Skip to content
Part 8 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

Aisha kuwa ɗakinta ta koma tare da ɗaukar waya, duk don ta rage ma kanta zafin hana ta zuwa kitso da Khamis ya yi. Jerin gwanon missed calls ɗin Zuzee ta gani a duka layukanta da ke cikin wayar.

Zama ta yi a gefen gado lokacin da ta danna kira a lambar Zuzee, “Haba baiwar Allah, ba zuwa ba aike, ko mun mi ki laifi ne?”

Abin da Aisha ta faɗa bayan Zuzee ta amsa kiran kehan.

Dariya Zuzee ta yi daga cikin wayar sannan ta ce,

“Yi haƙuri ‘yar’uwa, wallahi tun washegarin walimar amaryarki wayata ta ɓace, kuma ko ba wannan ma ai gidanki yanzu bai zuwuwa, don ana ganin mutum na zarya za a ce munafunci ya kawo shi.”

‘Yar guntuwar dariya Aisha ta yi tare da faɗin,

“Haba don Allah, ke dai ba ki yi niyyar zuwa ba kawai.”

Zuzee da ta fi ta iya zaman duniya ta ce,

“Ke dai.”

Gaisawa suka yi sosai, Aisha kuma ta jajanta mata ɓatan wayarta, daga nan kuma suka ci gaba da hirarsu ta ƙawaye, sai da labari ya nisa ne Aisha ta ce mata,

“To yaushe za ki zo don Allah?”

Zuzee ta ce,

“Ba rana.”

Ɗan marairaicewa Aisha ta yi sannan ta ce,

“Akwai labari fa.”

Zuzee na jin haka ta ce,

“Bari mu gani nan da jibi In sha Allahu zan shigo.”

Jibi ce ranar da Aisha za ta je kitso, saboda haka ta ce mata,

“Zan fita kitso a jibin.”

Da yake ‘yar tazara ce tsakanin gidansu Zuzee da kuma inda Aisha ke zuwa kitso, Sai Zuzee ta ce,

“To ki biyo ta gidanmu sai na raka ki, kin ga mun haɗu kuma kin yi zumunci.”

Aisha ta ce,

“Haka ne, to In Sha Allahu zan biyo.”

Da wannan ne suka yi sallama. Aisha na aje wayar ta ji zuciyarta sawai ba wata damuwa. Fitowa ta yi ta shiga kitchen domin girka abincin rana.

Khamis ya yi zaton zai dawo ya taras da ita tana fushi, saboda ba abin da ta tsana irin ya hana ta fita, saɓanin haka da ya gani ne ya ce mata,

“Su Sholy dai an chanza.”

Ta ce,

“Wurin me?”

Ya ce,

“Na ɗauka zan taras kina fushi ne ai.”

‘Yar harara ta yi mi shi saboda ta fahimci inda ya dosa, ce mishi ta yi,

“To ya zan yi tunda ka hana, kuma jibi ai kamar gobe ne ko?”

Ya ce,

“Haka ne.”

Jin daɗin haka ne ya sa shi sakar mata jiki suka sha hira. Ƙarfe taran dare na bugawa kuma ya baro mata ɗakin saboda ma’abocin kallon News ne.

Wayarsa da ya bari akan stool ta ɗauka,

“Kai Inna lillahi wa Inna ilaihir raji’un!”

Ta furta a fili lokacin da ta ga hoton Maryam a lock screen wallpaper ɗin Khamis. Gabanta na ci gaba da faɗuwa ta ce,

“Kai ni wannan jarababbiyar yarinya, Allah ka yi mini maganin ta in huta.”

Saboda daidai da jin sunan Maryam ɓata mata rai yake yi, bare kuma hotonta ko ta ganin ta a fili.

Shiga gallery ta yi da nufin chanza wani hoto, sai dai hotunan Maryam ɗin da suka cika kowace folder ne ya kusa tarwatsa mata zuciya. Foldan WhatsApp ta fara shiga, wasu irin picturse masu zafi ta gani na Maryam cike da folder, ba ta yi wata-wata ba ta yi delete ɗinsu all, cikin ranta kuma tana faɗin,

“Wato duk inda yake yana manne da ita.”

Sai dai ba pictures ɗin WhatsApp ne suka fi taɓa mata zuciya ba saboda su da gani Maryam ɗin ce ta ɗauke su da kanta.

Bidiyon da ta gani a camera, wanda Maryam ɗin ke sanye da wata farar vest da tsawonta bai kai guiwa ba, Khamis kuma yana mata waƙar ‘Oya shake body’ ita kuma tana ta kwasar rawa suna dariya. Sosai bidiyon ya sanya ma Aisha baƙincki a zuciya, kamar za ta yi kuka ta ce,

“‘Yar iskar banza.” tare da ci gaba da kallon pictures ɗin da ke folder, wanda mafi yawanci da english gami da night wears ta yi su, wani wurin ma towel ne take ɗaure da shi, kuma da gani duk Khamis ne ya ɗauke ta.

Tura wasu bidiyos da pictures ɗin ta yi a wayarta duk don ta kai ma Zuzee ta gani, ta haka ne take ganin Zuzee za ta sama mata mafita akan Maryam.

Bayan ta gama turawa ne kuma ta bi duk wata folder da ke da hoton Maryam ta goge, cikin ranta kuma tana faɗin,

‘Komai ta fanjama fanjam.’

Tashi ta yi ta koma kan gado ba tare da ta ɗauke wayar Khamis a ƙasan carpet ba. Fata ta riƙa yi bacci ya ɗauke ta, don ta haka ne za ta samu sauƙin raɗaɗin da take ji a zuciyarta. Rumtse idanunta ta yi, sai dai hoton Maryam inda take kwance a jikin Khamis da ke yi mata gizo a idanu ne ya sa ta buɗe idanun,

“Me ya sa na gano ma kaina bala’in da zai hana ni bacci?”

A ƙasan ranta take wannan maganar tare da ci gaba da sakin tsaki.

Khamis ɗin da take mafarkin ƙare rayuwarta ita kaɗai da shi, shi ne kuma take ganin shi maƙale da wata macen,

“Kai, lallai namiji bai da tabbas.” ta faɗa a fili tare da juya kwanciyarta a ɗayar kafaɗarta ta na fuskantar bango.

Jin motsin shigowar Khamis ne ya sa ta yin lamo kamar mai bacci. Shi kuwa ba don idanunsa sun sauka akan wayarsa da ke yashe a ƙasan carpet ba, da ba abin da zai hana shi take ta.

Duƙawa ya yi gami da ɗaukar wayar, danna powar ke da wuya ya ga ba hoton Maryam a jikin screen ɗin, fidda key ɗin ya yi, a zatonsa zai ga hoton Aisha tunda sun sanya kansu aikin chanza mishi wallpaper, nan ma ba hoton Maryam ɗin bare na Aishar.

Kallon Aisha da ta ƙame kamar gawa ya yi, cikin ransa kuma yana tuhumar ta don da ta yi haka to ba ta da gaskiya. Baki ya taɓe tare da shiga gallery da nufin sanya wani hoton saboda bai son wanda ke a kan wayar.

Ganin kowace folder empty ne ya sa gabanshi wata irin faɗuwa, “Inna lillahi wa Inna ilaihir raji’un!”

Ya furta tare da duban Aisha da ke ta ɗan motsi,

“Da kyau Indodo.”

Ya sake faɗa ba tare da ya ɗauke idanunsa daga kallonta ba.

Sosai Aisha ta kama kanta, kasa kunne ta yi ta ji ko zai cigaba da faɗa, sai dai ta ji ya yi ƙwafa tare da aje wayar a kan stool.

Banɗaki ya shiga ya watsa ruwa. Da tunanin abin da zai ma Aisha wanda zai ƙuntata mata zuciyarta itama ya fito daga banɗakin.

Nafila raka’a biyu ya gabatar, bayan ya gama ya sanya kayan bacci tare da kashe fitilar ɗakin.

Gadon ya hau shi ma, sai dai ya koma a ɗayan ɓangaren. Duk wannan kwaramniya da yake akan kunnen Aisha. Lambar Maryam ya kira tare da sanya ta handsfree. Aisha kuwa na jin muryar Maryam gabanta ya girɗe ya faɗi.

Cikin muryar soyayya ya yi ma Maryam magana.

“Ba ki yi bacci ba?”

Maryam ba ta san kusa da Aisha yake ba ta ce,

“Wallahi kuwa, ka san duk ranar da ba a ɗakina kake ba bana bacci.”

Sai da ya dubi Aisha da ƙafafunta ke ta karkarwa don masifa ya ce, “Ayya sorry! Pictures ɗinki masu zafi nake so.”

Maryam ta ce,

“A wannan daren?”

Ya ce,

“Eh, ki turo mini ta WhatsApp.”

“Okay.” ta ce, sannan suka tsinke kiran.

WhatsApp ya shiga, ba da daɗewa ba kuwa Maryam ta turo mishi, hada wasu vedios ɗin da suka ɗauka a tare. Voice note ya yi mata da,

“Da nagode matata, mu kwana lafiya.”

Rufe datar ya yi, sannan ya dawo gallery tare da ɗora wani hoton Maryam mai kyau a wallpaper, sannan ya dawo settings ya chanza security ɗin wayar.

Kwanciyarsa ya yi tare da sakar ma Aisha habaici da cewa,

“Na samu wasu pics ɗin, idan mutum ya isa ya goge tunda hoton matata na sanya ba na karuwa ba.”

Sosai Aksha ta cika ta tumbatsa, kamar ta maido mishi da raddi, amma sanin ita ta fara taƙalar shi ya hana ta.

Shi kuwa cigaba da magana ya yi “Na ɗauka abin na arziƙi ne, shi ya sa ban hana duk wadda nake ɗakinta ta ɗora hotonta a wayata ba, ashe abin na tsiya ne, to na ƙara ganin an taɓa mini waya ma, mutum ya ga yadda zan yi da shi.”

Haka ya gama surutansa ba tare da Aisha ta tanka mishi ba. Zuciyoyinsu cike da jin haushin juna suka yi bacci. Washe-gari kuwa ba wanda ya tanka ma wani a cikinsu. Sai ranar da Aisha za ta je kitso ne ta fara sakin fuska tana yi mishi magana.

Can wurin ƙarfe tara ne ta biyo shi a falo tana ‘yar dariya da cewa, “Abban Haneef yau ne zan je kitson fa.”

Wani irin kallo ya yi mata ya ce, “Ba yau ba, ki bari sai gobe.” saboda ya rantse ba za ta je yau ɗin ba tunda bai da arziƙin da za ta yi mishi magana sai tana son fita.

Wani irin takaici ne ya turnuƙe Aisha, baƙar magana take son faɗa mishi, sai dai tsoron kada goben ya hana ta ya sanya ta yin shiru. Dangane da zanen gado kuwa, Maryam na shiga ɗakin ta ga nata aje a gefe.

“To wa ya cire shi?”

Zuciya ce ta ba ta amsa da,

‘Maza dai ba sa gyaran ɗaki, bare ki tuhumi mijinki.’

Yunƙurawa ta yi za ta cire, zuciya ta hana ta, share ɗakin ta yi tare da wanke banɗaki sannan ta fito.

Ɗakinta ta dosa, inda tun kafin ta shiga ta jiyo ƙarar wayarta, tana dubawa ta ga lambar Hafsat, tana ɗaga kiran Hafsat ta faɗa mata sun samu wadda za ta dafa musu waken awarar saboda yau ne za su yi, Maryam da ke jin sun rage mata aiki ta ce,

“Yauwa to, amma ku tsaya ta dafa a gabanku yadda za ku koya.” Hafsat ta ce,

“Toh Anty Maryam.”

Sallama suka yi, sannan Maryam ta fita zuwa kitchen.

Wurin ƙarfe uku ne Hafsat da Ruƙayya suka zo, aikuwa Haneef da Haneefa na ganinsu suka kama murna. A falo suka zauna, Maryam da jin muryar Ruƙayya ta fito daga ɗaki ta ce,

“Sai yanzu?”

Tare da zama a gefen Hafsat a hannun kujera.

Hafsat ta ce,

“Mai awarar ce sai yanzu ta gama.”

Lokaci ɗaya kuma ta buɗe babbar ledar da Awarar ke ciki.

Ɗaya Maryam ta ɗauka ta ce “Amma dai ta yi kyau”.

Haneefa na gani ta ce ma Ruƙayya,

“Anty Ruƙayya miye wannan?” Ruƙayya ta bata amsa da,

“Awara ce.”

Haneef ya ce,

“Tamu ce?”

Ta ce,

“Eh.”

Aikuwa ya ruga ɗakin Aisha ya faɗa mata wai su Anty Hafsat sun kawo musu awara. Aisha kuwa ido ta zuba domin ganin shigowar su Hafsat ɗakinta da awara.

Hannu biyu ta ga sun shigo, suna gaishe ta ta ce,

“Ina awarar?”

Ruƙayya na kallon Haneef da ke ta dariya ta ce,

“To kwarmato.”

Maida dubanta ga Aisha ta yi ta ce, “Ta Anty Maryam ce ta bada kuɗi a yi mata.”

“Okay.” kaɗai ta ce, cikin ranta kuma ta riƙa tunanin yaushe Maryam ta yi sabo da su Hafsat, lallai idan ta yi sake, to har da dangin mijin duk za ta ƙwace.

Su Hafsat kuwa kitchen suka dawo, cikin ɗan lokaci aka soye awarar duka. Vegetables Hafsat ta yanka, Ruƙayya kuma ta daka musu yaji mai daɗi.

Falo suka dawo domin rabon awarar, Maryam ce uwar rabo, don haka sai da ta fara fidda ma Ummansu Khamis nata, sannan ta fidda ma Khamis shi ma. Haneef da ke ta leƙen shi da Haneefa ne ya ce,

“Ina ta Mammy?”

Hararar shi Hafsat ta yi,

“An ce ba za a bata bane?”

A plate aka ba shi ya kai ma Aisha, abin mamaki sai gashi ya dawo wai ba za ta ci ba. Karɓewa Hafsat ta yi tare da faɗin,

“Ta ƙara auki.”

A kan wadda aka zuba ma Aishar ce aka ƙara ma Haneef da Haneefa. Su kuma suka haɗu su uku a wuri ɗaya suna ci. Ruƙayya da awara ta kai ma karo ta ce, “Hafsat don Allah gobe ma mu yi tunda mun ga yadda ake yi.”

Dariya Maryam ta yi sannan ta ce, “Ai fita ranku za ta yi, gara ma ku ɗaga mata.”

Wurin ƙarfe biyar ne su Hafsat suka ta fi, inda kuma shida na bugawa Khamis ya shigo gidan.

Tun kafin ya zauna Haneefa ta ce mishi,

“Daddy mun ci awara mai daɗi.” Ya ce,

“Da gaske?”

Haneef ya riga ta da,

“Allah kuwa, Anty ma ta aje maka naka.”

Duban Maryam da ke ta ‘yar dariya ya yi.

“Wai kin aje min?”

Kai ta ɗaga,

“Uhm.”

Ya ce,

“To mu je ki taya ni rage kaya sai ki bani.”

Bayansa ta bi, Haneef da Haneefa kuma suka shige ɗakin Aisha.

Rufe ƙofar Khamis ya yi, sannan ya jawo Maryam a jikinsa, ƙuri ya yi ma fuskarta ya ce,

“Na yi kewar ganin fuskar nan taki.”

Kwantar da kanta ta yi a ƙirjinsa. “Nima haka baby.”

Ɗorawa ta yi da,

“Duk yau baka waiwayi gida ba sai yanzu.”

Ya ce,

“Wallahi kuwa, ayyuka ne suka riƙe ni.”

Ɗan gyaɗa kai ta yi, sannan ta taya shi rage kayan jikinsa. Hannunta ya kama,

“Mu je ki taya ni wankan.”

Maƙe kafaɗa ta yi don duk abinta bata iya shiga banɗaki ɗaya da shi saboda kunya. Ɗan marairaice mata ya yi,

“Don Allah.”

Cewa ta yi,

“To ka shiga banɗakin zan biyo ka.”

“To ina jiranki.”

Ya faɗa tare da shigewa banɗakin yana dariya. Yana fitowa ya shafa mai tare da sanya shirt da boxer, Maryam ce kuma ta koya mishi saka su, wai ita bata son yana sa jallabiya.

Ɗakin Aisha ya leƙa ya ce, “Madam ana ɗaka.”

Ta ce,

“To me zan yi cikin yara.”

Ya ce,

“Gaskiya kam babu.”

Falo ya dawo inda Maryam ta kawo mishi awarar, yana ci yana santi saboda ta yi daɗi, daga ƙarshe ya ce shi ma sai an yi mishi saboda wannan bata ishe shi ba.

Da daddare kuwa Maryam ta zo bacci a ɗakinsa ta tambaye shi,

“Ni kam kai ka cire min zanen gado?”

Duk da ta san ba shi ba ne.

“Uwargida ce ba ni ba.”

Ya bata amsa.

Kamar yadda Aisha ta cire zanen gadon haka ita ma ta yi, sai dai ita tsanar Aisha ne ya sa ta cirewa ba tsoron asiri ba. Bai hana ta ba, sai dai cikin ransa ya ce,

‘Mata halinku ɗaya.’

Jin Maryam ta ce,

“Ni kwana a ɗakin ma ya fice mini a rai.” ne ya ce,

“Ɗakin na waye?”

Ta ce,

“Eh, ina jin haushin yadda muke sharing gado da wata.”

Dariya ta bashi ya ce,

“Ku ka yi sharing miji ma bare wani gado.”

Cewa ta yi,

“Wannan daban.”

Lokaci ɗaya kuma ta shimfiɗa nata zanen gadon. Shiru ya yi yana nazarin yadda zai kawo ƙarshen canje-canjen zanen gadon nan shi ma.

Washe-gari da misalin ƙarfe goma ne Aisha ta fito cikin shirinta na zuwa kitso. Da kanta ne za ta je kitson saboda Khamis ya ce idan ya tsaya jiranta to ba zai fita da wuri ba.

Ita ma ta fi son kowa ya yi tafiyarsa don ta samu damar zuwa gidansu Zuzee.

A falo suka haɗu da Maryam, tamkar babu wata tsanarta a zuciyar Maryam ta ce,

“Har kun fito?”

Aisha ta ce,

“Wallahi kuwa.”

“Toh Allah ya kiyaye hanya.” Maryam ta faɗa tare da raka ta da idanu har ta fi ce falon bayan ta ce, “Amin.”

Maryam na hangen sa’adda Aisha ta shiga motarta, mai gadi ne ya buɗe mata gate ta fice daga gidan.

Da daɗewa Maryam ta san Aisha na da mota, amma bata taɓa tambayar wa ya siya mata ba, duk da ta san sana’ar mijinsu ce sayar da motoci. Kai tsaye gidansu Zuzee Aisha ta nufa. Gida ne madaidaici na masu rufin asiri.

A ƙofar gida ta faka motarta, sannan ta fito ta shiga cikin gidan.

A tsakar gida suka yi kiciɓus da Zuzee, Rumgume ta Zuzee ta yi tana murna saboda in dai Aisha ta zo, to kuwa samunta ya zo ita ma, kasantuwar Aisha bata da rowa, kayanta na kowa ne, kuɗinta kuma na ƙawayenta ne, da wannan ne suka samu damar da suke cutar ta ba tare da ta sani ba, barin Zuzee ma da har ATM Aisha ke bata ta ciri kuɗi.

Itama tana murna tare da kewar Zuzee ta ce,

“Haba ai na yi fushi.”

Zuzee ta ce,

“Don Allah ki yi haƙuri.”

Karɓar jakar hannun Aisha ta yi, sannan suka shiga ɗakin Mamarsu Zuzee, zaune suka same ta a ƙasan leda tana tsintar wake.

Tana ganin Aisha ta ƙara faɗaɗa fara’ar ta,

“Aisha ce yau a gidanmu?”

Aysha na dariya ta ce,

“Ai kuwa ni ce Mama.”

Zama ta yi akan kujera tana fuskatantar Mamarsu Zuzee.

Ita kuwa Zuzee tsaye ta yi daga gefen Aisha tana ƙare mata kallo, sosai ta ji a ranta ina ma ita ke cikin daular da Aisha ke ciki da ta more.

Gaishe da Mamansu Zuzee Aisha ta yi, amsawa ta yi tare tambayar Aisha,

“Ina Hamusu da Amarya?”

Aysha ta ce,

“Lafiya lau suke Mama”

Maida dubanta ga Zuzee da har yanzu take tsaye tana kallonta ta yi ta ce,

“Hajiya kin yi tsaye.”

‘Yar dariya Zuzee ta yi.

“Wai mamakin yadda ki ka yi ƙiba nake, lallai uwargidanci ya karɓe ki.”

Sai da Aisha ta ɗan dubi jikinta sannan ta ce,

“A haka?”

Zuzee ta ce,

“Wallahi kuwa kin ƙara kyau.”

Mamarsu Zuzee ma ta ce,

“Gaskiya kam ba laifi, jikinki ya ƙara kyau Aisha.”

‘Yar dariya Aisha ta yi sannan ta ce,

“Ƙila don mun daɗe ba mu haɗu ba ne, amma wallahi Mama na rame.”

Mamarsu Zuzee ta ce,

“Koh?”

Aisha ta ce,

“Wallahi Mama, jarabar kishiya ya za a yi ta bar mutum ya yi ƙiba?”

Mamarsu Zuzee mace ce mai hangen nesa, don haka bata biye ma Aisha akan maganar kishiya ba, cewa kawai ta yi,

“Rayuwa dai sai haƙuri Aisha, dama kishiya ai ba daɗi gare ta ba, amma da kin maida ta ba komai ba za ki zauna lafiya.” Zuzee ta san halin mahaifiyarsu ba ta son gutsuri-tsoma, don haka ta yi shiru.

Soyayyen dankali da farfesun nama Aisha ta fiddo a jaka ta miƙa ma Zuzee, aikuwa tana murna ta karɓa. Mamansu Zuzee da ta ga abin da Aisha ta kawo musu ta ce, “Aisha wannan daɗi haka?”

Dariya kawai Ayshar ta yi.

Rabawa Zuzee ta yi, ta ba Mahaifiyarta nata, ita ma ta ci nata, sannan ta rage ɗan kaɗan wanda za ta aje ma ɗiyarta da ta dawo da ita bayan mutuwar aurenta. Shiryawa Zuzee ta yi, Aisha ta ɗauke ta suka nufi gidan kitso. Magana ce cike da bakin Zuzee, tambayar Aisha ta yi,

“Wai ya Amarya, ɗazu ban sa baki ba saboda Mama bata son magana.”

Baki Aisha ta taɓe tare da faɗin, “Amarya ko ‘yar iska.”

Zuzee da ke son jin haka ta ce, “Kamar ya ‘yar iska?”

Aysha ta ce,

“Toh duk ta bi ta rikita Abban Haneef, bai ganin kowa sai ita, kullum da kalar salon da za ta fiddo da shi, duk ya bi ya wani susuce a kanta.”

Jinjina kai Zuzee ta yi.

“Aisha me na faɗa miki, ai wallahi ba banza ta shigo gidannan ba, su fa Katsinawa asiri ne gadonsu, don haka duk inda suka shiga da shi za su je.”

Aisha da ke shirin danna kan motarta a layin gidan kitson ta ce, “Na gani Zuzee.”

Tambayar ta Zuzee ta yi sake yi, “Kuna faɗa da ita?”

Aysha ta ce,

“Eh to, amma dai ko cacar baki bamu taɓa yi ba, sai dai ‘yar gaba-gaba.”

Zuzee ta ce,

“Ai gara kishiyar da za ku riƙa dambacewa duk safiya, a kan wadda za ta yi asiri ta mallake miji.”

Da wannan zance suka isa gidan kitson. Ko da suka shiga gidan ma basu fasa maganar ba saboda mai kitson ta san da kwanan zancen.

Wata mata da ake ma kitso na jin Aisha ta ce,

“Ai tunda aka yi mini kishiya ‘yar Katsina, na ji na tsani Katsinawa wallahi.”

Zama matar ta gyara tare da riƙe haɓa,

“Taɓ, haɗa da ni nan wallahi, ai da a yi miki kishiya ‘yar Katsina gara mijinki ya sake ki, don wahala ce za ki ɗaura aure da ita, asiri har da na innalillahi gare su.”

Aisha da tsoro ya ƙara cikata ta ce, “Kema kishiyarki ‘yar Katsina ce?”

Matar ta ce,

“‘Yar can ce, ai tunda Baban Faruk ya auro yarinyar nan farincikina ya ƙare, tsakanina da maigida kullum faɗa, da ya shigo ɗakina ya dinga haɗe rai kenan, ita kuwa har na waje na jin dariyarsa idan yana ɗakinta. Da ta guma mana asiri ma sai Baban Fruk ya daina kusantata, banda rashin lafiyar da muka riƙa yi ni da yara, duk inda muka je neman magani sai a ce sammu ne kishiyata ta mani, don haka wallahi sai kun tashi tsaye ke da ‘ya’yanki.”

Zuzee ta ce,

“Me na faɗa miki.”

Mai kitso ma ta ce,

“Ai kuwa gara ki tashi tsaye Hajiya A’i.”

Sosai Aisha ta tsorata, nan ta tuno tsohon labarin kaza da cicciɓi ta faɗa musu. Aikuwa mai kitso ta ce, “Yo asiri ne aka yi don ya daina jin daɗinki”.

Yadda Maryam ke jan yaran ta a jiki shi ma sai da ta basu labari, Matar nan kuwa ta ce,

“To wallahi su ma yaranki ki tashi tsaye a kansu, ɗan namijin nan ana iya kashe miki shi da asiri.”

Cikin ɗan lokaci taron matan nan uku suka ƙara cusa ma Aisha tsanar Maryam, sannan suka sanya take ganin kamar Maryam da asiri ta mallaki Khamis, hatta sharar ɗakin Khamis da Maryam ta tsira, sai da suka ce yanzu haka wani abin Maryam ta ke kaiwa ɗakin, don haka ta bincika.

Tunawa Aisha ta yi da hotunan Maryam da ta tura a waya, nuna musu ta yi, aikuwa Zuzee da salon Maryam ya dakar mata zuciya ta ce,

“Anya kuwa wannan ba karuwa bace?”

Matar ta ce,

“Ba wani karuwa, tsabar salo ne kawai da muguwar kissa, ni tawa kishiyar ai ba kaya ne kaɗai bata fitowa a tsakar gida.”

Jiki a mace Aisha ta fito daga gidan kitson, ita ma matar wadda suka fara kira da Maman Faruk tare da su ta fito, musayar lamba suka yi, sannan ta tafi, Aisha da Zuzee kuma suka shige mota suka tafi. A hanyar komawa gidansu Zuzee ne Aisha ta ce,

“To Zuzee wai ya zan yi da Maryam?”

Zuzee na son kai Aisha wurin Malamai, sai dai jin yadda Aishar ta ɗan tsani Malamai ne ya sa take dannewa, cewa ta yi,

“Ke ɗin ce idan an ce ki tashi tsaye sai ki ce me zaki yi, bayan kina da abin yi.”

Duban ta Aisha ta yi tana son sanin me za ta yi? Zuzee ta ce, “Idan an ce za a wurin Malam sai ki ce A’a.”

Aisha ta ce,

“To idan na je ai mun zama ɗaya da ita.”

Girgiza kai Zuzee ta yi.

“Ba wani ɗaya, su asiri suke, ke kuma addu’a da kariya za a baki.”

Har yanzu dai Aisha bata gamsu ba, sai dai ta ce za ta ba da kuɗi a yi mata rubutu irin wancan, ba don Zuzee ta so ba ta ce,

“To, rubutun ma lafiya lau ne.”

Gidansu Zuzee suka isa, Aisha ta yi Sallah tare da da cin abinci.

Maganar biyawa da za ta yi gidansu ta yi ma Zuzee, aikuwa Zuzee ta yi caraf ta ce,

“Mu je sai in raka ki.”

Saboda akwai yayan Aisha da Zuzeen take so.

Aisha na tuna mamanta ta ce ba ta son Zuzee ta ce,

“Yamma ta yi gaskiya, mu bari idan zan je sai in biyo mu tafi, har gidan sahibinki Abdul za mu biya ma.”

Wata irin dariyar farinciki Zuzee ta yi, cewa ta yi,

“To ki sa mana rana.”

Aisha na kimtsawa ta fito da shirin tafiya, Mamansu Zuzee da ke tsakar gida ta tsaida ta ta ce mata,

“Aisha ki ɗauki Kishiya abokiyar zama, kada ki cutar da ita, sannan shi mijinki ki cigaba da kyautata mishi fiye da kina ke kaɗai, ta haka ne za ki samu farinciki mai ɗorewa.”

Sosai Aisha ta ji daɗin nasihar duk da ba ta ɗauki wani ɓangare na cikinta ba. Godiya ta yi ma Mamansu Zuzee sannan suka fito.

Kuɗin rubutun ta ba Zuzee, daga bisani suka yi sallama. Motarta ta shiga ta tafi. Khamis na zaune a dakin Maryam suna ta shan soyayyarsu, inda kuma Haneef da Haneefa suke falo suna ta guje-guje.

Ɗan marairaicewa Maryam ta yi ma Khamis.

“Don Allah yaushe zan je Kt?”

Cewa ya yi,

“Ni ban san yaushe za ki je ba Mairo, ke ɗin ce Wallahi bana son ki min nisa.”

Kamar za ta yi kuka ta ce,

“To yanzu shikenan ba ranar da zan je na ga mahaifana?”

Ya ce,

“Ba sun zo ba?”

Ta ce,

“Nima ai yana da kyau na je.”

Ya ce,

“Hakane.”

Fiddawa suka yi idan Maryam ta cika wata shida sai ta je.

Aikuwa daɗi wurin Maryam ba a magana, maƙalƙale shi ta yi tana ta godiya. Sai dai kan ka ce me sun lula wata duniyar, har Aisha ta shigo gidan basu sani ba.

A falo ta tarar da Haneefa duƙe tana kuka, a fusace ta ce,

“Wa ya dake ki?”

Haneef da ya sha jinin jikinsa ta nuna. Ba tare da Aisha ta ji me Haneefa ta yi mishi ba ta fara sauke takaicinta a kansa.

Kukan da yake ne ya ba Khamis damar fitowa daga cikin ɗakin, inda kuma Maryam ta biyo shi a baya.

Cikin ɗaga murya Khamis ya ce, “Ya daga dawowarki za ki kama dukansa, me ya yi maki?”.

Cike da jin haushinsa ta ce,

“Kun shige ɗaki dama ya za ka san me ya yi mini, yara kamar basu da kowa an barsu yashe a falo.”

Maryam ta ji ba daɗi, sai dai bata tanka ba. Masifa Aisha ta ci gaba da zazzagawa tana faɗin,

“Daga yanzu ba zan sake barin yarana ba.”

Khamis da ya lura daga can aka zugo ta ya ce,

“Gara duk inda za ki je ki tafi da kayanki, mu kuma mu huta son aranmu.”

Maryam kuwa ɗakinta ta dawo, bayanta Khamis ya biyo, da tsiya ya tilasta mata suka yi wanka. Ana fara kiran Magarib ya ja hannun Haneef suka tafi masallaci. Ana gama sallah suka dawo, Sake fita ya yi, ba shi ya dawo ba sai ƙarfe tara na dare.

Manyan zannuwan gado guda uku ya shigo da su.

A falo ya kira Maryam da Aisha ya ce su zauna, bayan kowa ta bashi hankalinta ya ce,

“To kowace ta ɗauke zanen gadonta ta maida ɗakinta, ga nawa na siyo a riƙa shimfiɗa mini a gadona.”

Sosai abin nan yayi ma Aisha daɗi. Maryam kuwa bata so haka ba, Ita ke aiki, don haka ita ya ce ta kai zannuwan gadon ɗaki. Duban Aisha da ke ta cika ya yi.

“Madam rowar kitson ake mana.”

Lokaci ɗaya kuma ya ta so ya zo gefenta ya zauna.

Hannunta ya kamo ya ce,

“Ya yi kyau ba kaɗan ba.”

Cike da jin daɗin yabon ta ce, “Na gode.”

Yana cikin duba kitson ne Maryam ta fito daga ɗakinsa.

Sosai ta ji kishin yadda yake ta wani santin kitson, amma sai ta danne ta ce,

“Amma dai yayi kyau wallahi.” Murmushi kawai Aisha ta yi, cikin ranta tana jin ba abinda Maryam za ta yi wanda zai burge ta.

A kwana a tashi ba wuya wurin Allah, Maryam ta cika wata shida daidai, inda kuma ta fara shirin tafiya gida. Kitso, ƙunshi duk ta yi, sannan ta yi ma su Haupha da Umman Khamis bankwana.

A daren tafiyar ne Khamis ya lura da ta kasa bacci. Jawo ta ya yi a jikin sa.

“Ni ina kukan za ki yi nisa da ni, ke kuma kina murna ko.”

“Gida daban ne baby, amma ina jin ba daɗi a raina nima.”

Ya ce,

“Ai ba za ki daɗe ba, sati biyu ne ko?”

Ta ce, “Uhm.”

Kwana suka yi suna faranta junan bankwana.

Washe-gari tunda Asuba Khamis ya kai ta tashar mota, sai da ya tabbatar da motarsu ta tafi sannan ya dawo. Aisha kuwa a ranar ji ta riƙa yi kamar ta rabu da ƙaya, a ranar kuma sai da Zuzee ta zo gidan.

Cike da murna Aisha ta ce, “Wallahi na huta kafin ta dawo.” Zuzee ta ce,

“To kin san wane ƙulli kuma za ta dawo da shi?”

Nan fa ta riƙa ce ma Aisha Maryam na iya dawowa da wani ƙullin asiri. Da ta ga Aisha ta tsorata sai ta ƙara zuga ta wai su buɗe ɗakin Maryam su bincika ko za su ga wani abu.

Aisha ta ce,

“Abban Haneef ya kusa dawowa ai, ki bari sai gobe sai ki dawo mu buɗe ɗakin, ni dama ban yarda da ita ba wallahi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kishiyar Katsina 7Kishiyar Katsina 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×