Babu abinda yake tashi a wajan sai ihu da godiyar matasan dake wajan suna jero masa addu'ar samun nasara da ƙara buɗi, Baba ko tsananin farin ciki yasashi daskarewa a wajan baima san wacce irin godiya zai ma alhajin ba, ganin abin yake kamar a mafarki ba wai da gaskeba ashe darajar wayar har takai million da wani abu lallai dole ace za'ayi masa tsirara akan wayar.
Facal! Wani saurayi dake ta tsallen murna ya faɗa kwata inda yana ɗago ƙafarsa ya tafo da wani ƙaramin kwali, cikin mamaki da al'ajabi kowa yake kallon kwalin ganin kwalin. . .
