Tunda Hafsa ta dawo gida ranta yake a cinkushe, kasa daurewa ta yi, ji take kamar ta sa kuka saboda damuwa, tunanin Muktar da halin da yake ciki duk ya cika mata rai, miƙewa ta yi daga gadon da take kwance ta nufi wardrobe ɗin ta, doguwar riga milk da ta sha adon zaiba ta zaro ta sanya kafin ta fice daga ɗakin.
Falon Mum ta leƙa, bata ciki da alamu tana bed room, daurewa Hafsa ta yi ta ƙarasa “Momy zani Babban gida ganin babin,”
Mum da ke kwance ta ɗan ɗago, “naga shekaran jiya kinma fi yau dawowa da wuri, anma still kika ce kin gaji bare yau da kuka kai yanma”.
Fuszar da Iska Hafsa ta yi, “ai Mum gani nayi inna biyewa gajiyar nan sai baby din ta yi wayo banje ba,”
“sai kin dawo” kawai Mum ta ce ta maida kanta jikin filo.
Ko mai ta tuna kuma oho, zumbur Mum ta miƙe tare da fitowa tana ƙwalawa Hafsa kira wadda ta ja ta tsaya a falo tana roƙon Allah yasa kar Mum ta ce mata ta bari sai gobe, dan zuciyar ta zata iya bugawa kan tunanin ko ya jikin Muktar ɗin yake.
“Kin ɗauki kayan barkar da nace ki kai mata kuwa?”
“Af kinga na manta, da sai naje duk kunya ta ishen nazo hannu rabbana,”
Juyawa kawai Momy ta yi inda Hafsa ta ɗauko ledar kayan jariran da Mum tasa aka kawo mata daga ɗaya cikin shagunan ta.
A harabar gidan nasu ta ci karo da Yaya Usman ya dawo, kallon agogon da ke dantsen sa ya yi kan ya ce “Malama ina zaki da magaribar nan?”
“Sannu da zuwa yaya ta fara faɗa, kafin ta ce “Babban gida zani barka kullum ba lokaci.”
“Ki Bari gobe sai muje nima ina so in je ban samu dama ba.”
Girgiza kai ta yi “No yaya jibi ina da test inna ce zanje gobe bani da damar karatu,” ta yi ƙarya dan tasan abinda kawai zata ce kenan ya barta.
Ɗan shiru ya yi inda ta yi gaba cikin daƙiƙu ya juyo “muje kawai naci abinci acan,” ya faɗa tare da danna remote ɗin motar sa da ke hannun sa, kujerar gaba mai zaman banza ta zauna inda ya shiga tare da jan motar suka bar gidan.
Wayar sa ya zaro tare da fara kira, minti kaɗan aka ɗaga, “Please Mabaruka ɗan bawa Hajiya wayar,” abinda ya ce kenan kafin daga baya ya ce “Hajiya ina wuni?” bayan ya ɗan yi shiru da alamu na ta amsa gaisuwar tasa ne, sai kuma ya ce “dama yanzu zamu zo walllahi, yunwa nake ji Please kisa a ɗan tuƙan samo ko da miyar dage dage ne na ci, ah da akwai ma miyar kuka kenan ya faɗa yana murmushi tare da cewa sai mun zo.” Indai son tuwo miyar yauƙi ne to wurin Usman ba daga nan ba.
Hafsa da tunda suka hau titin ta langaɓar da kanta jikin glass ɗin tagar motar idanun ta a lumshe ya kalla kafin ya ce “Hafsa mai ke damun ki ne?,” Ahankali ta buɗe dara daran idanun ta ta ɗora su a titi kafin ta ɗan gyara zama, “ba komai yaya kawai na gaji ne yau sosai.”
“Ni kinsan banson ƙarya, kinsan nasan ƙarya kike tunda kuwa ko Momy ba zata nuna min sanin halin ki ba.”
Murmushi ta yi “to dai yau baka fahincen dai dai ba sam.” Ta faɗa tare da komar da kan ta jikin glass ɗin.
Muryar sa da abin ya ce ne suka daki kunnen ta aɗan razane ta kalle shi kafin ta basar.
“Soyayya kika fara?” Shine abinda ya ce hankalin sa kusan rabi kanta.
Daurewa ta yi ta janyo nutsuwar ta danma kar ya gano dan tun jiya ta gama yadda soyayyar Muktar ta gama kama ta, a nutse ta yi murmushin ƙarfin hali “No Soyayya da wa?” Nida ba ni da saurayi, kawai school ɗin ce ba daɗi sam karatun na ban takaici, kaga last semester na faɗi electricity ga this semester shima Physics ɗin ba daɗi, ga Mum ta kafe sai dai a dena min lesson ɗin nan, kuma wallahi ina fahinta tunda da akayi test ɗin ma nayi ƙoƙarin amsawa fiye da last term da banma gane mai ake a electricity ɗin.” Ta faɗa fuskar ta na nuna alamun rashin jin daɗi da damuwa.
Da alamu Usman ya yadda ɗari bisa ɗari kan cewar damuwar Physics da hana lesson ke damun ta, ganin sun zo dai dai gidan Kakan nin nasu yasa shi cewa cikin sanyin murya karki damu?, “Zanma Mum magana zata bari a cigaba tunda ai daga level one ne da kin tsallake shikenan.”
Murmushi tayi duda tana cikin danuwa, anma sai taji sanyi cikin ranta da yace zai maganar tasan Usman yasan takan shawo kan Momy tuni zai mata surutan da zata amince, aƙalla zuciyar ta zata samu nutsuwa in tana ganin Muktar ko ba soyayya suke ba.
A farfajiyar gidan suka faka, kafin su nufi ɓangare mai haihuwar gidan, shiru sai da suka ɗan yi tafiya suka isa ɓangaren bugu ɗaya yaro yazo ya buɗe yana ganin Hafsa yasa murna “Aunty Hafsy sannu da zuwa”
Usman yace “ah lallai Mashkur wato ni baka sanni ba ko?”
Dariya yaron ya yi sannan yace “yaya Usman sannu da zuwa” suka shiga ciki.
A falo inda yaran gidan ke kallo suka zauna, Basma ce ta leƙo goye da Jaririya “Hajiya Hansatu Ummi ta ce ku shigo ciki,”
Harar ta Hafsa ta yi “Madan ki fita idona tom” dariya Basma ta yi ta shige ɗaki, “Allah kin ci darajar goyon dake bayan ki da sai na mauje ki.” Hafsa ta faɗa bayan sun shiga falon.
Ummi da ke kwance ta ɗan yunƙura Basma ta ce “Ummi yi kwanciyar ki tunda in kin zauna cikin ke murɗawa.”
Usman ne ya yi saurin cewa “yi kwanciyar ki Ummi” kafin ya ce “Ina wuni an samu ƙaruwa Allah ya raya, ya karo lafiya.”
Daga kwancen ta ce, “amin Usmanu ɗazu da Sadik da ya sauke Ameerah nake cewa kana ina?, ashema kana tafe.”
“Eh walllahi tun da Momy ta ce tazo nake cewa zan zo sai yau ina Jaririyar?” Ya tambaya.
Basma ce ta ce “ka ganta tun ɗazu take kuka ita kuma Ummi bata jin daɗi, shine na goya ta,” Basma ta faɗa bayan ta gaishe shi.
Sai a lokacin Hafsa ta samu damar yin magana bayan ta gaida Ummi, ” kai har an fara goya ta.” Ta tambaya cike da mamaki
Murmushi Basma ta yi “kai tun shekaran jiya na fara goya ta, kuka ne da ita, Abba da yazo jiya yace ke ma haka kike gado ta yi.”
Tsuke fuska Hafsa ta yi “ni ai ko a yanayina so simple haka kowa yasan bani ta yo ba, kuma ai ni yayar ta ce ba’a gadon yaya,” haka sukai ta faman musu Usman ya ce su taso su shiga cikin gida wurin Hajiya tunda Ummi ta samu bacci.
Hajiya Babba na zaune suna kallon zee aflam, tana ganin su Usman ta washe baki Ameera da ke kwance tana karanta wani English Novel ta ɗago “a’a kace gwanda da ban tafi ba, yau she rabo.”
Gaisawa sukai Usman ya gaida Gwaggo kafin ya juyo ya ce da Ameera “ina wuni?,”
Dariya ta fashe da shi “kai yaya Usman karka sa in fara tunanin na tsufa, ɗauke gaisuwar ka, ka amshi tawa ina wuni” ta faɗa tana ƙoƙarin tashi zaune.
“Tsufa na nawa kuma ai tunda kika auri dattijo kamar yaya Sadik kin zama gwaggo Amira, ya faɗa lokacin da ya zauna tare da faɗin wash Hajiya ina tuwon nawa?.”
“Kubra ka wo masa tuwon nan,” Hajiya ta kwala mata kira
Ameera ce ta turo baki “walllahi mijina ba Dattijo bane, da me ka fishi yarinta ai ko yanzu aka jera ku shi ƴan mata zasu ɗauka.”
Murmushi Hajiya ta yi “ai ba sai kin faɗa ba shima yasan gaskiya, jibi yadda ya ragwaggwaɓe kamar wani ɗan shekaru sittin.”
Tuwo Usman yakai baki kafin yace “Haba Hajiya ya zaki shigarwa Anti Ameera sai ta rainani,”
Duka Hajiya ta kai masa matar wan Naka ce zata raina ka, yayin da Amira ta ce Hajiya gaskiya kice wannan ƙaton saurayin ya daina ce mun Anti.”
Miƙewa Hafsa ta yi ta wuce ɗakin Hajiya, cikin sauri Hajiya ta miƙe “bari in bi bayan yarinyar nan kafin ta kassarani,” suka sa dariya.
Tana shigs tagan Hafsa na dudduba kaya ta aje wasu gefen gado, Hajiya na shigowa ta ce “yawwa Hajiya waɗannan zan tafi da su.”
“Hansatu mai kika mai dani? Wato ma zaki tafi da su, dariya Hafsa ta yi lokacin da take zuba kayan cikin leda, karki damu zan kawo miki kwance in sun tsufa,”
Dariya Hajiya tasa kafin tasa salati, nikam ina ganin ta kaina wato nida kaya na za’a kawon kwance,” ta faɗa Hafsa ta yi kamar bata ji taba ta ratse ta gefen ta ta fice.
Sai wurin Tara suka wuce gida, Usman ɗauke da sauran miyar yace “in yaje gida gobe sai ya tuƙa tuwo yaci” ita kuma Hafsa ɗauke da ledar kayan da ta ɗebo, Sadik sai faman tsokanar su yake sun zama masu fashi wa yar tsohuwa, yayin da Amira ke faman tsokanar.
*****
Kasancewar tun a makaranta jikin Muktar ya yi zafi yasa aka bashi hutun sati, duda bai naima ba, ba laifi hutun ya taimaka sosai, ya ji jiki kusan abubuwa suka haɗe masa ga zafin zazzaɓi ga ciwon son da ya rasa tadda zai dashi kullum tsoro cika masa zuciya yake, yasan shi jarumi ne, sai dai wannan Soyayyar tana ƙoƙarin sawa ya gaza yadda da jarumtar tasa, yana jin tsoro kamar ya taro wa kansa abin da yafi karfin sa ne, in ya tuna da Hafsa da asalin sa yana jin shi akaran kansa yaso kansa, bai kuma kyautawa kan sa ba da ya faɗa soyayyar Hafsa wadda bazai taɓa ganin laifin ta ba in har ta ce bata son sa.
Zaune yake a ƙofar gidan su cikin farar Jallabiyar sa ƙarfin jikin da ya ɗanji sabida Inna ta takura masa ya haɗiɗi tuwon masarar da ta tuka masa da zafin sa yasa ya iya fitowa, duk ya faɗa baka ganin komai a fuskar sa sai dogon hancin sa da dara daran idan sa dama shi ba gwanin ƙiba ba.
Salisu ne ya ƙaraso wurin riƙe da kwano, ganin sa a ƙofar gida yasa shi tsayawa tare sa sakin murmushi, hannu ya bashi suka gaisa bayan ya masa sallama, kwanon ya aje gaban Muktar kafin ya zauna, “Alhamdulillah jiki ya yi kyau walllahi jiya da kai na kwan raina sai da nayi danasanin mai yasa jiya ban zauna na kwana anan ba.”
Murmushi Muktar ya yi “kana dai tsoron kar yau a aiko ma na cika,” ɗan ƙaramin tsaki Salisu ya yi kaji ka ana zaune ƙalau zaka kawo mana batun mutuwa, kwanon da ya aje ya janyo “kunun kanwa ne, da zafin sa sosai your favorite, ina ganin yau shi Umma ta yi na ce ta zuban na tawo.”
Girgiza kai Muktar ya yi “na ƙoshi komai naci Salisu ɗaci yake mun sam ban son cin komai dakyar naci tuwo ma wallahi.”
“Ko ba ƙoshi ba?, to walllahi sai ka sha ko darbejiya kake ji, shiru kawai Muktar ya yi ya bude ya hau sha dan yana ɗaya daga ɗabi’ar su duk wanda ya rantse ɗayan kawai haƙura yake ya yi.
Sai da ya ɗan sha zafin kunun yasa ya iya sha da ɗan yawa, sannan ya aje yace kasan “ina ta so in same ka muyi magana kan Hajara da Garba yazo ya samen yace shi ya yadda ta yi karatun ta kawai yana so ya dinga zuwa zance.”
Shiru Salisu ya yi kafin yace “ka barshi ya dinga zuwa ɗin, zaifi kan wuri wuri da suke bi dan su haɗu da juna, in a ƙofar gida ne da wuya shaiɗan ya raya musu wani abin fiye da in wuri wurin ne tun ana jin daɗin a haɗu a yi taɗin sai s koma tunanin ayi wani abun tunda ta nace sai ta yi zan ce, ai da sauƙi tunda tana son tayi karatun.”
Shiru Muktar ya yi kafin ya ce “eh kuma haka ne, in kayi area ɗin gurin sana’ar tasa ka faɗa masa Please bana jin kwarin jiki na bazan iya zuwa ba.”
Murmushi Salisu ya yi “karka ji komai Alhaji langai sarkin raki, ai kai dama badai cuta ta kama ba.”
Hararar sa Muktar ya yi yana murmushi, shiru sukai na wasu mintina Muktar na ta faman tattauna a ransa, yana son faɗawa Salisu son da yake wa Hafsa yana son shawara da shi yayin da wata zuciyar ke faɗa masa kar ya ya fada ɗagowar da zai yi Salisu ya riga shi faɗin “bari in koma gida ko karyawa ban ba” ya faɗa tare miƙewa.
Aje tunane tunanen Muktar ya yi yace “ok tom na gode mutumina, sai mun haɗu,” har ya ɗan yi taku mai tazara cikin rarraunar murya ta mara lafiya Muktar yace “kwanon shan fa?, daga inda yake Salisu yace in ka shanye na amsa anjima ya faɗa tare da karawa gaba, Muktar ya bishi da ido, kafin ya koma tunanin abar sonsa, salon tsokanar ta, salon murmushin ta komai nata da yake iya tunawa ƙara narkar masa da zuciya yake, kafin damuwa ta biyo baya in ya tuno da tazarar da ke tsakanin su, a hankali ya miƙe tare da ɗaukan kwanon shan ya shige gida, inna na tsakar gida ta ce “kwanon waye?.”
Kallon hannun sa ya yi kafin ya ce “Salisu ya kawon kunu kuma na samu na ɗan sha.”
Murmushi Inna ta yi “kai amma ya kyauta shine bai shigo mun gaisa ba?”
“Yace bai karya bane, nama ce ya faɗawa Garba ya dinga zuwa zance.”
Murmushi Inna ta yi kawai, yasan halin ta ba abinda zata ce ga hukuncin da ya yanke kan ƙannen nasa, bai ce komai ba ya shige ɗaki tare da kwanciya a katifar sa, ya lumshe idanun sa wanda ke faman zayyano masa lokacin da suke zaune a lsnbun su Hafsa suna karatu.