Skip to content
Part 4 of 5 in the Series Kowa Ya Debo Da Zafi by Fatima Rabiu

“Ku kira min doctor Anna, da sauri ta taho da allurar nan mai sa dogon bacci”. Cewar doctor dake dafe da kansa yadda ya fara jin ya fara sara mai.

Da sauri wata Nurse ta fice domin aiwatar da abunda doctor ya ce.

Haris zare ido yayi ganin yadda doctor yake jujjuya kansa ya runtse ido. Da sauri yayi wajan Fu’ad yana cewa “dan girman Allah kuzo mubar asibitin nan”. Wani kallo Fu’ad ya jefama Haris yana cewa “wai mi yasa Haris kake hakane?, y’an uwanmu ne fa ke cikin wani hali na rayuwa da mutuwa in… Maganar ce ta mak’ale ganin doctor ya nufo wajansu. Wata irin zabura Haris yayi yana komawa bayan Fu’ad “na shiga uku shima ya koma dodon hala?” Haris ya fad’a yana b’oye fuskarsa a bayan Fu’ad. Fu’ad ya jawo shi yana cewa “banza lafiyarsa lau bai koma ba tukunna, gaskiya ka cika tsoro da yawa, ka natsu mana”.

Doctor dake kallonsu ya saki wani k’aramin tsaki yana cewa “ya kamata ku bamu had’in kai, ya akai wannan abu ya fara, tun fari ku natsu kuyi mana baya ni”. Da sauri Haris ya ce “mu natsu fa ka ce ana cikin wannan hali ina wata maganar natsuwa, nikam iyanzu nayi dana sanin zuwa wannan k’asar duk abunda ya same mu dasa hannun George a ciki duk yasan komai shida wani ma’aikacin hotel d’insa”.

Wani tsaki Fu’ad yaja ya fara magana yana ba doctor bayanin duk abunda ya faru, daga k’arshe ya ce “kawai abun sha ne fa suka sha suka koma haka, sai dai idan wani abu akasa mana a cikin abun shan nan”

“Tabbas akwai abunda akasa haka nan mutum bazai koma kamar dabba ba”. Cewar doctor yana girgiza kai alamar tabbatarwa. Daurewa kawai yake cikin jikinsa ji yake kamar ana yankan naman jikinsa, Fu’ad dake kusa dashi bai lura ba da yadda yake shinshinarsa kamar yana son kai mai cizo. Da sauri Haris ya ce “nifa ban yarda da wannan doctor d’in ba, na rantse muyi nesa dashi ya kusa komawa shima”,

“Wai Haris mi yasa ka zama haka ne wai?” Ibina ta idasa maganar tana kallon Haris. “Kinga laifi na ne?, gaskiya fa nake fad’a, idan mukai wasa gaba d’aya sai mun koma irinsu wallahi”.

Doctor jin shigowar Doctor Anna, yasa ya juya inda take cike da kulawa ta kama hannunsa ganin jinin ya daina zuba sai fatar wajan data fara komawa bulu, cike da d’an mamaki ta ce “doctor Daniel mi yake faruwa ne?. D’an bayani ya fara mata sana ya ce “yanzu karki damu dani, ki fara masu allurar please dan suna gaf farkawa, and idan suka farka bana jin zamu iya dasu, domin wani shegen k’arfi gare su, domin da George ya kama min hannu na rantse ji nayi kamar ba’a duniya nake ba”

Dariya ce ta kama Haris jin yadda doctor ke bayani, saida ya dara da sauri kuma ya maze ganin kallon dasu Ninaah suke mai. Allurar ta fara masu sana ta dawo wajan doctor Daniel. Ganin yadda yayi shuru kamar baya cikin hayyacinsa kansa yayi k’asa, ta nufi inda yake takun tafiyarta na buguwa da zuciyar Haris duk taku d’aya sai zuciyarsa ta buga. Domin shi ya tabbata doctor Daniel ya kamu da irin cutar dasu Zuzuuh suka kamu da ita. Runtse idonsa yayi yana faman cewa “Fu’ad mubar d’akin nan na rantse maka doctor d’in can shima ya koma”. Sai lokacin ma su Ninaah suka tuna an cizi doctor shima, da mugun gudu Ninaah da Ibina su kayi bakin k’ofa, sai dai kamin ma su isa bakin k’ofar Haris ya rigasu isa, da mugun sauri ya bangajesu yana niyar tura k’ofar jikinsa na kyarma.

Fu’ad ne kawai yayi azamar nufar inda doctor Anna dake niyar isa inda doctor Daniel yake. Sai dai kamin ya isa doctor Daniel ya d’ago idonsa ne ya koma fari fat hak’oransa sunyi masifar yin tsini, ya wage baki yana faman yin wani irin gunji kamar mage ta samu nama. Wata irin zabura doctor Anna tayi duk da haka tana gaf dashi tana faman yi mai magana, wai yana lafiya kuwa? Miye yake yi haka?. Daga can wajan bakin k’ofa Haris dake hango su ya bud’e baki ya ce “zaki ci uwarki ne kika tsaya tabbayar wadda zai hallakaki wai yana lafiya tabbas zai nuna miki yana lafiya ai”. Duk da halin da suke ciki bai hana sauran doctors d’in yin dariya ba, domin da harshan turanci yayi maganar.

Fu’ad yana gaf isa inda take kawai suka ji ihun doctor Anna, doctor Daniel yayi kukan kura, wani mugun tsalle yayi yana kada doctor Anna k’asa ya turmushe ta, kokowa suka farayi tana sun kwatar kanta, shi kuma yana neman inda zai kafa mata cizo.

Nigeria.

Kwance yake kan makeken gadonsa, sai faman juye-juye yake. Can kuma ya zabura yana faman kiran sunan Ammar. Da sauri Haj Maria dake kusa dashi a kwance ta tashi tana kunna fitilar dake kusa da ita. Kallonsa tayi ganin duk yadda zufa ta wanke masa fuska, cike da kulawa Haj Maria ta ce “Alh lafiya kuwa?”. Sauke ajiyar zuciya yayi ganin cewa mafarki yayi ya ce “wani irin mafarki nayi da Ammar”. Kallonsa tayi da d’an mamaki ta ce “Alh Ammar ai yanzu na tabbata yana d’akinsa a kwance”. Da sauri Alh Lado ya sakko daga kan gado yana nufar k’ofar fita yana cewa “hankali ya kasa kwanciyar wallahi wani fa mugun mafarki nayi dashi yana cikin wani hali, dama tun jiya naga alamunsa kamar suna shirya wani abu shida abokansa kinsan Ammar baya jin magana”.

Da sauri itama tabi bayansa. Suna shiga d’akin nasa suka ja turus suka tsaya, ganin wutar d’akin a kunne dubunsu suka kai akan gadon nasa babu komai akai ga waduruf a bud’e, hatta durowar da yake aje kud’i a bud’e take an yashe komai na ciki. Wata irin zufa ce ta yanko ma Haj Maria zuciyarta na bugawa da mugun sauri. Alh Lado kuwa wani irin jiri ne yaji yana neman kayar dashi, ba shiri ya nemi waje ya zauna yana dafe kansa.

Kallon Haj Maria yayi idonsa yayi jawur gabanta ne ya fad’i ganin irin kallon da yake mata da sauri ta ce “na rantse Alh bada sa hannuna a ciki banma san baya gidan nan ba”. Tashi yayi a hargitse yana nunata ya d’an yatsansa yana cewa “waye ya basa makullin duruwar kud’in nan to?, bana amsheta a hannunsa ba? , kuma kinsan yaron nan baya jin magana ko kad’an mi yasa baki sa mai ido yadda ya kamata ne?, yanzu wannan yaro ina zaize cikin uban ruwan nan cikin dare haka?”.

Haj Maria tama kasa magana sai hawaye dake zuba ta cikin idonta, domin bama fad’an Alh ne yake damunta ba, tunda suka shigo d’akin jikinta ya bata akwai wani abu mummuna dake faruwa da yaronta. Da sauri ta juya tabar d’akin tana nufar d’akinta. Wayarta ta d’akko tana danna ma wata number kira. Tana jin an d’au wayar bata tsaya jiran jin mi za’a ce ba ta fara magana tana cewa “Haj Aliya, ko Ammar yana gidanku yanzo wajan Haris ne?” Daga cikin wayar Haj Aliya itama cike da tashin hankali ta ce “nima abunda nake shirin kiranki naji shin Haris yazo wajan Ammar ne?”.

“Innalillahi wa’inna ilarhir raju’un” kawai Haj Maria ta take anbata ta sake cewa “tabbas duk inda suke suna tare da juna, amma bari na kira Haj Bilki ko suna tare da Fu’ad”. Da sauri Haj Aliya ta tari hanzarinta tana cewa “ai yanzu na gama waya da ita suma suna cikin tashin hankali dan shima Fu’ad d’in baya gida”.

Haj Maria bata san sadda wayar ta fad’i kasa ba ta tarwatse. Dafe kanta tayi tana tunanin ina yaran nan zasuje haka, tana tabbacin baza su zauna a k’asar nan ba, domin taga irin mak’udan kud’in da Ammar ya d’iba.

Haj Salma dake zaune kusa da Alh Mande ta ce “yau ka dad’e baka dawo gida da wuri ba, domin d’azo Zainab (Zuzuuh), ke tabbayar baka dawo ba”. Kallonta yayi yana kai lumar abinci a bakinsa yana cewa “yauwa kira min itama ina son ganinta”, “amma yanzu baka ganin tayi bacci”. “Ki taso min ita”. Shuru Haj Salma tayi tana nufar d’akin Zuzuuh, koda ta shiga sai da ta kwanna wutar d’akin, ta kai dubanta akan gadon Zuzuuh, murmushi ta saki ganin kamar mutum ne ke kwance akan gadon duk daukarta Zuzuuh ce kwance kai. Sai dai tana yaye abun rufar, ta zaro ido tana kallon yadda aka jera fulillika a tsaye sai yayi kamar mutum ne akan gadon yana kwance. Da mugun sauri ta fice daga d’akin tana nufar darning inda Alh Mande ke zaune, ganinta a hargitse yasa ya ajiye cin abincin yana cewa “lafiya dai na ganki kin fito haka?”

“Alh ba lafiya ba wallahi, na duba ko ina na d’akin Zuzuuh ban ganta ba, dama tun d’azo na lura kamar bata da gaskiya kamar tana shirya wani abu”

Tashi Alh Mande yayi ba shiri yana cewa “gidan ubanwa zata je cikin wannan daren da ake tsula uban ruwan nan, maza ki kira k’awayenta su biyu ko suna tare.

<< Kowa Ya Debo Da Zafi 3Kowa Ya Debo Da Zafi 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.