Washegari ma haka ya sake ɗaukar ƙafa ya sulala ya shige wajen Zalihar.
Misalin ƙarfe goma sha ɗaya ba safe, 11:00am. Bai gan ta a falo ba, don haka kai tsaye sai kutsa cikin uwarɗakin tamkar ɗakin matarsa, can ɗin ma bai iske ta ba. Sai ya ji ƙarar zubar ruwa a banɗaki, falo ya koma ya zauna kan kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ya hakimce kamar wani basarake yana jiran ta fito.
Fitowa ta yi ɗaure da tawul tana tsane ruwan jikinta ta yo falon, ba ta ankara ba sai da ta shigo tsakiya ta ga mutun zaune, da sauri ta ta shige uwarɗaki tana sakin tsaki. Shi kuwa dariya ya riƙa yi. Hijabi ta sako har ƙasa ta sannan ta dawo da faɗin, “Na lura ba jin magana kake yi ba, na bi ka da lalama ka ƙi fahimta ko?”
Ya lumshe idanu yana cewa, “Haba don Allah! Ba na son kina faɗin haka, ki saurare ni ki fahimce ni zan faɗa miki abin da yake raina. Wallahi tun ranar da idona ya yi tozali da ke na ji gabaɗaya son ki ya sarƙe mini zuciya. Ina son ki ina buƙatarki fiye da duk wani mahaluki a faɗin duniyar nan, ban taɓa ganin macen da ta kwanta wa raina ba kamar ki. Ba cutar da ke zan yi ba, ni soyayya ce a tsakanina da ke. Ki yi haƙuri don Allah ki karɓi wannan tayin nawa, babu abin da zai faru, ba wanda zai san me yake faruwa.”
Wani kallo mai ɗauke da mamaki ta riƙa yi masa tare da faɗin, “Wai kana cikin hankalinka kuwa kake faɗin wannan maganganun? Ina matsayin matar babanka ka ce kana so na? Don Allah ina roƙon ka ka bar wannan maganar kuma ka daina shigowa wajena.”
Ya marairaice cikin kalar tausayi ya ce, “Ba ki yi kama da mararsa tausayi ba, da a ce kin san yadda nake ji a raina da ba ki ce na daina shigowa wajenki ba.”
Yana maganar yana sake ƙare mata kallo, a ƙarƙashin zuciyarsa kuma yana faɗin, “Allah Gwanin halitta! An tara kyau da ni’ima a nan wajen.”
Idanunsa suka kada suka yi jajir kamar gauta, muryarsa ta canja. Ya marairaice sosai, ita kanta ta fahimci yanayinsa ya gama sauyawa, kausasa harshe a yanzu ba zai yi amfanin komai ba.
Don haka sai ta yi ƙasa-ƙasa da murya ta ce, “Na gode da soyayyar da kake mini, kuma na tausaya maka. Amma abin da ranka yake kitsa maka bai dace ba, haramun ne. Sannan kuma uwa uba ni fa matar mahaifinka ce, haƙuri za ka yi Allah sai ya ba ka wacce ta fi ni kyau.”
Shiru suka yi na ɗan lokaci zuwa can ta katse shirun da tambayar, “Ai kana da budurwa ko?”
Ya yi shiru bai ce komai ba, ta ci gaba da cewa, “Ina ganin ka gabatar wa da mahaifinka ita, idan ya so sai a shiga cikin lamarin abin ya tabbata. Hakan ne zai sa ka daina kallon wasu.”
“Na ji, zan yi hakan. Amma ina son ki janye sharaɗin hana ni shigowa wajenki, wallahi ba zan iya ba matuƙar kina cikin gidan kin zama uwarɗakina.”
Murmushi kawai ta saki ba tare da sake ce masa komai ba, ta nufi ɗaki ta yi kwalliya sannan ta dawo falon, har lokacin bai fita ba. Cikin dabara ta lallaɓa shi bayan sun ɗan taɓa hira ya fice.
Mamakinsa ta shiga, ‘shi ko kunyata ba ya ji, wai yana so na ya kama shi. Ina matsayin matar babanka? Lallai wannan da tsaurin ido kake! Ai ko ka yi ɓatan kai, wannan hanya da ka biyo ba za ta taɓa sada ka da abin da kake so ba. Ni mahaifin naka ma ban yarda da shi ba, ba kusantar sa nake ba bare kai.’ Ta dire tunanin da fatan Ubangiji Ya tsare ta ya ba ta damar cinye jarabawoyin da take fuskanta.
*****
To kamar yadda Anty Maryam ta yi alƙawarin ganawa da Abban Zaliha, hakan ce ta samu. Da dare ta isa gidan, bayan an yi gaishe-gaishe ta zarce kai tsaye da zayyana masa duk halin da Zaliha take ciki, ta bayyana masa irin matan da take zaman kishi da su babu abin da ta rage. Daga ƙarshe ta ɗauraye zancen da cewa,
“Duk waɗannan matsalolin da suke faruwa na san ba ka sani ba, kuma zai yi wahala koda sun shigo gidan nan su isa kunnenka. Ita ma yaya ɗin ba na jin ta san haƙiƙanin halin da yarinyar take ciki, saboda haka ya kamata a ɗauki mataki da wuri tun kafin ta kai ga shiga matsalar da za a zo ana tsugunni tashi. Sam zaman ba zai yiwu ba, akwai tsantsar cutarwa. Abokan zaman nata ba mutanen arziki ba ne, manyan banza ne marasa tsoron Allah. A baki Musa a zuci Fir’auna, haka suke. Don haka na ce lallai sai na sanar da kai domin na firgita da ganin yadda Zaliha ta rame ta lalace cikin ƙanƙanen lokaci. Babu shakka tana buƙatar kulawarmu da taimakonmu cikin gaggawa.”
Shiru Abba ya yi yana sauraren ta daki-daki har ta sauka sannan ya ɗan yi gyaran murya ya fara da cewa, “Da farko dai na gode wa Allah da ya nufa Zaliha take da dangi irin ki, sannan na ji daɗi da Ubangiji Ya fargar da mu da wuri kafin komai ya kai ga taɓarɓarewa. Watau komai ƙaddara ce ga bawa, Allah Ya ƙaddara wa yarinya shan wannan wahala, amma fa uwarta ga ta nan zaune tana ji na ita ce sila. Duk abin da ya samu Zaliha to ba za ta koka da kowa ba sai uwarta. Ba da son ranta aka yi auren ba, babu irin nunin da ban yi mata ba akan ta kaucewa tilasta mata auren wanda ba ta so, amma ga ta nan fur ta toshe kunnuwanta ta ƙi saurare na, ta ƙi fahimtar irin waɗannan matsalolin da kan taso bayan aure. Yarinya tana da tsayayye yaron kirki ɗan mutunci wanda ya san ƙimarta da darajata, amma sai ta rena arzikinsa, ta ci masa fuska ta butulce wa iyayensa ta ɓata duk wata kyakkyawar dangantaka da ke tsakaninmu da su. Yanzu tun bayan da aka yi bikin nake neman yaron na danni ƙirjinsa na haƙurƙurtar da shi amma sam ya ƙi yarda mu haɗu, idan na kira lambarsa koyaushe a kashe. To yanzu mene ne amfanin irin wannan?”
Ya ɗan tsahirta sannan ya ɗora da faɗin,
“Kuma babban abin takaici ba wani cikakken bincike aka yi game da shi wannan ɗin ba, kawai daga zuwa ya nuna mata kuɗi shike nan ta hau ta kafe lallai sai yarinyar ta amince da buƙatarta, babu ruwanta da abin da kan je ya zo. To saboda haka lallai na miki alƙawarin zan ɗauki mataki a kai, zan tuntuɓe shi cewa na ji ‘yan ƙorafe-ƙorafe daga wajen yarinya game da abokan zamanta, domin shi ya san halinsu. Ba za su taɓa bari a yi zaman lafiya ba, bare ma sun gan ta ƙarama ai sai yadda suka yi da ita. To za a yi wa tufkar hanci.”
Umma ta cika ta yi fam, ta rasa yadda ta yi sai kumbura take kamar ana buga mata iska. Ita a gurgun tunaninta bakin ciki ne kawai ake mata, ya ya sai da ta gama shan wahalar ‘yar tata daya tal, lokacin da za ta ci moriya ya zo sai kuma a zo mata da cikas! “To duk kun yi kun gama indai ni ce, zama kuma a wannan gida yanzu ta fara.”
Abin da ta iya fada a ranta kawai ke nan.
Anty Maryam ta yi musu sallama ta koma gida abinta.
To Hausawa na cewa faɗa wa mai zuciya biki ba mai kadara ba, kuma mai kamar zuwa ake aike. Kwana biyu da gabatar da ƙorafin Anty Maryam ga Abba, ya wanki ƙafa ya samu Alhaji Saminu da batun, magana ya yi masa cikin tattausan lafazi, shi ma ya risina matuƙar risinawa ya ce In Sha Allah ba za ta sake kawo ƙorafi makamancin wannan ba.
Bayan Sati Biyu.
Kamar yadda Hajiya Lami da Hajiya Sabuwa suka ƙuduri aniyyar sauya takun tafiyar tasu ta makirci da burin fitar da Zaliha daga gidan, haƙar tasu ta ƙi cim ma ruwa. Domin sun je wajen bokan nasu sun yi masa bayanin yadda suke so, kuma ya yi musu iyakacin abin da zai iya amma sam ba su ga alamar aikin yana yi ba.
A hannu guda kuma Hajiya Sabuwa tana nan ƙullace da Haijya Lami, sai ta rama tozarcin da ta yi mata. Ta ƙudurce ta kowacce hanya sai ta rama koda kuwa za su yi ragas.
Watarana da hantsi ta sake kiran Anas sashenta take tambayar sa, “Ya ya alaƙarka da Zaliha? Shin tana sauraren ka ko kuwa?”
Ya nisa tare da cewa, “E, to ba laifi. Amma maganar fatar ba ki ce, tana da kamun kai.”
“Ba damuwa, a haka sannu a hankali za ka riƙa bibiyar ta. Kada ka gajiya, za a dace kuma da kanta ma nan gaba za ta neme ka.”
Dariya ya yi ya ce, “Allah ko?”
Cikin salon makirci ta ce, “Ƙwarai kuwa, ai za ka sha mamaki.”
Haka dai ta riƙa zuga shi tana nuna masa dabarun yadda zai ƙara ƙaimi wajen cim ma baƙin burin nasa. Da marece bayan Magariba, Anas ya yi wuf ya shige ɓangaren Zaliha, iske ta ta ya yi bisa sallaya tana lazimci bayan ta idar da sallah. Sallama ya yi mata kamar koyaushe ya ɗora da cewa, “Antyna ta kaina! Barka da yini.”
“Barka dai!” Ta amsa.
Ya yi shiru ya zuba mata ido ko ƙiftawa ba ya yi, zuciyarsa ke saƙa masa wasu muggan tunane-tunane, zuwa can ya sauke ajiyar zuciya.
Dagowa ta yi ta kalle shi tare da cewa, “Ya ya lafiya kuwa?”
Ya ɗan ɓata rai kaɗan sannan ya ce, “Wancan banzar yarinyar ce mana, wai na je zance kawai na gan ta da wani old man.“
Ta yi dariya ta ce, “Gaskiya ba ta kyauta ba, amma da ka tsaya ka gani wataƙila ta sallame shi tunda ta gan ka.”
“Haba ai da na ci gaba da tsayawa a wajen zuciyata za ta iya bugawa.”
Dariya ta sake yi ba tare da ta ce komai ba, ya miƙa mata wani kwali ya ce, “Karɓi wannan idan kina ci cingan ne, ita na sayowa amma ba za ta ci ba.”
“A’a ba za a yi haka ba, ka ajiye gobe ka kai mata, ni na gode.”
“Yasin ba zan ba ta ba, ni ke nake so ki karɓa, sai dai idan ba kya son kyautar tawa ne.”
Tilasta mata ya yi sai da ta karɓa, har ma ta buɗe ta ɗauki guda ɗaya ta saka a baki. A ransa ya ji wani daɗi kamar zai yi shewa don farinciki. Suka ci gaba da hira, mintuna kamar biyar gyangyaɗi ya fara ɗaukar ta, kafin wani lokaci tuni barci na sosai ya yi awon gaba da ita.
Ya ɗaga hannunta ya tabbatar da barcin take yi, dariya ya yi, a ransa ya ce, “Maganar Hausawa daidai ce, a juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe. Yau burina zai cika.”
A hankali ya gyara mata kwanciya, ya zare mata hijabin daga jikinta ya miƙe. Ya cire rigarsa ke nan sai ga sallamar Alhaji, kai tsaye kuma ya shigo falon, da ma yau ce ranar da Zalihar za ta karɓi kwana.
Anas ya yi duburburce ya rasa inda zai yi. Motsa ƙafarsa gazawa ya yi, saboda kiɗimewa sai ya faɗa kan Zaliha tana kwance. Da yake barcin ba na Allah da Annabi ba ne, na magani ni ne, sam ba ta farka ba sai ma gyara kwanciya da ta yi, ta baje sosai. Alhaji ya tsaya cak!
Wani duhu-duhu yake gani, cikin sarƙewar murya ya ce, “Anas! Me ya kawo ka nan? Me kake aikatawa?”
Bai jira ya ba shi amsa ba ya ƙwalla wa matan nasa kira, nan da nan suka hallaro. Cikin zaƙuwa Hajiya Lami ta ce, Me ya faru Alhaji? Mene ne ya same ta ba lafiya ne?”
Hajiya Sabuwa ta wuce ta kama Zaliha tana jijjigawa tana faɗin, “Wai me ke faruwa ne Alhaji? Ka kira mu kuma ka ƙi faɗa mana abin da ya faru.”
Cikin tsananin ɓacin rai ya ce, “Ga shi nan ku tambaye shi.”
Hajiya Lami ta dubi Anas, kafin ta buɗa baki ya ce, “Abba don Allah ka yi haƙuri wallahi ban yi mata komai ba, kawai na shigo ne sai na gan ta a kwance.”
“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!” Hajiya Sabuwa ce da faɗin wannan addu’a daidai lokacin Zaliha ta farka. Ita ma salatin ta yi ganin ta a kan cinyar Hajiya Sabuwar, da sauri ta mayar da hijabinta.
“Munafuka! Wane hijabi za ki saka kuma? Bayan Allah Ya toni asirinki. Uwarki ta cuce ni, ashe duk kukan da kike na munafurci ne? Kara da kiyashi ɗaukar marar sani. Cin amanata kike yi da ɗan cikina. Allah Ya isa tsakanina da ke, ba zan yafe miki ba. Maza ki tashi ki bar mini gidana fasiƙa kawai.”
Hajiya Lami ta buɗa baki za ta yi magana ke nan, ya dakatar da ita da cewa, “Ki saurara mini kin ji, shashashar banza! Duk ba ke ce silar taɓarɓarewar yaron ba.”
Cikin zafin rai da ɗaga murya ya faɗi maganar.
Ya matsa kusa da Anas ya shammace shi ya dalla masa wani kyakkyawan mari a daidai, sai da ya tintsira bayan ya ga wata walƙiya mai tsananin haske ta gifta wa ganinsa.
“Ka gama yawo a faɗin duniyar nan, ba sai na bar ka ba har za ka yi abin da ranka yake so ba? Zan sa a killace mini kai.”
Yana faɗa ya sa hannu a aljihu ya zaro waya ya kira wani Baturen ‘Yansanda abokinsa, ya ce ya ya turo masa yara biyu. Nan da nan sai ga su, kasancewar babu nisa daga gidan zuwa ofishin nasu. Ce musu ya yi kada a ajiye Anas a nan kusa su kai shi can shalkwata sai ya zo. Hakan suka yi kamar yadda ya umarta, sannan ya koma cikin gida.
Wani irin farinciki ne maƙare a ran Hajiya Sabuwa, ji take tamkar ranar salla. Burinta ya cika, ko a iya haka aka tsayar da wasan tana jin ta rama abin da Hajiya Lamin ta yi mata.
Kuka marar amo Zaliha take yi mai tsananin ban tausayi da taɓa rai. Hajiya Sabuwa ce ta riƙe ta tana rarrashi, ta dubi Alhajin ta ce, “Kana yanke hukunci a cikin fishi, wanda hakan ba daidai ba ne a matsayinka na babba. Da alama yarinyar nan ba ta da laifi, dubi wannan cingan ɗin ka gani. Mai sa maye ne, shi ne a bakinta.”
A fusace Hajiya Lami ta harare ta tare da cewa, “Watau kina nufin Anas ɗin ne ya kawo mata shi don ya kauda hankalinta ko? Ke dai munafuka ce, wutarki daban.”
Tsawa Alhaji ya daka musu tare da cewa, “Ya ishe ni haka! Kowacce ta ɓace mini da gani.”
Hajiya Sabuwa ta ce, “Alhaji ka yi haƙuri ka ƙyale yarinyar nan zuwa gobe tukunna, a bi komai a hankali.”
“Ke wallahi ba zan iya ba, na haƙura da ita. Idan na ci gaba da zama da ita ban san kuma da wa zan gan ta ba, babu aure a tsakaninmu har abada. Afuwa ɗaya da zan yi mata shi ne ta kwana gobe da safe ta wuce gidan iyayenta.” Yana faɗa ya fice abinsa.
A nan aka bar Zaliha ita kaɗai, ta rasa wace irin ƙaddara ce wannan? Shin wane yanayi take ciki? A hannu guda kuma tana farinciki da sakin da ya yi mata, abin da take buri ke nan. Sai dai a ɗaya hannun tana tunanin ya ya za ta bayyana abin? Wa ya kamata ta fara sanarwa? Kai tsaye zuciyarta ta ce, “Anty Maryam mana, ita kaɗai ce za ta fahimce ki.”
Tana gama wannan tunani sai kuma ta shiga tunanin yadda Allah Ya kuɓutar da ita, ta ƙetare rijiya da baya a hannun Anas. Allah Ubangiji Ya yi gaskiya da Ya ce, “Kada ku kusnaci zina…”
“Babu shakka tun farko ni ma na yi kuskure da na ba shi fuska har yake shigo mini. Allah na gode maka da ka tsare ni daga faɗawa cikin wannan mummunar ƙaddarar. Ya Allah ina roƙon Ka ka buɗe wa mahaifiyata zuciyarta ta gane gaskiya ta kuma karɓe ta, ta yi aiki da ita.”