Motarsu Hajiya Mairo da Habeeb na sauka a tasha suka tari Napep. Unguwarsu Habeeb ɗin suka nufa, suna cikin tafiya ne Hajiya Mairo ta ji ya kwanto a kan kafaɗarta, lokaci ɗaya kuma yana ta sauke numfashi, hankali a tashe ta ɗan duƙo da kanta tare da faɗin "Habeeb mene ne?"
Murya can ciki ya ce "Zuciyata nake jin kamar zata fashe, Umma." Ajiyar zuciya ta sauke, ƙasan ranta kuma tana jin itama kamar tata zuciyar zata fashe, saboda tunda ta ga yanayinsa take jin wani irin tashin hankali, gani take kamar zata rasa shi.
Ido. . .