Skip to content
Part 16 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

“Mairo! Mairon Khamis”.

Wannan shi ne abin da Maryam ke ji a saitin kunnenta, da zaran mai maganar ya rufe baki kuma sai wannan dariya mai firgitarwa ta ci gaba da bayyana. A yadda take jin su kusa da ita kai ka ce mai maganar da mai dariyar rungume suke da ita.

Idan ana maganar tsoro aka zo ga Maryam to zance ya ƙare. Domin tun tana gidansu ta taɓa ganin wani mutum kafin ta yi aure, lokacin tana kwance ita kaɗai a ɗakin Mamansu, sauran ‘yan gidan kuma suna ɗakin Hajiyarmu ana hira kasantuwar dare bai yi ba. Ba ta ga fuskar mutumin ba, sai dai ta ji yana taɓa ta, ko da ta yi ƙara sai mutumin ya ruga. ‘Yan gidansu na jin muryarta tana karanta ayatul kursiyyu suka shigo. Ko da suka tambaye ta, “Lafiya?”

Sai ta ce,

“Aljani na gani.”

Tun daga wannan rana tsoro ya sarƙi Maryam, gaba ɗaya ma ta daina kwana a ɗakin Mama, sai dai ɗakin Hajiyarmu. Dare kuwa, da tana da ikon hana shi zuwa to da ta hana, saboda ba ta bacci, kuma ba ta barin wani ya yi.

Kwana ita kaɗai kuwa dama ba ta taɓa ba tunda a gidan yawa ta taso, sai da ta yi aure sannan ta fara, shi ma sai da Khamis ya yi mata lallashi mai kyau sannan ta rage tsoro.

Wannan tsoro na Maryam sosai yake birge Khamis, don muddin za ta ji motsin da bai yi mata ba, ba ta sanin lokacin da za ta ƙanƙame shi tana kyarma, shi kuwa in dai za ta taɓa shi to kuwa zai susuce, har daga wurin lallashinta ya samu abin da zai faranta ransa.

To yau ga Maryam cikin wani hali, wanda ba ta da wani mutum da za ta fake a wurinsa sai ALLAH. Wanda kuma dama a wurinSa dukkan mafaka take don haka ba abin da ke fitowa a bakin Maryam sai, ‘Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un’ lokaci ɗaya kuma ta sa hannunta na dama ta danne mararta da ta ke jin kamar za ta buɗe, ɗayan hannun kuma da shi ta yi dubarar toshe duka kunnuwanta. A yadda ta yi dubarun nisanta kanta daga waɗannan sautuka dole ta baka tausayi saboda tsohon ciki.

Ayatul kursiyyu gami da wasu addu’oin da ba ta san ma bakinta na furta su ba ta cigaba da karantowa a cikin maɗaukakin sauti. Gwargwadon yadda ta nace ma addu’ar, gwargwadon yadda wannan dariya ke yin nisa da ita.

Bata kuma fasa addu’ar ba har sai da ta ji an daina wannan dariya. Wani irin haki ta riƙa yi, cikin ranta kuma tana faɗin ‘me ke shirin faruwa da ni ne?’ Don wannan bala’in ya sha banban da na mutumin da ta taɓa gani a gidansu.

A wannan lokaci kuma ko motsi mai ƙarfi ba ta son yi saboda gani take kamar dariyar za ta dawo. Da a ce lokacin mutum zai je kusa da ita sai ya ji ƙarar faɗuwar gabanta.

Janye hannunta ta yi daga kan marar tare da dafa gado ta miƙe da ƙyar, har a lokacin kuma bakinta na ta ci gaba da addu’o’in da take yi, wanda kuma ya ɗan rage mata tsoron da take ji a ƙirjinta

Anya za ta iya kwana ita kaɗai a cikin wannan dare da ta kira da shi baƙin dare? Da wahala kam, mafarin ta shiga kiran lambar Khamis kenan, sai dai abin damuwar ba ta same shi ba. Mantawa ta yi da faɗansu da Aisha, lambarta ta kira, ita ma switch off.

Zuciya ce ta riƙa ruwaita mata ta fita ta yi musu Knocking, sai kuma tsoro ya dakatar da ita. Rashin sanin yadda za ta yi ne ya sa ta shigewa blanket bayan ta tofe kowace kusurwa ta ɗakin da addu’a, cikin ranta kuma tana ta addu’ar Allah ya kawo mata bacci mai nauyi don ta huta da wannan fargaba, saboda duk abin da ya shafi dariya to ba ƙaramin mugun abu ba ne, an ce ko mafarkin dariya ba’a son yi, bare kuma a riƙa jinta a zahiri tana karaɗe wuri.

Baccin ne ya fara awon gaba da ita, sai dai da ta san abin da za ta ji idan baccin ya fara fizgar ta da ba ta yi shi ba. Farko dai fitilar ɗakin da ta bari a kunne ta ji an kashe, an ku ma faɗin,

“Mairo, Ni ne Khamis.”

Muryar kam ta Khamis ce, amma ‘Yaushe ya shigo? Kuma idan shi ne ai ba zai kashe fitila ba.’ Samun yaƙinin wannan shaiɗani ne ya sa ta furta,

“Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un.” tare da yunƙurawa da ƙarfi ta diro daga kan gadon, a irin wannan yanayi ko babu ciki a tare da mace sai ta ji a jikinta, bare kuma mai tsohon ciki.

A kiɗime ta dubi ƙofar ɗakin saboda an kunna fitilar, ganin ba kowa ne yayi sanadiyyar sulalewarta ƙasa sumammiya.

A kuma wannan lokaci da Maryam ke naman ɗaukin Khamis, shi kuwa yana can wata duniya mai cike da jin daɗi, wadda kuma Aisha ce ta yi sanadiyyar zuwansa. Bayan ya samu nutsuwa, ya kuma dawo duniyar da ya saba rayuwa a cikinta ne ya jawo Aisha a jikinsa, a kunne ya raɗa mata,

“Lallai fitarki ta yau ta min rana, sosai ki ka faranta ran mijinki, kuma mai ƙaunarki.”

Yana rufe baki ya sumbace ta a goshi.

Shigewa ta yi jikinsa ta na ƙara narkewa, shi ma ɗin narkewar yake, ce mata ya yi,

“Aisha haka nake son rayuwarmu ta kasance har abada.”

Saboda ba ƙaramin daɗi yanayin ya yi masa ba.

Aisha da ta san me ta taka ta ce, “Uhm, Insha Allah farincikinmu ya dasa daga yau mijina.”

Cikin ranta kuma ta ce,

‘Tunda ƙarshen waccan ‘yar banzar ya zo ba.’

Ita a rayuwarta babu son Maryam ko kaɗan a ciki. Kuma ta yi imanin da in dai Maryam na cikin nutsuwarta to ita kuma ba ta da zaman lafiya a gidan, shi ya sa ta zaɓi yi mata asiri, don a ganinta wannan hanyar ce kaɗai ta rage mata wadda za ta samu farinciki.

Soyayya ta musamman Asha ta gwada ma Khamis, wadda bata san ta iya irin ta ba sai a wannan dare. Ashe in dai mace na son cimma wata manufarta a wurin namiji babu kalar kular da ba za ta iya bashi ba.

Sosai suka faranta ran juna a wannan dare. Washe gari Khamis na dawowa masallaci ya zarce ɗakinta. A kuma wannan lokacin idan da za ka tambaye shi ya matsayin Aisha a wurinsa? To zai ce a yanzu ta zarce dukkan mata. Sai dai a ƙasan ransa yana tababar anya har da Maryam? Saboda salon soyayyar Maryam na daban ne.

A kan prayer mat ɗin da take zaune shi ma ya zauna, sai da ya riƙo hannayenta sannan suka gaisa, daga bisani kuma ya ce “Princess Eesha, haka kika iya faranta rai?”

Saboda ya kasa manta kulawar da ta bashi.

Far ta yi da idanu akan yabon da ya yi mata, sannan ta ce,

“Sosai ma.”

Ya ce,

“Amma ai ba kya yi.”

A shagwaɓe ta ce,

“Ai laifinka ne.”

Ya ce,

“Toh Sorry, zan gyara laifina in dai zan riƙa samun wannan kula daga gare ki.”

Aysha gani take asirin da ta fara yi ne ya sa ta samun kan Khamis. Shi kuma har ga Allah kulawar da ya samu daga gare ta ne ya bashi damar faranta mata ita ma.

Bayan sun ɗan taɓa ‘yar hira ne ya ce zai je ɗakin Maryam, nuna mishi ta yi ba ta so, ɗan marairaicewa ya yi gami da faɗin, “Mai ciki dole a kula da ita fa.”

Ba don ta so ba ta bar shi ya fita.

Ɗakin Maryam ya nufa tare da yin Knocking, lokaci ɗaya kuma ya yi magana sak irin yadda aka yi ma Maryam a daren jiya, inda ya ce “Buɗe ƙofa Mairo.”

Tun cikin dare Maryam ta farka daga suma. da ta yi. Daga can kuma Khamis ya jiyo ta tana kuka tare da faɗin,

“Wayyo na shiga ukuna, don Allah ka daina tsoratar da ni saboda ina cutuwa.”

Kuka da lafuzzanta ba ƙaramin ɗaga hankalisa suka yi ba, murɗa handle ɗin ɗakin ya yi da ƙarfi, don ya manta da ta sanya key a ƙofar.

“Ni ne fa Maryam, waye ne ya shigar miki ɗaki?”

Ya faɗa hankalinsa a tashe.

Ƙarar da ya ji ta fasa ce ta ƙara gigita shi. A gurguje ya zagaya bayan ɗakinta tare da buɗe window, saboda a ƙagare yake ya ga halin da take ciki.

Cikin tashin hankalin ganinta baje a kan carpet ya kira sunanta, amma bata yi motsi ba ma bare ta amsa.

Ɗakinsa ya koma ya ɗauko spare key, tare da faɗa ma Aisha Maryam ba ta da lafiya.

Gabanta na faɗuwa ta ce,

“Ko haihuwar ce?”

Kai ya girgiza,

“Wadda ke unconscious wane haihuwa kuma.”

Bai jira ta sake magana ba ya yi gaba.

Jikinta na ɓari ta bi bayansa, cikin ranta kuma tana faɗin,

‘Ko maganina ya fara aiki ne?’

Zaune ta iske Khamis har ya ɗaga Maryam ya ɗora mata kai a kan cinyoyinsa, sosai ya duƙar da kansa a saitin fuskarta yana faɗin “Maryam.”

Shirun da ya ji ne ya sa shi duban Aisha da ita ma ta duƙo tana sallallami ya ce,

“Aysha ruwa.”

Ruwan da ke cikin bottle a kan mirror ta miƙo mishi, ai kuwa yana fesa ma Maryam ta buɗe idanu. Suna yin ido huɗu kuma Maryam ta fasa wata irin ƙara tare da yunƙurin zare jikinta daga nashi tana faɗin

“Don Allah ka fita ba na son ganinka.”

saboda fuskar wani baƙi kuma mummunan mutum mai jajayen idanu take gani a fuskar Khamis.

Kamar zai yi kuka ya ce,

“Maryam ni ne fa.”

Tare da riƙe ta, suna sake haɗa ido sai gashi ta sake sumewa.

Aisha kuwa sake tambayar kanta ta yi a zuci,

‘Ko aikina ya ci ne?’

Kafin ta samu amsa ta ji Khamis ya ce,

“Ya Allah!” tare da ɗaukar ruwa ya fesa ma Maryam.

Tana buɗe idanu suka yi ido huɗu. Yanzu Khamis ne Maryam take gani, sai dai cikin ranta tana jin wata irin tsanarsa, zaune ta tashi sannan ta haɗa hannyenta biyu. tana roƙonsa,

“Don Allah ka fice mini a ɗaki.” Riƙo hannayen ya yi ya ce,

“Ni ne fa Maryam, mijinki ne Khamis.”

Fizge hannunta ta yi tana cewa, “To ba na sonka, don Allah ka fita.”

Dafe kai Khamis ya yi,

‘Meke faruwa ne, anya Maryam kanta ɗaya?’

Abin da kenan ya faɗa a ransa.

Aisha kuwa tuni ta samu amsar tambayar da take ta jefo ma kanta, saboda ta ga tsanar Khamis a tare da Maryam, kuma manufar asirin kenan

Take fargaba ta kama ta, don ba ta yi tsammanin Maryam za ta shiga mawuyacin hali irin wannan ba.

Jikinta a sanyaye ta dafa shi “Abban Haneef ka fito tunda ba ta so.”

Shiru ya yi yana duban Maryam da ta yi ma wuri ɗaya ƙuri, kasa tashi ya yi, suna sake haɗa ido da Maryam ya ga ta rumtse idanunta gam. Zuciyarsa cike da ƙuna gami da mabanbantan tambayoyi ya fice daga ɗakin shi da Aisha.

Hannun Ausha na cikin nasa suka zauna a falo.

“Abban Haneef na tsorata da Maryam, anya kuwa babu aljanu a kanta?”

Sai da ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ya ce,

“Nima tunanina kenan.”

Shiru ya yi tare da dafe kai,

“To dama Maryam na da iskoki ne kafin na aure ta?”

Tambayar da ya yi ma kansa kenan, bai da amsa, don mahaifan Maryam ne kaɗai za su ba shi wannan amsar.

A hankali ya lumshe idanu tare da kwantar da kansa a kujera.

Aisha kuwa a yadda ta ga ya yi jugum ɗin ne ya dame ta. Gani ta yi ya miƙe zai nufi ɗakin Maryam, ruƙo shi ta yi ta ce,

“Ka ga fa bata son ganin ka.”

Kasa bata amsa yi saboda jin zafin wai shi ne Maryam ba ta son gani. Ɗakin Maryam ɗin ya nufa.

Sai dai ba shi da yake cikin ɗakin ba hatta Aisha sai da ta firgita da ƙarar da Maryam ta saki. cikin kiɗima Khamis ya fito yana faɗin, “Na shiga ukuna, kai wai miye haka ne, matata da ganina ne cikar farincikinta, amma ita ce yau take gudu na?”

Lallai da walakin goro a miya! Aisha da ta dafa shi ya ce ma wa, “Ke shiga mu gani ko za ta yi ƙarar.”

Idanu ta ɗan zaro.

“Tsoro nake ji.”

Ya ce,

“Zan tsaya a bakin ƙofa ai.”

A tsorace Aisha ta shiga ɗakin, a bin mamaki Maryam na ganinta ta fashe da kukan da dole a tausaya mata.

“Umman Haneef, ki ce ma Abban Haneef ya dakna shigowa.”

Aisha na ganin haka ta daina jin tsoron, gefenta ta ɗan duƙa tare da dafa ta.

“Maryam ai mijinki ne, ta ya kuma zan ce ya daina shigowa?”. Maryam ta ce,

“Ai fuskar wani mutum nake gani a tare da shi.”

Ta na faɗin haka ta sake fashewa da kuka.

Zuciyar Aysha da sauran Imani, take ta karaya ta ce,

“Wani kuma Maryam?”

Maryam ta ɗaga kai.

“Ni ban san me ke damuna ba, ji nake kamar ba ni ba, na dana jin mijina a zuciyata, ko an raba ni da shi ne?”

Take tausayin Maryam ya kama Aisha, zuciya ce ta yi mata faɗan me ya sa ta yi haka, zama ta yi a gefen Maryam ta ce,

“Ba abin da ke damunki, ke dai ki yi ta addu’a.”

Maryam ta ce,

“To, cikina yana riƙewa kuma.”

Aisha ta ce,

“Zai bari.”

Ta shi ta yi za ta fito, Maryam ta ce,

“Ki sa mini key don kada ya shigo.”

A falo Aisha ta samu Khamis ya dafe kai da dukkan hannayensa, saboda ya ji duk abin da Maryam ta faɗa lokacin yana laɓe a bakin ƙofarta.

“Aysha yanzu wani matata take gani ba ni ba?”

Ya faɗa bayan Aisha ta janye mishi hannayen.

Ya Salam! Daga shi har Aisha damuwa ce ta mamaye su, shi rashin sanin mafarin ciwon Maryam ke damun shi, ita kuma tsoron ita ta yi asiri har haka ta faru ke damunta.

Khamis kam ba zai juri wannan ba, duk da yana da yaƙinin aljani ne Maryam ke gani, amma bai hana shi jin kishi ya turnuƙe mishi zuciya ba.

‘To ko Jinnul Ashiq gare ta?’

Ya tambayi kansa, bai fatan amsar ta zama gaskiya don shi da aljani ke aurenta kenan.

Aisha kuma tuni ta aje ma Zuzee saƙo a WhatsApp cewar ta zo a gaggauce saboda asiri ya fara aiki, don ta faɗa mata zuwanta gidan Jamsy.

Shirya ma yara school ta yi. Suna yin breakfast Khamis ya kira Sani ya zo ya kai su.

Ita ɗin ce ke ta ɗawainiya da Maryam, ba kuma komai ya sa ba sai don ita ta yi sanadin shigarta wannan hali. Shi kuwa Khamis yana ji yana gani ɗakin Maryam ya gagare shi, damuwa kuma tuni ta samu mazauni a zuciyarshi don ko breakfast bai yi ba. Da wuri Aisha ta gama lunch, duk yadda ta so ya ci amma ya kasa, sai ma yayi alwalar azuhur suka tafi masallaci shi da Haneef, don sun daɗe da dawowa daga school.

A kuma wannan lokaci ne Zuzee ta zo. Tana ganin yadda Aisha ta tsure ta ce,

“Ya na ga kin wani yi sanyi kamar a kanki asirin ya dira?”

Aisha da ke shirin zama a kan kujera ta ce,

“Zuzee ni fa da na san haka za ta yi da ban yi ba.”

Wani mugun kallo Zuzee ta yi mata bayan ta zauna a gefenta kan kujera three seater.

“Rama cuta ga macucin ce kike nadama, to ke wanda ta yi miki fa? Wallahi idan ma za ki cire tsoro ki ƙwaci ‘yancinki to.” Damuwa bayyane a fuskar Aisha ta ce,

“Zuzee ba ki ga yadda ta koma ba, tsakanin jiya da yau har ta fara canja kamanni. Shi ma Abban Haneef yau kaɗai ba ki ga yadda ya koma ba, kamar shi ne mai ciwon.”

Ko kusa Zuzee bata karɓi uzurin Aisha ba, taɓe baki ta yi sannan ta ce,

“To saboda ta canja kamanni ne za ki wani damu, ita kin san baƙin ƙudurinta a kanki? Ki nutsu kawai, wannan don yana na farko ne, da kin saba za ki ji ba komai ko da mutuwa ta yi.”

Aisha ta ce,

“Banda mutuwa dai, ciwon ma ba na so ta yi, ni dai a cire mata son mijina kawai.”

“To ai ta hakan ne za’a cire mata son nashi.”

Zuzee ta faɗa saboda burinta Aisha ta daina damuwa da abin da ta yi. Ci gaba da cusa ma Aisha yadda za ta ga asirin ba komai ba ne tai ta yi.

“Yanzu da lafiyarta ƙalau, a safiyar yau kaɗai sai kin haɗi baƙinciki ya fi a ƙirga.”

Aisha ta ce,

“Wallahi kuwa Zuzee, ni kaina yau ji na nake sawai, saboda ba damar Abban Haneef ya shiga ɗakinta bare su yi abin da zai sa ni a damuwa”

Zuzee ta ce,

“To kin gani, don haka duk halin da za ta shiga kada ya ɗaga miki hankali, dama ce Allah ya baki a kanta, don haka ki yi amfani da damarki ki.”

Da Aisha ta nuna mata tsoron kada a gane ita ta yi ma Maryam asiri, sai ta ba ta shawara wai ta riƙa cewa Maryam na da iska. Ita ma sai a kwanan nan ta fahimci haka.

A ɓangaren dangin Aisha kuma, Zuzee ta ce mata,

“Ki ce musu ƙila asiri ne ya koma mata. Su kuma danginta ki barsu da hasashensu saboda sun san wacece ‘yarsu.”

A batun damuwar da Khamis ya yi da ciwon Maryam shi ma yana taɓa zuciyar Aisha, tambayar Zuzee ta yi,

“Ya zan yi da shi? Na ga kamar shi maganin bai kama shi ba.”

Saboda yanzu kam Aisha ta fara ci ta gyare. Zuzee da neman hanyar da za ta ƙara kai Aisha ta baro take yi, cewa ta yi,

“Akwai Malamin da zan haɗa ki da shi, idan ya yi miki aiki sai yadda kika yi da shi.”

Aisha ta ce,

“Ke don Allah?”

Zuzee ta ce,

“Wallahi, Anty Jamsy ma ai tana zuwa wurin shi.”

Aisha na jin haka ta ce,

“Ai kuwa za ki raka ni tawar.” Saboda yadda Jamsy ke mulkin mallaka a gidanta ba ƙananun Malamai take hulɗa da su ba.

Duk wannan zuga da Zuzee ke ma Aisha ba don tana son ta ba take yin ta, sannan wurin Malamin da take shirin kai ta don su tatsi kuɗi a wurinta ne kawai, amma ba don ta yi ma Khamis asiri ba, saboda Zuzee ba ta ƙaunar Aisha ta mallaki Khamis, bata ƙi ba ma su watse da shi.

Bayan sun gama ƙullin ne suka shiga ɗakin Maryam. Kwance suka same ta tana bacci. Wani irin kwarjini ne ta yi musu kasantuwar bacci na mata kyau, har wasu lokuta Khamis na ce mata ‘My Sleeping beauty.’

Duk yadda Zuzee ke ƙin Aisha, idan aka haɗa da tsanar da take ma Maryam ba komai ba ce. Mugun bakinta da bai saba faɗin alkhairi ba ta buɗe za ta yi magana, alamu Aisha ta yi mata da ta yi shiru.

“Maryam.”

Aisha ɗin ta faɗa, a hankali Maryam ta buɗe idanunta da suka ƙanƙance. Sannu Aisha ta yi mata.

Sai da ta ɗan cira kanta da take jin kamar zai tsage sannan ta amsa.

Duban Zuzee ta yi, kawai sai ta ji faɗuwar da gabanta ke yi ta ƙaru, da sauri ta maida idanun ta rufe.

Zuzee kuwa shu’umin murmushi ta yi, don malaminta ya faɗa mata duk wanda ta tsana ba zai yarda su haɗa idanu ba, to a ganinta maganin ne yayi aiki a kan Maryam.

Maida hankalinta ga Aisha ta yi lokacin da ta ce ma Maryam,

“Me za ki ci?”

Idanun Maryam a rufe ta ce,

“Ba komai.”

“A’a ki daure ki ci wani abu, ko don saboda cikin ki.”

Cewar Zuzee da ke ta yi ma Maryam kallon tsana.

Shiru Maryam ta yi, sai da ta ji muryar Aisha ta sake yi mata magana sannan ta ce duk abin da aka dafa a ba ta za ta ci.

Fitowa suka yi daga ɗakin. Zuzee ta ce,

“Ki ci gaba da kula ta, yadda duk bala’in mutum ba zai gane ke ce muguwar da kika sa ta a wannan hali ba, kuma ta haka za ki ƙara ɗura mata wani bala’in.”

Aisha na ‘yar dariya ta ce,

“Ki daina ce mini muguwa fa, na san da wasa ake faɗa ma wawa magana.”

Tabbas da niyyar yankan Aisha ta yi wannan magana, ganin Aishar ta ankare ne ta ce,

“Aaaa! Ai ba jifar juna da magana a tsakaninmu, yadda za ki ci karenki babu babbaka ne nake faɗa maki.”

Jin motsin Khamis ya hana Aisha yi ma Zuzee magana, sai dai ta ce “Ga Abban Haneef nan.”

Zuzee na ganin Khamis ya shigo falon ta ji gabanta ya faɗi, kwarjinin da ya yi mata ne ya ɗan fama mata tsohon ciwon son da take mishi.

“Zuhura.”

Ya faɗa daga inda yake tsaye, gefensa kuma yaransa ne rike da hannunsa. Gaishe shi Zuzee ta yi, duk da damuwa ce cike da ransa, amma sai da ya ƙaƙaro fara’a sannan ya amsa.

Maida kansa ga Aisha ya yi,

“Aisha ya Maryam ɗin?”

Cikin ‘yar kissa ta ce,

“Da sauƙi, amma ka sanar da Mahaifanta ko?”

Kai ya girgiza,

“Tukunna dai, mu je ɗakin.” Saboda gani yake kamar abin zai wuce. Gaba ya yi, Aisha da Zuzee suka bi bayansa.

Cike da fatan kada Maryam ta tsorata da ganinshi ya shiga ɗakin. Sai dai ina, tana ganin shi ta bazama da gudu ta ɓoye fuskarta a kusuwarwar ɗakin. Aisha da Zuzee kuwa basu san sa’adda su ka yi kanta ba saboda tsohon cikinta da ta dafe bayan ta durƙushe a inda take.

Cike da tausayin Maryam ya fice daga ɗakin.

Su kuwa lallaɓa ta suka yi ta tashi, kwanto da kanta ta yi a kafaɗar Aisha tana kuka ta ce,

“Don Allah ku fitar da ni daga gidan nan, tsoro nake ji kada na rasa raina, mutumin nan tsoro yake ba ni.”

Haka Aisha take son ji, duban Zuzee ta yi suka yi shu’umar dariya, duk da a can ƙasan ranta tana jin tausayin Maryam, ce ma Maryam ɗin ta yi,

“Ki yi haƙuri kin ji, komai zai wuce.”

Kama ta suka yi ta kwanta sannan suka fito.

A bakin ƙofar ɗakin suka sami Khamis, Zuzee ce ta yi saurin magana inda ta ce,

“Irin wannan ciwo ba lafiya ba Abban Haneef, ko dama tana da iska?”

Khamis ya ce,

“Wallahi Zuhura ban sani ba, amma dole na tambayi mahaifanta.”

Tunda ya fara magana Zuzee ke kallon shi, take ramar da ya yi ta ƙara tafi da ita. Kuma a wannan lokacin za ta yi amfani da damarta duk don ta kutsa kai a cikin rayuwarsa, don tafi son shi akan Abdul ɗin gidansu Aisha.

Fita Khamis ya yi. Su kuma ya barsu nan suna ta saƙawa da kwancewa.

Gidansu ya nufa, saboda mahaifiyarshi ce farkon wadda ya zaɓa ta fara jin dukkan damuwarsa.

A can kuma ya samu Anty Rahama ta je. Bayan sun gaisa ne suka fahimci yana cikin damuwa.

Rahama ce ta riga Ummansu tambayar shi,

“Ya dai babban Yaya?”

Kamar zai yi kuka ya ce,

“Maryam ce bata da lafiya.”

Umma na jin haka ta ce, “Haihuwar ta zo kenan?”

Ya ce,

“A’a wallahi Umma, ciwonta kamar iska ne ma.”

Labarin yadda abin ya samo asali ya ba su, ai kuwa sai suka shiga sallallami.

Rahama ta ce,

“Ko dai tana da iskokinta dama aka aura maka?”

Umma ta ce,

“Ba ta a nan Rahama.”

Sosai suka shiga zargin Maryam na da iska tun a gidansu, kawai an ɓoye ma Khamis ne.

Tambayar shi Umma ta yi,

“Me aka yi mata na magani?”

Ya ce,

“Ba komai, kawai ki je gidan sai mu ga ya za’a yi, ni cikin jikinta ne ke damuna.”

Tashi Umma ta yi ta shirya, Rahama kuma ta ɗauki mahayafinta da waya tare da zura takalma suka tafi. Su Hafsat kuwa sun so aje da su, to ganin ba wanda za’a bar ma gidan sai suka haƙura.

A falo suka taras da Zuzee da Aisha. Daga Umma har Rahama ba wanda bai ji tsanar Zuzee a ransa ba, musamman yadda da ganinsu ta fara kauɗi.

Ɗunguma su duka suka yi zuwa ɗakin Maryam. Nishin da suka taras da tana yi ne ya ɗaga hankalin kowa, hatta Khamis da ya toge a bakin ƙofa bai san sa’addda ya kutsa kai cikin ɗakin ba.

Gaba ɗaya suka matsa kusa da ita, Umma ce ta zauna a gefen gadon tare da dafa Maryam ta ce, “Maryam, me ke damunki?”

Tsananin ciwon da ke damun Maryam bai bari ta yi magana ba, sai dai ta riƙo hannun Umma gam. Rahama da su Aisha kuwa sai sannu suke mata, don ko Zuzee da ke da muguwar zuciya sai da ta tausaya mata.

“Wannan a shirya zuwa asibiti kawai, don kamar tana labour.” Cewar Umma tana duban Khamis. Rufe bakinta ya yi daidai da sakin ƙarar Maryam.

Umma da hankalinta ya gama tashi ta ce,

“Wannan yarinyar ko da labour kuma akwai iska a kanta, dole a san abin yi.”

Shi Khamis ta cikinta yake yi, yadda take ta fizge-fizge suna riƙe ta ne ya ƙara tsorata shi. Gani yake kamar cikinta zai taɓu.

“Umma asibiti ya kamata a fara kai ta domin duba lafiyar cikinta, daga baya kuma idan na islamic za’a yi sai a yi.”

Rahama ta karɓe da,

“Gaskiya nima na yi wannan tunanin.”

Aisha da Zuzee kuwa sai muzurai suke yi don sun san mugun abin da su ka yi.

Aunty Rahama kuwa sai harare-harare take, kuma da Zuzee take don ta tsani ganinta. Zuzee na lura ta ce tafiya za ta yi, sallama ta yi musu, ba wanda ya kula ta sai Khamis, Aisha kuma tare suka fito da nufin yi mata rakiya.

Addu’a Umma ta riƙa tofa ma Maryam, cikin ikon Allah sai gashi ta nutsu, amma har a lokacin ba ta san wa ke kanta ba.

Waya Khamis ya buga ma Dr. Dini, nan yake faɗa mishi suna hanya za su kawo Maryam. Dini ya san ba lafiya ba saboda ya fi kowa sanin kwanikan cikin Maryam, kasantuwar shi ne likitanta.

Umma da Rahama ce suka sanya mata kayan da Khamis ya ciro mata a wardrobe. Hijabi da takalma suka zura mata, sannan suka riƙe hannunta don tana iya tafiya zuwa parking space.

Aisha da ke ta nuna tausayin munafunci ta ce za ta je asibitin. Khamis ya ce ta bari su fara tafiya, idan ya so daga baya sai ta biyo su.

A can asibiti kuwa tuni Dini ya tanadar ma Maryam gado a emergency. Suna zuwa asibitin ya shiga duba ta da abin da ke cikinta.

Ko kusa cikin Maryam bai yi motsi ba. Scanning room ya tura ta, inda kuma da kansa ne yayi mata. Abin da ya gani ba ƙaramin ɗaga mishi hankali ya yi ba. Domin alamu sun nuna ɗan cikin Maryam gab yake da mutuwa.

Zuciyarsa a dagule ya fito daga ɗakin, duban Khamis da ke zaune kan wani benci ya yi, bai ɓoye masa ba, don haka ya ce,

“Maryam na cikin critical condition, mafita ita ce ayi mata CS a fiddo bebin, tunda seventh month zai iya rayuwa, idan ba haka ba za’a iya rasa su ita da bebin.”

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Khamis ya sauke tare da sanya hannunsa cikin na Dini.

“Duk abin da ka ke ganin shi ne mafita ga lafiyar Maryam ka aiwatar da shi Dini.”

Wurin su Umma suka tafi tare da shaida musu yadda za’a yi.

Sosai suka tausaya ma Maryam, Umma ta ce,

“To Khamis, idan hakan ne zai ba ta lafiya sai a yi, amma kafin nan a faɗa ma danginta.”

Rahama kuwa kasa magana ta yi saboda tausayin Maryam da ya mamaye ta.

Lambar Mamansu Haupha ya kira, switch off ya ji lambar, sai ya danna lambar Haupha. Ya yi sa’ar samunta kuwa, bayan ta amsa sallamar da ya yi mata ne ya ce, “Hajiya fa?”

Yana jin sadda Haupha ta miƙa ma mahaifiyarta waya ta ce,

“Hajiya Khamis na magana.”

Cike da ladabi Khamis ya gaida Hajiyarsu Haupha, bayan ta amsa ne yake shaida mata Maryam na asibiti, daga can ta ce, “Haihuwar?”

Duk da ta san cikin bai isa haihuwa ba.

“Eh.”

Ya faɗa, tare da faɗa mata yadda haihuwar ta zo. Asibitin da suke ya faɗa mata, sannan suka yi sallama.

Kai tsaye theater room aka wuce da Maryam. Lokaci da sa Hannun duk wanda ya kamata kawai Dini ke jira.

Hajiyarsu Haupha na zuwa ta ga halin da Maryam ke ciki, hankali tashe ta ce,

“Maryam haka Allah ya yi da ke?” Da yake Maryam ɗin ta dawo hayyacinta ta riƙe hannun Hajiyarsu Haupha,

“Hajiya mutuwa zan yi.”

Take zuciyar Hajiyar su Haupha ta karye,

“Ba za ki mutu ba Maryam.”

“To Hajiyarmu ki yi mini addu’a kaina yana mini ciwo. Kuma wani mutum mai muryar Abban Haneef yana tsorata ni.”

Faɗuwar gaba ce ta riski Hajiyarsu Haupha, cikin son kwantar ma Maryam da hankali ta ce,

“Zafin ciwo ne Maryam, amma ba wani mutum.”

A ƙasan ranta kuma tana tunanin ko har da iska ke damun Maryam.

Khamis kuwa tuni ya buga waya gidansu Maryam ya faɗa musu halin da ake ciki. Cewa suka yi ce ai shi ne wakilinsu a wurin Maryam, kuma ga mamansu Haupha nan ai, don haka duk yadda Allah ya yi da Maryam mai kyau ne.

Tuni Dini da wasu Doctors uku suka shiga don yi ma Maryam aiki. Khamis kuwa sai sintiri yake a bakin ƙofar ɗakin.

Hajiyarsu Haupha da su Umma kuma su ka je ƙarƙashin wata bishiya suka zauna.

Zuciyoyinsu a dagule suka riƙa maganar halin da Maryam ke ciki, Hajiyarsu Haupha ta ce ma Umma, “Wai kin ji wani mutum ne ke bata tsoro.”

Umma da dama ke son su yi maganar ta ce,

“Wallahi kuwa, ni kam tana da iska ne?”.

A iya sanin da Hajiyarsu Haupha ta yi Maryam ba ta da iska, cewa ta yi,

“A’a wallahi, ko akwai to daga bayan nan suka same ta.”

Rahama ta ce,

“Ƙila kuma ba iska ne ba, zafin ciwo ne ke damunta.”

Fatan samun lafiya su ka yi mata.

Tuni Doctor Dini da sauran Doctors sun samu sa’ar fito da ɗan cikin Maryam. Duk da yaron preemie ne, amma ba wanda kyawunsa bai ɗauki hankalinsa ba, kasantuwar akwai fuskar Maryam da Khamis duk a tare da shi.

A baby incubator suka sanya shi tare da kai shi NICU domin bashi agajin gaugawa.

Maryam ma Room ɗaya aka bata domin ita ma ta samu kulawar musamman ba tare da takurawar wasu patients ba. Har lokacin da aka baro da ita theater room bacci take yi. Gaba ɗayan su kowa fata yake ta farka cikin hayyacinta, shi ma baby suna ta fatan ya samu lafiya.

Tun kafin a kai shi NICU suka ganshi, su Haneefa kuwa sai murna suke sun yi ƙane.

Aisha kuwa zuciyarta ta kasa sukuni saboda namiji ne aka ciro a cikin Maryam, gani take saura ƙiris Maryam ta gaje gida. Ba ta taɓa damuwa a kan tsayawar haihuwarta ba sai a wannan lokaci. Ji ta riƙa yi ina ma Maryam ta mutu.

Dangi na kusa ba wanda bai zo ya ga Maryam ba Preemie ɗinta kuwa sai dai su ganshi a picture, babansa ma baya samun ganinsa sai idan likitan da ke kula da shi ta zo. Sosai Khamis ke son yaron, don cikin ikon Allah lafiyarsa ta ƙaru sakamakon kular da yake samu.

Yanzu fatansa shi ne lafiyar Maryam da har yanzu take bacci. Zaune yake a gefen gadon da take kwance, inda kuma Aisha da su Haneef suna tsaye a gaban gadon duk suna kallon ta.

“Allah ya ba Anty lafiya.”

Cewar Haneefa cikin muryar tausayi, don Khamis ya ce su sanya ta a addu’a. Khamis da ya ji daɗin addu’ar ya ce,

“Amin tawan.”

Haneef ma addu’ar samun lafiya ya yi ma Maryam. Aisha kuwa fuskarta a murtuke, a zahiri za ka ce damuwar halin da Maryam ke ciki take, a baɗini kuwa ita kaɗai ta san me take ƙullawa, don ba ta ƙi ba Maryam da preemie ɗinta su mutu gaba ɗaya. Tunda ta tsaya a wurin sau biyu ta yi magana, Khamis kuma abin da ya isheshi a rai ya ishe shi, ko kaɗan bai buƙatar maganarta. Duƙar da kansa ya yi tare da riƙo hannun Maryam, a zahiri ya ce,

“Allah ya baki lafiya Mairota.”

<< Kishiyar Katsina 15Kishiyar Katsina 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×