Aisha kuwa ɗakinta ta koma tare da ɗaukar waya, duk don ta rage ma kanta zafin hana ta zuwa kitso da Khamis ya yi. Jerin gwanon missed calls ɗin Zuzee ta gani a duka layukanta da ke cikin wayar.
Zama ta yi a gefen gado lokacin da ta danna kira a lambar Zuzee, "Haba baiwar Allah, ba zuwa ba aike, ko mun mi ki laifi ne?"
Abin da Aisha ta faɗa bayan Zuzee ta amsa kiran kehan.
Dariya Zuzee ta yi daga cikin wayar sannan ta ce,
"Yi haƙuri 'yar'uwa, wallahi tun washegarin walimar amaryarki wayata ta. . .