Skip to content
Part 5 of 5 in the Series Kowa Ya Debo Da Zafi by Fatima Rabiu

Hannunta Denial ya cafke tare da kafa mata haƙora. Ihu take tamkar ranta zai fita sakomakon azababben zafin da yayi mata dirar mikiya. Fu’ad ne ya lura da allurar da suka jefar can gefe, shammatar Denial yayi tare da daka masa ita a kai, nan take ya sulale a kasa sumamme. Numfashi Doctor Anna fita ya rika yi da kyar cikin radadin ciwo take fadar a miko mata karamin akwatin ta. Kafin ta rufe baki sauran likitoci sun shigo dakin a gigice. Nan suka hau ba Doctor Anna taimakon gaggawa.

Babban abinda ke tayar masu da hankali shi ne wannan wace irin cuta ce da zaka riƙa cin naman jikin dan uwansa. Daga taimako ga shi suna shirin rasa manya-manyan likitoci su guda biyu. Allurar bacci suka yima Anna nan take nannauyan bacci yayi awon gaba da ita. Ninaah da Haris ne suka shigo dakin tamkar ka ce masu tak su tsere. Tsattsaye suka yi ganin ana dibar jinin wadanda suke fama da cutar, “mutum biyu su biyo mu don akwai binciken da muke sonyi” daya daga cikin likitocin ya fada. “Babu inda zanje, ta ya zan fita in bar yan uwana cikin wannan halin?” Fu’ad ya fada ranshi a matukar bace. “Kaga Haris da Ninaah su je mu sai mu tsaya nan” Bayan fitar su Haris Fu’ad ne ya matsa kusa da gadon Ammar.

Kafe shi da ido yayi cike da tausayin halin da suka tsinci kansu, kamar ba sune cike da farin ciki a jiya ba. Tabbas rayuwar nan akwai ban tsoro, Ammar ne kwance bai son wanda ke a kanshi ba, shin me zasu fadama iyayensu in suka koma gida, ina bazai yiwuba dole ku warke. Maganar da Ibina tayi ma shi ce ta dawo da shi cikin hayyacina shi. “Fu’ad dubi jikin Zuzuuh ka gani duk tayi fari ga inda aka cije ta yana fitar da wani irin ruwa mai yauki.” “Jikinsu duk haka yake tunda lamarin nan ya faru, anya ba zamu nemi transper ba mu tafi wata kasar da su?” Turo kafor da aka yi ce ta saka su yin shuru, Haris ne da Ibina jiki a sanyaye.

Duk faman tambayar da suke masu amsa ta kasa samuwa sai faman binsu da ido suke. A hasale Fu’ad ke magana “kada ku mayar da mu sakarkari mana, ya zamu yi maku magana amma ku kasa bamu amsa” ya karasa maganar tare da nufar inda Haris yake gadan-gadan. Da sauri Ibina ta sha gaban shi don tasan shi da zafin zuciya ba tun yau ba. “Fu’ad mun mutu, ku dauka mun mutu kawai” Haris ya fada hawaye banin fuskar shi tamkar mace haka yake cizgar kuka. “Bangare mun mutu ba?” Ibina ta faɗa cikin tashin hankali “Lemun da su Zuzuuh suka sha, hade yake da wani acid mai matukar hatsari ga lafiyar dan adam.” Ninaah ta karasa maganar tare da share hawayen fuskarta. “Wa ya sanar da ku?” “Likitocin” Haris ya bada amsa. Yaraf! Ibina ta koma ta zauna cike da tashin hankali tare da dafe kanta da take jin yana barazanar tarwatsewa. Tsit dakin yayi kowa da abinda yake sakawa. “Duk wancan la’anannen ne Goarge ya haddasa mana wannan masifar, don haka banga amfanin rayuwarsa ba.” Fu’ad ya karasa maganar a fusce tare da nufar inda Goarge yake kwance.” Saurin shan gabansa Haris ya yi. “Mi zaka yi ma shi, wannan ba lokacin fada bane mafita ya kamata mu nema tun kafin lokaci ya kure mana” “mafita fa ka ce? Wace irin mafita bayan ya salwantar mana da rayukan abokan tafiya biyu, bayan raunin da ya ji ma Ibina. Ka matsa ka bani wuri tun kafin raina ya ba ci.” Ya karasa maganar a fusce. “Fu’ad ka dawo cikin hayyacinka, mafita zamu nema ba fada ba” tatss! Kake ji Fu’ad ya dauke Haris da lafiyayyen mari. “Naga alamar bakinku daya da George, ko dai siyar da mu kayi ka fada Mani.” Fu’ad shaƙe da wuyan Haris ke maganar cikin ƙaraji. Ibina da Ninaah ne suke kokarin ɓanɓare Haris amma sun kasa don ba rikon wasa yayi ma shi ba. Kuka suke suna rokon su daina fadan amma ina bugun juna suke tare da farfasa duk wasu glass dake wurin. Ganin zasu yi kisan kai ya saka Ninaah fita a guje ta Kira ma’aikata, da kyar aka raba su, nan take aka koro su daga cikin dakin. Ibina Kuka take tamkar ranta zai fita “Yau suke ke fada bama cacar baki ba, abinda tunda suke basu taba yi ba tun daga kuruciyarsu, anya basu debi ruwan dafa kansu ba, domin hausawa sunce kowa ya ɗebo da zafi bakin shi.” “Haris Fu’ad! muna cikin wannan halin kuke fada, abinda tunda muke ko a kuruciyar mu bamu taba fuskanta ba. Na roke ku mu aje komi a gefe yanzu ne lokacin da zamu rungumi juna ba lokacin fada ba, muyi wa kanmu adalci na rokeku.” Ninaah ta karasa maganar tare da sake fashewa da kuka. Samun kansu suka yi jikinsu yayi sanyi, domin tabbas gaskiya ta faɗa, dama Fu’ad akwai saurin zuciya.

 

Lab.

Tun bayan shigowar su abu daya suke yi, wato gwaje-gwaje akan jinin da suka deba. Duk iya binciken da suka yi abu daya suke gani wato cuta mai haddasama kwalwa cin naman ko wane iri ne. Babban tashin hankalin su ga George cikin mugun hali bare ya sanar da su inda ya sami wannan kwayar cuta domin sanin inda zasu samu maganinta, basu baro lab ba sai da dare ya raba amma duk da haka sun kira babban likita ya sanar masu yana zuwa da safe. Su Fu’ad kuwa juyin duniya anyi da su akan su shiga inda aka tanada domin kwanan masu jinya amma fur sunki tafiya sai ma suka kwanta saman kujeru dake daf da ɗakin da su Ammar suke. Dare ya tsala asibitin tayi tsit baka jin karar komi sai ta karnuka alamun kowa ya yi bacci. Su George tare da su Ammar dake kwance a gadajensu lokaci daya idanunsu suka bude. Dirowa suka fara yi daga saman gadajensu suna jan kafa kansu ya karkace kafa a murgude tare da nufar kofar fita. Cikin baccin Ibina ta ji kamar mutum tsaye a kanta, bude idanunta yayi daidai da sakin gigitacciyar karar da ta saka su Fu’ad farkawa, bude idon da zasu yi su Ammar suka gane sun zagaye da su sun saka su tsakiya idanunsu fari fat bakunansu na dalalar da jini.

<< Kowa Ya Debo Da Zafi 4

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×