"Wai dan Allah Hafsa ke wacce irin mutun ce? Kin kira mutun kince ya zo ya taimaka ya koya mana, kuma yazo kin ce yunwa kike ji" Bilkisu ta faɗa a fusace cikin faɗa fada.
Juyowa Hafsa ta yi cikin halin ko in kula "Please Hajiya dena mun ihu, kina ji fa ya ce zai je gun abokin sa ɗan level five ya jira mu ai ko addini ya bawa yunwa haƙƙin ta, in coke village ɗinne ba zaki ba ki je gun sa ku fara" ta faɗa gami da yin gaba ba tare da jiran. . .