"Ku kira min doctor Anna, da sauri ta taho da allurar nan mai sa dogon bacci". Cewar doctor dake dafe da kansa yadda ya fara jin ya fara sara mai.
Da sauri wata Nurse ta fice domin aiwatar da abunda doctor ya ce.
Haris zare ido yayi ganin yadda doctor yake jujjuya kansa ya runtse ido. Da sauri yayi wajan Fu'ad yana cewa "dan girman Allah kuzo mubar asibitin nan". Wani kallo Fu'ad ya jefama Haris yana cewa "wai mi yasa Haris kake hakane?, y'an uwanmu ne fa ke cikin wani hali na rayuwa da mutuwa in. . .