Skip to content
Part 17 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Dan iskar da aka samu kwana biyu ba tare da anyi ruwa ba yasanya garin yin zafi, wannan yasa da yawan mazan unguwar firfitowa kama daga matasa har dama maginta ko ina ka bi cikin unguwar maza zaka gani wasu bisa bencina wasu bisa tabarmi kowa da abinda yake, can gefen kwata bakin wani kanti bencin su Muktar ne shida abokan sa da suke zaune gefen teburin da Ibrahim ke saida kaza soyayyiya, kilishi, da dambun nama.

Nasir da ya ƙara so wurin ɗauke da katuwar baƙar leda ne ya zauna ƙarshen bencin tare da faɗin “wash! Allah yau na gaji da yawa” Salisu ne ya ɗan leƙo kai “kai dai walllahi ka cika ragon ta in ba haka maine abin gajiya a wannan ƴar ledar da ka ɗauko?”

Hararar sa Nasir ya yi “ai gwamma ni da baki kawai na ce na gaji kai na tabbatar sai dai kama faɗi wanwar”

Muktar ne yasa dariya “kai dai Nasiru baka mutunci mai ka maida Salisun ne?”

Nasir bai bashi amsa ba ya hau fito da atamfofi cikin leda yana faɗin ” Haja ce na kawo muku dukan mu nasan kayan aure muke haɗawa”

Ibrahim da ke gaban glass ɗin da kayan sana’ar suke yana zubawa matashin saurayin da ya zo siyan dambun nama da doya ne ya yi caraf ya ce inason jar can zatawa Fiddausi na kyau” ya faɗa yana ninke takardar da ya zuba doya.

Salisu ne ya zuro hannu zai ɗauka Nasir ya yi caraf ya ce “koda bashi bani baka, kuɗi hannu nake bawa marasa sana’a”

” Kut.. wai mai kuka maida ni ne?” Salisu ya faɗa a fusace.

Ibrahim da ya komo ya zauna ne ya ɗauki jar da yace yana so yana ƙara ɗaga ta cikin hasken street light “anma atamfar nan ta yi kyau, bama zan sa a lefe ba gobe zan kai mata, in haɗa mata da kwanukan da tayo min cin cin” ɗan juyowa ya yi ya kalli Salisu mutumina kabi shawarar Muntari ka kama sana’a walllahi”

Banza Salisun ya masa tare da ci gaba da ƙoƙarin kama tasha a radiyon sa.

Nasir ne ya taɓo Muktar da tunda aka fara batun kayan baice komai kan su ba yace ” ya mutumina banga kafa ɗauka ba?” Murmushi Muktar ya yi abin ai na masu ƴan mata ne.

Nasir ne ya ɗago wata golden ɗin atamfa ya ɗora kan cinyar Muktar wannan ko fara ko baƙa zata mata kyau ina faɗa ma, kama daina wayancewa ni namiji ne nasan duk nunƙufurcin mutun dole akwai wadda yake ɗan tayawa”

Kallon atamfar da ke cinyar sa ya yi, bai ankara ba zuciyar sa ta fara zayyano masa Hafsa cikin atamfar cikin sauri ya mayarwa da Nasir kan cinyar sa, ” aiko kai namijin ƙarya ne tunda dai bakasan da irin mu ba wanda sam soyayya bata gaban su”

Dariya Nasir yasa tare da mayar masa atamfar ” ka rantse da Allah babu wadda kake so”

Shiru Muktar ya yi tare da shan kunu, Salisu ne ya zuro kai “ka rantse mana” ya faɗa yana tsare Muktar da idanu.

Tsuke fuska Muktar ya kumayi lokacin guda zuciyar sa na ayyano masa Hafsa yanzu da ya yi tunani mai zurfi ya fahinci bawai iya burgeshi yarinyar kawai take ba, har da ɓurɓushin so duda shiɗin baisan ya son yake ba.

” Sabida mai zan rantse, abinda na sani shine dai kawai ba wanda nake so”

“Wai kana nufin wannan tsuke fuskar zai sa in ƙyale ka,” Salisu ya faɗa tamkar da shi aka fara musun tun asali.

“To karma ka kyale ni mana” Muktar ya faɗa, nefa da yaran da ke ɗan wasa tsakanin hanya suka faɗa suna tsalle ya bawa Muktar damar miƙewa bayin Allah sai da safen ku dama zafi ya fito dani”

Nasir ne ya yi saurin miƙewa ya danƙa masa atamfar kaban kuɗin ƙarshen wata,” numfashi ya furzar tare da kallon atamfar kamar zai maido masa da ita sai kuma ya juya ya yi gida.

Wutar nefan da aka kawo ta haske tsakar gidan su Inna na zaune tana kwaɓin fanke Juwairiyya na Feraye kabewa yasan ta abincin safen gobe ce yayin da Hajara ke rubutu ya yi sallama kusan dukkanin su suka amsa.

Hajara ta ɗago ne ta ce “lah yaya mai ka siyo?”

Hajara ta tambaya cewa ya yi “Idon matambayi,” Juwairiyya tasa dariya inda Hajara ta yi ƙas da kai tana zumɓura baki. Gefen Inna ya aje ledar tare da faɗin “Nasiru ke siyar wa na ɗaukan miki wannan in kalar bata miki ba sai ince ya kawo ki zaɓa”

Da rawar jiki Inna ta buɗe “kai masha Allah, ai ta yi sosai gabaki ɗaya suka faɗa, albarka Inna ta hau sa masa tamkar ya siya mata duniyar nan yayin da shi kuma yake ta faman murumushi da faɗin “Amin”

Ɗakinn sa ya shige yana sauraron Addu’oin da Innar ke masa idanun sa bisa fanka da ke kaɗawa baima san sa’adda bacci ya yi gaba da shi ba.

*****
Tunanin yadda zata iya koyan electricity and magnetism ɗinnan ne duk ya cika mata rai, mafita ɗaya ta faɗo mata shine Uncle Muktar, inda tasan course ɗinnan zata faɗi ɗin da gaske, da tuni tun suna hutu da take zuwa da zaman hira da suke lokacin break da tuni tasa ya fara koya mata, sai dai yanzu babu dama tunda sun koma makaranta, next week zasu fara lectures gobe ko jibi take son siyi handing over da malamar da zata rike ajin da take.

Sam ta rasa mai yake mata daɗi, karatu da BUK ɗin duk tabi ta tsane su, dama ba son Agric ɗin nan take ba, tsaki taja ita dama art take tasan ba za’a bata Agric ba.

Yunwa da ta fara tambayar ta yasa ta miƙewa ta kunna fitilar ɗakin ta dan tunda ta shigo ta yi sallah take kan daddumar bata ko motsa ba tun bayan sakon da ta turawa Aunty Halima, ranta sam babu daɗi ta daure ta fito falon fatan ta kar ta haɗu da kowa har zuwa gobe ta samu ta koma gidan Gwaggo.

Hango ta da Khalil ya yi wanda yake ta fama wasa shida ƙanwar sa khairi ne ya rugo da gudu yana tsalle yana faɗin “Aunty Hafsa shine kika tafi kika barni ko, yau she kika dawo?”

Jin Khalil ya anbaci Hafsan ya sa Abba juyowa ” Hajiya Hansatu ashe kina gida?” Daurewa Hafsan ta yi ta ƙaraso.

“Abba sannu da gida” ta faɗa kallon ta yi damuwar da ta bayyana a fuskar ta yasa shi shima damuwa kafin ya ce wani abu Momy ta fara faɗa.

“Eyye sannu issasshiya, wato har kin yi girman da zaki shigo gidan nan ki kasa cemun kin dawo, eh ba laifin ki bane laifin jami’a ne eh ai dole kiji kin isa tunda kin shiga University”

Tun ɗazu da Hafsa ta gano result ɗin ta take son yiin kuka ta kasa sai yanzu faɗan Momy duk yadda takai ga daurewa na kar kukan ya kwace mata sai da ya kufce mata, aiko kamar ta tunzura Momy ta inda ta shiga ba tanan take fita ba.

Abba ne ya ce “Dan Allah Hadiza ki kyale ta, jarrabawar su aka sa ta samu CO bawai faɗan da kike mata ne yasa ta kukan ba” ganin da ya yi ta kuma tunzura kan Hafsan ta shagwabe daga ɗan faɗa ta hau kuka yasa shu faɗin haka, zaton sa hakan zai sa ta yi tausaya ta yi shiru bai san tunzura ta ya kuma yi ba.

Miƙewa ta yi tana faɗa tana faɗin ” retake fa kace, ke yanzu ahaka da kike cewa zakiyi medicine din, ai Allah ya taimake ni da can kike da kunya ta ishe ni, ki na dai kallon Sajida ita ce best student a faculty ɗin su”

Takaici ne ya kuma kama Hafsa ta tsani a dinga haɗata da wasu a rayuwar ta, bacin haka ai kowa da irin tasa kwakwalwar.

Abba ne ya ce “dan Allah Hadiza ki kyale ta, bacin ma haka ai GP din ta mai kyau ne in ta dage next semester ta samu GP irin wannan CGPA ɗin ta zai kyau kafin su shiga lvl two din zan wa Malamin da yake koyawa yaran mu Physics magana ya dinga zuwa gida lahadi yana koya mata har na second semester ɗin da zasuyi”

Bawai baƙin cikin samun CO ɗin ne ya bar ta ba, a’a sai dai anbatar Muktar zai dunga zuwa gida koya mata ne ya kwantar mata da hankali, farin ciki ya ɗan samu a zuciyar ta, murmushi ta yi na gode Abba ta faɗa tare komawa wurin da ake aje abinci ta ɗiba Inda Khalil yabi bayan ta cike da murna Khairi tasa kuka Abba ya ɗauke ta yayi ɗakin Hafsan.

Momi ta ja tsaki sam lamarin Hafsa takaici yake bata, ko wata ba’aiba Hajiya Sa’adatu mahaifiyar Hidaya ta gama cika mata baki Hidayan bata samu matsala ba, itama jira kawai take a kafewa su Hafsan ta take taje ta zayyana mata, komai ta tuna oho ta kuma jan wani dogon tsakin tare da faɗin aikin banza..

<< Ko Da So 16Ko Da So 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×