakan yasa na lalubi AbdulFatah din da neman shawara, don kuwa a lokacin gani nake shi kadai ya rage min. Wannan shine kuskure mafi muni dana taba yankewa, amma idona a rufe yake lokacin. Son zuciya da son abin duniya ya rufe min ido, Yasa na kusa tafka mummunan aikin da nasan har abada ba zan taba daina dana saninshi ba, wanda har a yanzu nake kanyi!

AbdulFatah shi ya taimaka min muka gudu. Dabararshi ta mu tafi dake shine zamu yi amfani da wannan damar ne mu sake amsar wasu kudaden, amma ni maganar gaskiya na amsa mishi da hakan ne kawai amma ba don ina da niyar bada ki wajen Isma’il ba, saboda na kudirce ba zan rabu dake ba.

Sai Allah Ya aiko mana da wannan hatsari, kaina ya matukar bugu, ban ma san cewa AbdulFatah yana biye damu ba sai dana ganshi a gabana a lokacin yana kokarin fitar dani daga cikin motar. Nayi ihu, na mishi kuka da magiyar, ya barni in tafi dake, amma haka ya ja ni zuwa tashi motar muka kwasa muka tafi. Wannan tafiya da muka yi bamu dira ko’ina ba sai Togo. Daga can kuma muka kara gaba.

Ban kara kallon AbdulFatah da mutunci ba tun daga wannan lokaci. Yayi lallashi da ban hakurin, amma naki bashi damar hakan ko fuska. A haka har na kammala iddata. Ban san ta yaya aka yi har ya iya shawo kaina ba na yarda aka daura mana aure dashi.

Zakin soyayya yasa na fara mantawa da wasu abubuwan. Muka samu matsugunni a kasar Ghana, AbdulFatah ya fara kasuwancin sarrafa fata wanda kuma ya karbeshi kwarai da gaske.

Zamanmu gwanin dadi da ban sha’awa, muka dauki shekaru da dama a haka. a can na haifi Zainab kuma.

Kwatsam aka samu matsalar rigima tsakanin yan Nigeria da Ghana, suka kadomu gida cikin kankanin lokaci, dalilin da yayi sanadin tabarbarewar kasuwancin kenan, yan sauran abubuwan da suka rage mana ba wasu na azo a gani bane.

Dawowarmu gida cikin yan’uwanmu, wadanda har a wannan lokacin suka kasa yafe min, da sauran yan kudaden hannunmu muka yi amfani muka sayi gida, ya kuma fara neman wata sana’ar dasu.

Na kasa daurewa raina, abubuwa sun rincabe mana ta ko’ina, daga ni har shi aiki ya ki samuwa, tunda ni dama ba wani sakamako mai kyau gareni ba, haka duk sana’ar daya kama bata zuwa ko’ina take lalacewa, a haka kudinmu suka watse. Ni nasan hakkin mutanen da muka zalinta ne kawai yake dawainiya damu. Musamman idan na tuna irin bashin da muka ci, muka kuma baro Nuhu yana biya bai ji ba bai gani ba, sai inji raina yana kara dugunzuma.

Watarana na dauki hanya dai na diro Abuja, ba don komi ba sai don kawai in nemi gafarar su Isma’il in kuma ganki, amma hakan ya gagara. Ba karamar wahala na sha ba kafin in samo gidan da Isma’il ya koma, haka na kara cin wata wahalar kafin a sada ni da mutanen gidan.

Na durkusa gaban Isma’il da kukana ina rokon gafararshi, yace min shi tuni daya jima da yafe min, amma kuma yana rokon alfarmar in fita daga rayuwarshi kwata-kwata. Baya son ya kara ganina a kusa dashi ko wani nashi, nace naji na amince da hakan, amma ya barni koda sau daya ne in ganki, amma fir ya ki. Nayi magiyar, nayi nacin, amma a banza. Yace tun daga lokacin dana barki a kwance a halin mutuwa da rayuwa, na barar da damata ta matsayin uwa, shi tuni ya sake miki da mahaifiya. Maganganunshi basu bata min rai ba, don kuwa nasan kome ya fada gaskiyane, kuma ni na jawa kaina. Hasalima sai naji tsanar kaina ta kamani, haka na kamo hanya na dawo gida gwiwa a sage.

Nasan cewa ban sake gigin sake bibiyarki ba balle inje inda kike, to in ce miki me? Kunyar haduwa nake dake watarana ki tambayeni dalilin daya sanyani gudunki kuma naki waiwayarki, da wata kalma zan kare kaina? Da wani kalami zan wanke kaina a wajenki?

Amma hakan ba shi ya sanya na manta dake ba Kauthar. A kullum kina cikin raina, a kodayaushe kina cikin addu’ata. Ban taba daga hannu na sauke da sunan rokon Allah wani abu ba tare dana ambaci sunanki ba. Domin kuwa nasan hakan shi kadai ne alamun kaunar da zan nuna miki.

Na kuma ji dadi da kika kawar da komi, kika zo gareni da kanki. Ki yafeni don Allah, hakika son zuciya ya kaini ya baroni. Na aikata miki abinda baki cancanta ba, musamman daga wajen wadda ta tsuguna ta haifeki!”

Ta karashe tana rufe fuskarta da hannuwanta cikin sheshhekar kuka.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kauthar 21Kauthar 23 >>

1 thought on “Kauthar 22”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×