Harabar makarantar cike take da hayaniyar yara suna ta wasa da ciye ciye sakamakon sports day din da sukayi da yake ranar juma’a ce. Yan red house sune team din uncle Mukhtar kuma su suka cinye. A gajiya ya samu wuri ya zauna sannan ya dauki ruwan gefen sa ya fasa yana sha idan sa akan daliban.
Lokaci lokaci daliban sukan wuce ta gaban shi su masa hi sannan su wuce. Murmushi ne ya kubce masa ganin yadda malamtar dai da aka raina tafi komai jawowa mutum farin jini a wajen yara in yayi ta yadda ya kamata. A yanzu yaran har kallonsa suke yi a matsayin abun kwaikwayo. Hakan yasa yaji son yaran da koyarwar ya kara shigar sa sosai. Jin su yake kamar kannensa ne.
Yana kallonsu ne idonsa ya fada kan wani yaro dan ss1 Umar Sadiq ya kifa kan shi a kan gwiwar sa. Yaron dama sam bei cike walwala ba da surutu kuma komai nashi shi kadai yake yi. Ganin kowa yana tare da yan team din sa yau shi kuma ya ware yasa uncle Mukhtar jin babu dadi. A hankali ya taka inda yake ya dafa kafadar sa.
“A minute?” Ya tambaya, yana kallon yadda idon yaron yayi ja duk da ba kuka yake ba. Ba musu ya bishi.
Mukhtar ya gyara murya. “You can trust me.” Ya fadawa yaron wanda yanzu yake kallonsa da alamar shakku a ranshi. Ajiyar zuciyarsa kawai yaji sannan ya dan yi shiru yace.
“Failure has always been my identity. Nasan saboda a yellow house nake shiyasa muka fadi…” Mukhtar ya zuba masa ido cike da mamaki da rashin sanin abun cewa.
Ya dafa shi. “Why do you think so?”
Umar ya daga kafada sama sannan ya tabe baki. “Babana ne ya gaya min. Kuma it’s true. Ko fifth position ma ban taba yi ba. Whenever i want to focus, my whole attention freezes. Sai naji ba zan iya ba. Ko yau ma ina tsoron gaya mishi we failed.”
Mukhtar ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa yana nazarin ta inda zai soma. Shi malami ne kuma his opinion matters. Yara suna kallon malaman su tamkar iyayen su ne kuma tunda uban wannan yaron ya sanya wa yaron gwiwa, shi ne in a good place ya karafafa masa gwiwa.
“Yadda nake gani ni kuma shine your future is bright. I wish dama ni ne kai, all qualities of perfection ka hada su you just need a little push. Ka san waye zai yi pushing dinka?”
Ya girgiza kan shi. “Kai ne. Kai zaka gayawa kanka zaka iya because no matter what, sai ka fara yadda da kanka zaka iya cimma wani abu. Ka sani na yarda zaka iya, all teachers ma naji suna zancen ka rannan a staff room. They all wish sune kai saboda yadda kake daban a dalibai. Ba hayaniya, ba surutu, just goodness.”
Yaron yayi murmushi ya gyada kai. Uncle Mukhtar ya cigaba. “Baba kuma yana gaya maka hakane saboda yana so kafi shi.”
Umar ya zare ido. “He’s a great man fa. Major general ne.”
Mukhtar yace, “wow, he’s pushing you to do better in his own language.”
Umar yaji dadi yace, “I will try. But please don’t tell anyone not even him akan maganar mu.”
“You have my word.” Mukhtar ya bashi amsa sannan yaron ya mike da fara’ar sa. Daidai lokacin mahaifin Hafsah ya shigo school din.
Yara da yawa suka je suna gaishe shi. Malamai ma duk suka je suna gaishe shi yana amsawa. Mikewa Mukhtar yayi cike da jin nauyin mutumin ya taka har inda yake sannan ya russuna yana mika masa hannu su gaisa.
“Yauwa uncle Mukhtar dama saboda kai na shigo. Gashi ma lokacin masallaci yayi. In ba matsala, ka bini zuwa masallacin, akwai maganar da nake so muyi.” Mukhatr ya daga kai ya kalle shi saboda yaga ko mene dalilin neman sa amma ya rasa. Gaban shi ya fadi, Allah yasa ba wani abu yayi ba.
“Yes sir. Let me round up.” Da nauyin zuciya ya juya ya nufi staff room inda shi kuma mahaifin Hafsah ya shiga zaga school din yana jin dadin yadda komai yake tafiya. Shi mutum ne mai son farantawa jama’a. Mutum ne me kaunar taimako.
*****
Bilkisu ta jima tana kallon Hafsah kafin ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Bata taba ganin Hafsah a damuwa makamancin wannan ba. Duk sai taji rashin dadin zuwan ta yau. Da ta nutsu ai tuntuni zata zo tayi wa Hafsah jaje ta kuma bata baki.
Sam babu walwala a tattare da ita. Babu wannan kuzarin da surutun da take ciki kullum. Duk yadda Bilkisu take tunanin abun ya wuce nan da tazo ta ganta a haka. Kwallar idonta ta goge sannan ta sake kallon Hafsah wadda fuskarta ce kadai a waje inda sauran jikinta yake lullube da bargo.
“Haba besty…” ta soma amma Hafsahn ta katse ta.
“Ni don Allah ki kyale ni da zancen makarantar nan. Dama can ba sonta nake yi ba.” Ta juya kanta ta fara hawaye
Duk yadda suke da Bilkisu haka tayi tayi Hafsah bata kula ta ba har ta gaji ta tafi gida ganin magariba ta taho.
Baccin da ya sace Hafsah me nauyi ne hakan yasa ta kai kusan isha bata farka ba har sai da mummy ta shigo tana buga filonta.
“Sannu isasshiya. Wato ma bacci kike maimakon ki tashi ki fara biitar course din da kika fadi ko?”
Cike da kunci Hafsah ta juyo. Kafin tayi magana sai ga Yaya Sadiq nan ya shigo dakin. Ganin sa yasa taji dadi ba sai ta amsa mummy ba.
“Allah dai ya shirya mana.” Mummy ta fada tana ficewa da bacin ran da take ji yafi ma na Hafsah din. Yarinya sam baudaddiya. Ana nuna mata gabas kullum tana kallon yamma. Badon kamanni ba sai tace canjo mata ita akayi a asibiti don duk wanda jinin ta yake yawo a jikinsa kamata yayi ko ba duk ba, ya dauko wani abun a halinta. Ko Sadiq ma yana da wasu dabi’unta amma Hafsah? Hnmm.
“Hey…” Sadiq ya fada bayan mummy ta fice. Hafsah ta mike zaune tana kallonsa ta gaishe shi muryarta a dashe.
“Wai duk carryover dince ta maida ki haka?”
Ta tabe baki. “Damuwar yadda zan gyara tafi yawa da yadda ba zan sake disappointing dinku ba. Kowa a gidan nan is perfect. Kalli Bilkisu ma. Ni kuwa komai nawa takes its own shape duk yadda naso na tsara shi ba ya yi.”
Ya kalleta cike da tausayinta ya rungume ta. “You’re different shiyasa. Kuma don dai wannan daya, ki kalle shi da positivity watakila Allah ya boye miki wani abu babba ne a karkashin lamarin. Ke dai kawai embrace it with good faith, okay? Ki dauke shi a matsayin jarabawa da kuma albarka… ko da kuwa ke baki fahimci menene hikimar ba…”
Hafsah ta gyada mishi kai. “Shi yasa nafi son ka. Your wife is one lucky girl.” Yayi dariya kadan.
Hafsah ta turo baki tace, “Amma only when you’re not bossy like…”
Ta kalleshi ta kumbura fuska da murya irin yadda yake yi.
“Ke Hafsah, kawo min ruwa kuma in kin zo ki ajiye ki juya.”
Duk suka sa dariya sannan suka fara hira har ma ya ja ta waje suka fita suna hira.
*****
Tunda ya dawo yake tunanin offer din da aka bashi na koyar da Hafsah ranar lahadi. Zuciyarsa har tsalle take yi saboda murna. A gefe guda kuma tunanin yadda yanzu zai zama bashi da wani isasshen lokaci ne yake masa yawo. Kannensa mata ne kuma suna bukatar idonsa ko da yaushe musamman ma Hajara da yaga duk fadan sa ba zai chanja mata ra’ayi ba.
Juyi yake a kan katifar amma ya kasa yanke shawara. Yana so ya taimaki Hafsah amma yana duba gidansu. Family first, family over everything. Ganin dai duk yadda zaiyi ba zai iya shawara shi kadai ba yasa ya nufi dakin kannensa. A karon farko da zai tambaya shawararsu ba ta Inna ba.
Saboda yasan Inna cewa zatayi kawai yayi.
Zaune ya same su suna hira ko wacce ta amsa sallamarsa. Fitilar kwan dake ci ya kalla yaga hasken babu yawa sannan yace.
“Fitilar ma sai an gaya muku kun kunce ku wanke kwan ko?”
Juwairiyya ta kada kai. “Ai wankin Hajara ne kasan kuma duk sanda ta dauka sai ta fasa.”
“Wallahi yaaya karyane. Itace fa ta fasa dayan.” Ganin zasu fara musu yasa ya daga hannu.
“Duk ba wannan ba. Ni kawai shawara nake baku ku zama masu tsafta kafin kuje gidan ku. Musamman ma Hajara da naga Garban nata dan gaye ne…”
Hajarah ta sunne kai kasa ita kuma Juwairiyya ta kwashe da dariyar tsokana. “Tab Yaya wannan garan? Kayan miya yake tsaidawa fa…”
Hajarah ta harare ta.
“Bar ta Hajarah ai ita ko mashinshini babu.” Hajarah ta kwashe da dariya sannan ta mata gwalo tace,
“Sana’a sana’a ce dai. Kuma gonar ma tashi ce a wajen sa da yawa suke sarar kayan miya. Ko ba komai ba zan kwana da yunwa a gidan sa ba. Ehe…”
Kallon da Mukhtar ya musu ne yasa ba wadda ta kara cewa komai. Nan ya shiga gaya musu yadda sukayi.
“Maganar karin dubu ashirin akeyi amma kunsan kasancewa tare da ku yafi min dubu ashirin.” Suka yi murmushin jindadi sannan suka ce.
“Mu ma muna son ka.”
“Amma Yaya babu komai ka karba kawai in da wata matsalar daga baya ba sai ka ce ka fasa ba?” Juwairiyya ta fada.
Hajarah ta yi shiru sannan tace, “Ni dai kar aje a siye mana yaya. Kasan masu kudinnan.”
Sukayi dariya sannan ya mike.
“Toh zan dai yi tunani.”
Da haka ya bar dakin ya koma nashi ya kwanta. Kaso me yawa ya tafi ga karban aikin a ransa inda ragowar kason yake makale da family dinsa…