"Mairo! Mairon Khamis".
Wannan shi ne abin da Maryam ke ji a saitin kunnenta, da zaran mai maganar ya rufe baki kuma sai wannan dariya mai firgitarwa ta ci gaba da bayyana. A yadda take jin su kusa da ita kai ka ce mai maganar da mai dariyar rungume suke da ita.
Idan ana maganar tsoro aka zo ga Maryam to zance ya ƙare. Domin tun tana gidansu ta taɓa ganin wani mutum kafin ta yi aure, lokacin tana kwance ita kaɗai a ɗakin Mamansu, sauran 'yan gidan kuma suna ɗakin Hajiyarmu ana hira kasantuwar dare bai yi. . .